Lokuta 6 da mutanen gari suka yi wa wasu kisan gayya a Najeriya

Asalin hoton, Murtala
Kisan atara-atara na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke janyo rasa rayukan ɗimbin al'umma a Najeriya musamman bisa la'akari da yadda nau'in kisan ya daɗe na faruwa a tsawon lokaci.
Ana alaƙanta ci gaba da faruwar kisan jama'a ta hanyar yi musu atara-atara ne sakamakon rashin ɗaukar matakin doka akan mutanen da suka aikata kisan.
A Najeriya dai ana aikata kisan na atara-atara ne bisa wasu dalilai da suka hada da zargin ɓatanci da sata da tsafi da kuma maita.
Ƙungiyar kare haƙkin bil'adama ta Amnesty International ta ce an kashe aƙalla mutum 555 a tsawon shekaru 20 da suka gabata wato tsakanin watan janairun 2012 zuwa Agustan 2023.
BBC ta yi duba dangane da manyan kisan da jama'ar gari suka yi waɗanda suke zargi da aikata wani laifi a Najeriya da suka faru a baya-bayan nan.
Ummulkhair Marabar Jos - 21 Yuni 2026

Asalin hoton, Family
A ranar Lahadi wani gungun mutanen gari suka far wa wata baiwar Allah mai suna Ummulkhair inda suka kashe tare da ƙone ta bisa zargin satar yara, a garin Maraba da ke jihar Kaduna.
Da farko dai wani bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda cincirindon mutane suka yi dandazo a bakin ofishin ƴansanda na Marabar Jos, suna neman a miƙa musu Ummulkhairi, wadda aka kai wurin domin tseratar da ita.
Wannan ne ya sanya mutanen garin, wadanda a cewar rahotanni ke fama da matsalar satar yara a baya-bayan nan, suka nace kan dole sai sun ɗauki mataki a kan matar duk da cewa babu wata shaida da ta tabbatar da cewa ita mai satar yara ce.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai wani malamin Ummulkhair ya sheda wa BBC cewa ɗalibar tasa ta nemi rakiyar wani yaro zuwa wurin wa'azin, a inda wata mata ta hana hakan bisa cewa tana zargin ta da satar yara.
"Mun shirya wa'azin goron sallah, inda muka yi wa'azi 11 kafin daga baya muka jinkirta, daga nan sai muka shirya yin wannan wa'azin", in ji Shugaban kwamitin wa'azin matasa na Marabar Jos, Jamilu Tahir.
Shi ma mijin marigayiyar ya shaida wa BBC cewa DPO ne ya fitar da ita daga ofishin ƴansandan abin da ya sa jama'a suka samu damar yi mata kisan gilla.
"DPO ne ya kama ta, ya cire mata hijabi, ya tura ta kan titi, sannan ya juya ya koma ofishinsa," in ji mijin marigayiya Ummulkhair.
Bugu da ƙari, mutumin da ya yi ƙoƙarin ceton ran Ummulkhairi ya kuma jagoranci kai ta ofishin ƴansanda,Sulaiman Isah, ya tabbatar da cewa "DPO ne ya miƙa ta wurin al'umma".
BBC ta tuntunɓi ƴansanda domin jin martaninsu game da wannan zargi.
Mai magana da yawun rundunar, Mansir Hassan ya ce mutane ne suka fi ƙarfin ƴansanda suka ƙwace ta a hannunsu.
Ya kuma musanta zargin, inda ya ce: "Babu yadda za a yi DPO ya miƙa wa mutane matar.
"Shiga suka yi suka ƙwato ta da ƙarfi, kuma har yanzu muna ci gaba da bincike." a cewar DSP Hassan.
Rundunar ƴansanda ta kuma ce yanzu haka an kama mutanen da ake zargi da hannu wajen kisan matar.
Uromi, Jihar Edo - 27 Maris 2025

Asalin hoton, BBC Pidgin
A ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2025 ne wasu wasu mafarauta 16 ƴan jihar Kano da ke kan hanyarsu ta komawa gida daga jihar Rivers domin halartar bukukuwan Sallah ƙarama, suka gamu da ajalinsu a hannun ƴan banga bisa zargin garkuwa da mutane.
Hotunan da aka riƙa yadawa, waɗanda BBC ba ta tantance da kanta ba sun nuna yadda aka yi wa wasu mutane jina-jina, sannan aka riƙa jefa tayoyin mota a kansu.
Haka nan an ga yadda wasu ke dukan wani mutum da katako a cikin kwalbati, sannan a wani hoton kuma an ga wuta na ci daga nesa.
Sannan kuma an ga babbar motar kamfanin Dangote, wadda aka farfasa wa gilashi yayin da wani ɓangare nata ke ci da wuta.
Wani hoton kuma ya nuna bindigogin harba ka ruga, irin ta masu farauta ta gargajiya, da kuma adduna.
Bayanai sun nuna cewa ƴan sintiri ne dai suka tare motar mafarautan ne domin yin bincike amma mafarautan ba su bayar da hadin kai ba, wani abu da ya janyo sa-in-sa da bugun juna daga bisani.
Binciken da ƴan sintirin suka yi ya sanya aka gano bindigogi a motar, lamarin da ya janyo mutanen gari suka far wa waɗanda ke cikin motar bisa zargin cewa masu garkuwa da mutane ne.
Deborah Yakubu - 12 Mayu 2022

Asalin hoton, Deborah Yakubu/ Facebook 2022
A ranar 12 ga watan Mayun 2022 ne wasu matasa suka yi wa Deborah Samuel, ɗalibar shekara ta biyu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto, kisan atara-atara bisa zargin ɓatanci ga Manzon Allah (SAW).
Wani bidiyo da ya rinƙa karakaina a shafukan sada zumunta ya nuna yadda wasu matasa suka kashe Deborah bayan sun jefe ta da duwatsu.
Ƴansanda sun isa wurin da al'amarin ya faru bayan kisan Debrah kuma mutanen da aka kama bisa zargin hannu a al'amarin an sake su.
Ahmed Usman, Abuja - 04 Yuni 2022
A ranar 4 ga watan Yunin 2022 ne wasu matasa suka far wa wani ɗan sinitiri mai suna Ahmed Usman da aka fi sani da Musa bisa zargin ɓatanci ga annabi (SAW).
Al'amarin dai ya faru ne bayan da matasan suka zargin matashin da furta kalaman ɓatanci, inda suka far masa suka kuma kashe shi a Tipper Garage da ke unguwar Lugbe a Abuja.
Zainab Ahmed, matar ɗan bangar da aka kashe ta ce ba za ta yafe wa waɗanda suka kashe mijin nata ba.
Usman Buda, Sokoto - 25 Yuni 2023
Shekara day bayan kisan Ahmed Usman ɗan banga a Abuja sai aka kuma samun irin wannan ɗaukar doka a hannu a jihar Sokoto, inda wasu al'ummar gari suka yi wa wani mahauci mai suna Usman Buda kisan taron dangi.
Al'amarin wanda ya faru ranar 25 ga watan Yunin 2023 kamar yadda bayanai suka tabbatar ya fara ne lokacin da wani almajiri ya je wurin da Usman Buda yake domin yin bara.
Bayanai sun nuna cewa almajirin ya nemi a ba shi sadaka saboda annabi, inda shi kuma Usman ya faɗa wa almajirin cewa saboda Allah ake bayar da sadaka, al'amarin da ya janyo mutanen wurin suka yi zargin kalaman ɓatanci ga annabi.
Sai dai wasu sun yi zargin cewa akwai kwantacciyar rigima tsakanin marigayin da wasu abokan kasuwancinsa.
Martina Okey Itagbor, Cross River - 18 Yuli 2023

Asalin hoton, BBC Pidgin
A ranar 18 ga watan Yulin 2023, wani gungun matasa a ƙaramar hukumar Akamkpa da ke jihar Cross River suka yi wa Martina Okey Itagbor kisan gilla bayan sun zarge ta da maita.
An dai zargin dattijuwar ne da kama kurwa da mutuwar wasu matasa maza guda biyu waɗanda suka mutu a haɗarin motar da aka zarge ta da haddasawa.
Hakan ne ya sa aka yi cincirindo a gidan Misis Okey inda aka rinƙa yi mata tambayoyi, inda kuma daga bisani suka tsinto duwatsu suka jefe ta tare da ƙone ta a bakin titi.











