Abu 4 da wasu ƴan Najeriya ke fargaba game da ƴansandan jihohi

Asalin hoton, Getty Images
A wannan mako ne majalisar dattawan Najeriya ta amince da dokar da za ta bai wa jihohin kasar samar da rundunar ‘yansanda ta kansu, bayan da majalisar wakilan ƙasar ta amince da ita a watannin baya.
Sai dai wannann batu ya dade yana haifar da muhawara a fadin kasar.
Shugaban ƙasar Bola Tinubu ne ya buƙaci majalisar ta yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyaran fuska domin amincewa da dokar.
Yanzu haka za a tura dokar zuwa majalisun jihohin ƙasar domin tafka muhawara da amincewa da ita kafin shugaban ƙasa ya sanya mata hannu.
Gwamnati ta ce kafa ƴansandan jihohin zai taiamaka wajen magance matsalar tsaro da mafi yawan jihohin ƙasar ke fuskanta.
To amma masu sukar matakin na ganin cewa in ba a yi hankali ba ƴansandan za su ƙara jefa ƙasar cikin hatsari.
Mece ce fargabar?

Asalin hoton, Getty Images
Babban abin da masu sukar ke ambatowa shi ne fargabar amfani da ƴansandan jihohin ta hanyoyin da ba su dace ba.
Ɗaya daga cikin masu sukar shi ne Dr. Audu Bulama Bukarti, fitaccen lauya, kuma mai sharhi kan al'amuran tsaro a ƙasashen Afirka.
Ya kuma bayyana cewa matakin na da manyan illolin da za su iya haifar wa al'umma kamar haka:
Tasirin gwamnoni
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙwararren lauyan ya ce babban abin damuwar shi ne gwamnonin jihohi za su iya amfani da ƴansandan ta hanyar da ba ta dace ba wajen muzguna wa ƴan adawar siyasa a jihohinsu.
''Muna ganin yadda suke yin uwa da makarɓiya da hukumomin zaɓe na jihohinsu'', in ji shi.
Don haka ne ya yi kira ga hukumomin ƙasar da za su tsara dokar su tabbatar ba su bai wa gwamnonin jihohi damar amfani da yansandan wajen cimma manufofin siyasa ba.
Jamilu Aliyu Caharanci shugaban gamayyar ƙungiyar al'ummar arewacin Najeriya da aka fi sani da CNG ya ce duba da irin gwamnonin da ake da su yanzu a Najeriya da wahala a bar yansandan su yi aiki yadda ya kamata.
''Nan fa aka yi dokar cin gashin kan ƙananan hukumomi, amma mun ga yadda gwamnonin suke tauye wannan doka'', a cewar Charanci.
A tsarin dokar, gwamna shi me ke da damar nada kwamishinan ’yansandan jihar kuma zai iya ba shi umarni kai-tsaye.
Sai dai bayanin da fadar shugaban kasar ta fitar ya ce kwamishinan ‘yansandan na da damar ya ki bin umarnin gwamna idan yana ganin hakan ya saba wa doka.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙabilanci da bambancin addini
Najeriya ƙasa ca da har yanzu ta kasa magance matsalar ƙabilanci da bambancin addini.
Bukarti ya ce akwai jihohi da dama a Najeriya da hatta gwamnonin jihohin na ganin wasu da ke zaune a jihar a matsayin ƴan kama wuri zauna.
"To ka ga idan ka bai wa irin waɗannan gwamnoni ikon ƴansanda, za su yi amfani da su wajen muzguna wa wani ɓagare na al'umma da ba sa shiri da su'', in ji shi.
Jihohi da dama ne ke fama da matsalolin tsaro masu nasaba da bambancin kabila ko kuma addini.
Rashin iya ɗaukar nauyin su
Rundunar ƴansanda na bukatar kuɗi masu yawa da kayan aiki domin gudanar da ayyuka.
Akwai buƙatar yin gine-ginen ofisoshin rundunar da kayan aiki da ababen hawa da kuma albashin da za a biya su, wani abu da ke ganin da wahala jihohin su iya samar da su.
Masana da dama dai na ganin hakan zai haifar da ƙaruwar cin hanci da rashawa daga ƴansandan jihohin.
Jamilu Aliyu Charanci ya ce a halin yanzu ƴansandan tarayyar ma na ƙorafin rashin albashi mai kyau da walwala.
''Bindigoginsu sun jima har duniya ta riga ta manta da su, ya wanda ya kasa inganta wannan kuma ya ƙara ƙirƙiro wasu'', in ji shi.
Shiga aikin juna

Asalin hoton, Getty Images
Wata matsalar da za a iya fuskanta da ƴansandan jihohi idan an yi shi ne batun shigar aikin juna.
Galibi iyakokin jihohin Najeriya ba a ƙayyade suke ba, don haka Bukarti ya ce hakan zai sa ƴansandan jihohin za su riƙa samun ruɗani game da iyakokinsu.
''Za a iya samun ƴansandan wata jiha su shiga wata jiha su yi aiki, har kuma abin yanjo matsala'', in ji shi.
Sannan kuma ya ce idan ba a fayyce aikin ƴansandan jihohi da na tarayya ba za su riƙa samun shigar aikin juna tsakanin rundunonin biyu.
Matsayar gwamnonin
Sai dai gwamnonin sun kare matakin ne ta hanyar kafa hujjar cewa suna son samar da ƴansandan jihohin ne domin magance matalolin tsaron da ake fuskanta a sassan ƙasar.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani na daga cikin gamnonin da ke kan gaba wajen son samar da ƴansandan jihohin, ya kuma ce sun son matakin ne domin ƙarancin jami'an tsaron da ake da su a ƙasar.
A cewarsa, akwai aƙalla mutum miliyan 230 a Najeriya, yayin da ƴansandan ƙasar ba su wuce 230,000 ba.
"Akwai wurare a ƙasar nan da sai ka yi tafiyar kilomita 30 zuwa 100 ba ka ga jami'an tsaro ba."
Haka kuma Uba Sani ya ce samun ƴansandan jihohi zai taimaka saboda su ne suka san lungu da saƙon jihohin da suke.
A cewarsa: "Idan ka ɗauki ɗansanda ɗan Birnin Gwari (a Kaduna), za ka ga ya san dazukan yankin sosai, ya san lungu da saƙo, kuma ya san kowa a wurin."
Yayin wata tattaunawa da BBC a baya gwamnan na Kaduna ya ce a kundin tsarin mulkin Najeriya, ba za su iya gina ofishin ƴansanda ba sai sun samu izini wajen shugaban ƴansanda.











