KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 3/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Iran na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya da Pakistan kafin tattaunawarta da Amurka

    ....

    Asalin hoton, IRNA

    Iran na ci gaba da ƙarfafa hulɗarta da Saudiyya da Pakistan ta hanyar tattaunawa da manyan jami'an ƙasashen biyu, a daidai lokacin da ake sa ran fara sabon zagayen tattaunawa tsakanin Tehran da Washington cikin sa'o'i masu zuwa.

    Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran (IRNA) ya ruwaito cewa ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araqchi, ya yi tattaunawa ta biyu a ranar Lahadi da takwaransa na Saudiyya, Faisal bin Farhan Al Saud.

    Haka kuma ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Pakistan, sannan daga bisani ya tuntubi shugaban rundunar sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, wanda ake kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu tasiri a harkokin tsaro da siyasar ƙasar.

    Wadannan tattaunawa na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa za a fara sabon zagayen tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, inda za a mayar da hankali kan batutuwan mashigin ruwa na Hormuz da kuma shirin nukiliyar Iran.

  2. Trump ya sanar da fara sabbin tattaunawa da Iran a yau Litinin

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa za a fara sabbin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a yau Litinin, bayan sanarwar da ya yi a daren jiya game da janye wasu hare-haren da aka shirya kai wa Iran.

    Trump ya ce a halin yanzu akwai fahimta kan batun mashigar Hormuz, kuma yana da yakinin cewa za a cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran.

    Trump ta fadi hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One a ranar Lahadi.

    A gefe guda kuma, ministocin harkokin wajen Iran, Saudiyya, Pakistan, Qatar da Jordan na ci gaba da gudanar da tattaunawa da shawarwari, waɗanda ake ganin sun fi mayar da hankali kan tattaunawar da ke tsakanin Tehran da Washington.

  3. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.