Me zai faru idan gwamnati ta soke shirin sauya tunanin tubabbun ƴan Boko Haram?

Mayakan Boko Haram dauke da bindigogi da motoci biyu a bayansu

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan sulhu da ƴanbindiga da sauran mayaƙan ƙasar, hankali ya fara komawa kan makomar tubabbun mayaƙan da rayuwarsu a tsakanin al'umma.

A farkon makon nan ne majalisar dattawar Najeriya ta yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta dakatar da shirin da take aiwatarwa na yin afuwa da kuma sauya tunanin tubabbun ƴan kungiyar Boko Haram da sauran masu tayar da ƙayar baya.

Haka nan dan majalisar wakilan Najeriya Yusuf Adamu Gagdi ya shaida wa BBC cewa “tun farko bai dace a ce ana amfani da kudin gwamnati wajen aiwatar da shirin sauya tunanin masu tayar da kayar baya ba”.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun kwan-gaba-kwan-baya wajen yaƙi da matsalolin tsaro a ƙasar.

Wasu ‘yan majalisar na ganin cewa a maimakon sulhun, zai fi kyau gwamnati ta tabbatar da cewa an kama waɗanda suke aikata laifuka kuma a hukunta su kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada.

A baya-bayan nan rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin da ake yi cewa ana bai wa tsofaffin mayaƙan Boko Haram makamai tare da tura su zuwa fagen daga a ƙarƙashin shirin gyaran hali.

Mai kula da shirin, Birgediya Janar Yusuf Ali, ya ce zarge-zargen ba gaskiya ba ne, bayan wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna wasu tsofaffin mayaƙa, suna fafatawa tare da dakarun soji.

Ya ce mutanen da aka gani a cikin faifan bidiyon ba su da wata alaka da shirin, sannan wurin da aka nuna ba ya ɗaya daga cikin cibiyoyin shirin.

Yadda aka fara shirin

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta yi, ya nuna cewa a shekarar 2016 ce gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shiri ga tsofaffin mayaƙan Boko Haram mai suna "Operation Safe Corridor."

A cewar hedikwatar tsaro a lokacin, manufar shirin ita ce tantancewa da kula da mayaƙan da suka miƙa wuya da kansu.

Da farko an ƙaddamar da shirin ne domin yankin Arewa maso Gabas da rikicin ya fi shafa, kafin daga baya a faɗaɗa shi zuwa wasu jihohin Arewa maso Yamma.

Shirin ya taimaka wajen sauya tunanin tubabbun mayaƙan Boko Haram, inda rahotanni ke nuna cewa an sauya tunanin dubbai.

Rahoton ya ƙara da cewa zuwa shekarar 2017, alƙaluma sun nuna cewa aƙalla tsofaffin mayaƙan Boko Haram 10,000 ne aka sauya wa tunani, sannan aka mayar da su cikin al'umma, sannan shirin ya ƙunshi abubuwa kamar haka:

  • Sauya tunani tubabbun mayaka
  • Sulhunta tsakani
  • Karɓe makamai

Ya dace a dakatar da shirin?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yanzu dai ana muhawara ne a ƙasar kan buƙatar da wasu ‘yan majalisa suka gabatar ta neman a dakatar da shirin.

Dr Kabiru Adamu, masani kan harkokin tsaro a yankin Sahel kuma shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence ya ce akwai buƙatar a bi a hankali domin a cewarsa, kada wurin neman gyara a ƙara ɓallo ruwa.

"Akwai buƙatar a yi wa wannan batu nazari na tsanaki da kyakkyawar fahimta. Na farko dai shi wannan shiri na sauya tunanin tubabbun mayaƙa yana cikin tsarin ƙasa na ƙoƙarin yaƙi da ta'addanci da ake kira 'National Counter Terrorism Strategy'," in ji shi.

Masanin tsaron ya ce a cikin tsarin akwai ɓangarori kusan guda huɗu da suka ƙunshi:

  • Hadaƙa da ƙasashen waje
  • Yaƙi da matsalolin tsaro ta amfani da karfi
  • Amfani da dabarun da ba na ƙarfi ba
  • Ƙoƙarin canja salon wa'azi
  • Sauya tunanin tubabbun mayaƙa

Kabiru Adamu ya ce ganin cewa tsarin ya ƙunshi matakai daban-daban, dakatar da guda ɗaya kawai ba daidai ba ne.

"Ka ga a zo a cire tsari ɗaya kacal a ciki ko a dakatar da shi ba tare da an yi la'akari da alaƙarsa da sauran ba, bai dace ba. Kuma abu mafi muhimmanci ma shi ne ba a yi bincike don a gano wuraren da aka yi nasara da wuraren da aka samu tsaiko ba. Ka ga kuwa idan ba hakan aka yi ba, gaskiya ina ganin akwai kuskure," in ji Dr Kabiru Adamu.

Ya ƙara da cewa asalin abin da ya kamata a yi shi ne shi ne bincike da ake kira 'Evaluation' domin gano matsalolin tsari da kuma nasarorinsa, wanda a cewarsa majalisar ba ta yi wannan ba.

"Na biyu ina tabbatar maka cewa babu shaidar kai-tsaye da bincike na kimiya da ke nuna cewa akwai tubabbun mayaƙan da aka gano sun shiga cikin wannan matsalar ta tsaro. Akwai dai hasashe da raɗe-raɗi kuma suna da ƙarfi."

Ya ce idan ana so a tabbatar da zarge-zargen, "hanya ɗaya tilo ta tabbatarwa ita ce a yi bincike kuma majalisa ce ke da ikon haka," in ji shi.

Hanyoyin sulhu da mayaƙa

Masanin tsaron ya bayyana a wata tattaunawarsa da BBC cewa matakan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar domin kula da tubabbun mayaƙan su ne:

  • Sanin ko su wane ne
  • Amfani da kimiyya wajen ɗauka da tattara bayansu
  • Sanin na'ukan makamansu kafin karɓe su
  • Tsara me za a yi da makaman
  • Me za a yi da tubabbun? misali, koya musu sana'a ko saka su cikin jami'an tsaro.
  • Waɗanda suka yi wa laifi sun yafe ne ko suna buƙatar diyya?

Sai dai an daɗe ana nuna yatsa tsakanin gwamnati da mayaƙa kan abin da ya sa ake zargin suke komawa ruwa, lamarin da Kabiru Adamu ya ce babban laifin na gwamnati ne a dukkan matakai.

"Gwamnati ke da laifi, ita ke da haƙƙin tabbatar da doka. A tsarin da muke ciki yanzu akwai abin da ake kira 'social contract' mun hannanta wa gwamnati tsaronmu," in ji shi.