Arsenal na son Junior Kroupi, Real Madrid na nazari kan Branthwaite

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na matuƙar son ɗaukar ɗan wasan gaba na Bournemouth da tawagar Faransa ta ƴan ƙasa da shekara 21, Eli Junior Kroupi mai shekara 20, amma ƙungiyar ta Cherries na sa ran samun kuɗi masu yawa daga cinikin. (Football London)
Real Madrid na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan baya na Everton, ɗan ƙasar Ingila Jarrad Branthwaite mai shekara 24, wanda kuma wasu ƙungiyoyin Premier League ke zawarcinsa. (Goal)
Chelsea na son tattaunawa kan yarjejeniyar fam miliyan 69 domin ɗaukar ɗan wasan gefe na Spain da Athletic Bilbao, Nico Williams mai shekara 24. (Fichajes)
Arsenal ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan tsakiya ɗan ƙasar Spain mai shekara 27, Martin Zubimendi, a watan Janairu. (Football Insider)
Ƙungiyoyin Real Madrid da Barcelona sun sake nuna sha'awar ɗaukar matashin ɗan wasan Amurka mai shekaru 16, Cavan Sullivan, wanda ake sa ran zai koma Manchester City daga Philadelphia Union idan ya cika shekara 18. (Teamtalk)
An tabbatar da cewa dole sai Liverpool ta biya fam miliyan 130 da Bournemouth ke nema kan ɗan wasan Brazil mai shekaru 20, Rayan, duk da dangantakar da ke tsakaninsa da kociyan ƙungiyar Andoni Iraola. (ESPN Brazil)
Ɗan wasan tsakiya na Atletico Madrid da Argentina, Julian Alvarez mai shekara 26—wanda ƙungiyoyin Arsenal da Barcelona ke zawarcinsa—yana tunanin rabuwa da wakilinsa na tsawon lokaci bayan jita-jita game da sauya ƙungiya a lokacin bazara. (Mundo Deportivo)
Ba a sa ran Everton za ta nemi ɗan wasan gaba na Tottenham da Brazil, Richarlison, duk da cewa an danganta ɗan wasan mai shekara 29 da yiwuwar komawa ƙungiyar ta Everton a lokacin bazara. (Football Insider)











