Barcelona ta nace wa Rodri, Romero na son tafiya Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona na ci gaba da tattaunawa da Manchester City kan ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Sifaniya, Rodri, mai shekara 30, inda ta ƙara tayin da ta yi zuwa fam miliyan 51.4.
Ɗan wasan tsakiya na Argentina, Cristian Romero, mai shekara 28, na son tafiya Arsenal, amma Tottenham Hotspur ba ta da niyyar barin shi ya koma abokiyar hamayyarta ta arewacin Landan.
Romero kuma na cikin jerin 'yan wasan da Barcelona ke sa ido a kansu, yayin da ake sa ran kulob ɗin zai amince da tafiyar ɗan bayan Uruguay, Ronald Araujo mai shekara 27, zuwa Liverpool a matsayin aro.
Nottingham Forest na dab da kammala cinikin ɗan bayan Cote d'Ivoire Ousmane Diomande, mai shekara 22, daga Sporting Lisbon kan fam miliyan 34.
Ɗan wasan gaba na Sifaniya, Ferran Torres, mai shekara 26, ya sanar da Barcelona cewa yana son komawa Paris Saint-Germain, bayan ya amince da sharudan kansa da zakarun Turai.
Everton da Crystal Palace sun tattauna yiwuwar musayar 'yan wasa, inda Dwight McNeil na Everton da Brennan Johnson na Palace za su iya sauya kulob.
Tottenham na ci gaba da tattaunawa mai zurfi da Manchester City kan ɗaukar ɗan wasan gefe na Brazil Savinho, mai shekara 22. Ana ganin tayin fam miliyan 60 zai iya wadatar da kammala cinikin.
Aston Villa na gab da cimma cikakkiyar yarjejeniya da Atletico Madrid domin sayen ɗan bayan hagu na Italiya Matteo Ruggeri, mai shekara 24.
Ɗan wasan tsakiyar Southampton, Shea Charles, mai shekara 22, na iya komawa Leeds United idan kulob ɗin ya gabatar da tayi da ya zarce fam miliyan 30 da Fulham ta yi.
Niclas Fullkrug, mai shekara 33, ya amince da sharuddan komawa Venezia, amma cinikin ya tsaya saboda farashin da West Ham United ta sa wa ɗan wasan gaban na Jamus.
West Ham ta cimma yarjejeniya ta farko domin ɗaukar ɗan wasan gefe na Isra'ila Manor Solomon, mai shekara 27, daga Tottenham.
Fenerbahce na gab da kammala cinikin ɗan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 33, daga Napoli. Idan cinikin ya tabbata, Chelsea za ta samu wani kaso daga kuɗin sayarwar bisa yarjejeniyar da aka cimma a baya.










