Rabiu Ali: Ɗan ƙwallon Kano Pillars da ya zama abin koyi ga matasa

Asalin hoton, Rabiu Ali Pele/Facebook
A ranar Lahadi, 30 ga Agustan 2026, filin wasa na Rashidi Yekini da ke Ilorin ya ɗauki hankalin masu sha'awar ƙwallon ƙafa a Najeriya. Wasan mako na farko na kakar NPFL ta 2026/27 tsakanin Kano Pillars da Kwara United, wanda ya kasance mai cike da armashi.
Baƙin ne suka fara da ƙarfi, inda suka fara da ci 2-0 kafin masu masu masauƙin baƙin suka farke aka koma 2-2.
Sai dai abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne ƙwallon da Rabiu Ali ya zura daga wajen layin 18, lamarin da ya sa ake ta muhawara kan yaushe tsofa da yanayin jiki za su danne fitaccen ɗanwasan.
Bayan wasan, Kano Pillar da magoya bayanta sun yi murnar samun maki, yayin da ita Kwara United ta yi murna ƙoƙarinta.
Amma ga masu bibiyar gasar firimiyar Najeriya, ɗan wasan mai saka lamba ne abi magana.
Tasowa da tashe
A tarihin Kano Pillars, an yi zaratan ƴan wasa da suka nuna bajintarsu a shekarun baya, amma yanzu ana ganin da wahala a samu wanda ya kai Rabiu Ali.
An haife shi a ranar 27 ga Satumban 1980, kuma ya fara rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa ne a Nasarawa United kafin daga bisani ya koma Kano Pillars, inda sunansa ya fara tashe har zuwa yanzu.
Tun bayan zuwansa Kano, ya taka muhimmiyar rawa wajen mayar da ƙungiyar ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin Najeriya.
Yayin da wasu ƴan wasa suka yi ƙaura zuwa ƙasashen waje ko wasu kulob daban, shi ya ci gaba da zama a Kano, inda ya gina wata alaƙa ta musamman da magoya bayan ƙungiyar.
A yau, idan aka ambaci Kano Pillars, akwai yiwuwar sunan da zai fara zuwa zuciyar mutane shi ne Rabiu Ali.
Kaka 18 yana taka leda
Abu mafi ban sha'awa game da labarin Rabiu Ali ba wai kawai tsawon lokacin da yi yana taka leda ba ne.
Abin mamaki shi ne yadda ya ci gaba da kasancewa mai tasiri bayan duk waɗannan shekarun.
Bayanan wasansa sun nuna cewa yana tare da Kano Pillars tun kakar shekarar 2008/2009, kuma har yanzu yana ci gaba da taka rawa a ƙungiyar.
A cikin wannan lokaci, ya ga canje-canje da yawa. Ya yi aiki da masu horaswa da dama, sannan ya yi zamani da gwamnoni da yawa, kasancewar ƙwallon Najeriya da da alaƙa sosai da gwamnatocin jihohi, sannan uwa-uba ya ga sauye-sauye a fasalin gasar da dama.
Amma abu ɗaya bai canza ba. Tasirin da Rabiu Ali ke takawa a ƙungiyar ta Kano Pillars.
Yaya batun ritaya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shekarar 2023, lokacin da yake da shekaru 43, tambayar da ake yawan yi masa ita ce: "Yaushe za ka yi ritaya?"
A wata hira da ya yi da shafin NPFL, an sake tayar da wannan tambaya. Amma amsarsa ta nuna irin tunanin da ya bambanta shi.
"Jikinka ne zai faɗa maka lokacin da ya kamata ka daina wasa, amma har yanzu jikina bai nuna nuna hakan ba."
Wannan ke nufin har yanzu yana jin ƙarfi a jikinsa, kuma alamu sun nuna ba magana kawai ya yi ba, har yanzu da yake da shekara 45, yana ƙara nuna ƙwazo da ƙwarewa duk da shekarunsa.
Wasu ƴan wasa kan daɗe a ƙungiya amma tasirinsu yakan ragu bayan lokaci. A wasu lokuta ana ajiye su ne saboda gogewarsu ko matsayinsu, amma sun fi zama a benci, amma labarin Rabiu Ali ya bambanta.
Shi ba kawai yana cikin ƙungiyar ba ne. Har yanzu yana taka muhimmiyar rawa a cikinta.
Har yanzu yana fara wasanni. Har yanzu yana raba ƙwallo, kuma har yanzu yana zura kwallaye.
Wannan ne babban bambanci tsakanin "dadewa" da "ci gaba da yin tasiri".
Wakiltar Najeriya

Asalin hoton, Rabiu Ali Pele/Facebook
A sakamakon yadda yake taka leda a cikin gida, ya samu damar wakiltar Najeriya a matakin ƙasa da ƙasa. Ya taka leda a tawagar Super Eagles ta masu taka leda a gida, inda ya buga gasannin CHAN na 2014 da 2018.
Ya bug wa Najeriya 18 tare da zura ƙwallo biyar.
Wannan nasara ta ƙara tabbatar da cewa ba kawai ɗan wasan Kano Pillars ba ne, har ila yau yana daga cikin fitattun ƴan wasan cikin gida da Najeriya ta samar.
Bayan wasan da Kano Pillars ta buga da Kwara United, kafar TheCable ta bayyana shi a matsayin ɗan wasan da ya ƙi tsufa, tana mai nuni da yadda yake fafatawa da matasan da za su iya kasancewa ƴaƴansa a filin wasa.
Wata rana babu shakka Rabiu Ali zai buga wasan ƙarshe. Kamar yadda lokaci yake yi wa kowa hukunci, shi ma wata rana zai ajiye takalminsa.
Amma idan wannan rana ta zo, ya kamata a tuna da shi a matsayin mutum wanda ya nuna cewa nasara ba kawai game da saurin gudu ko ƙarfin jiki ba ce. Wani lokaci nasara tana cikin ikon mutum na kasancewa mai amfani duk da tsawon shekaru.
A lokacin da yawancin takwarorinsa suka dade da yin ritaya, shi har yanzu yana fitowa fili.
Har yanzu yana ba da gudummawa, har yanzu yana zura ƙwallaye, har yanzu yana sa magoya baya su tashi tsaye suna tafa masa.
A shekaru 45, har yanzu yana da muhimmanci.










