Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 8/08/2026

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 8 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. KACRAN: Babu wani babban rikicin manoma da makiyaya a Yobe

    Khalil Moh'd Bello

    Asalin hoton, Khalil Moh'd Bello

    Ƙungiyar Makiyaya ta Kulen Allah ta Najeriya (KACRAN) ta ce jihar Yobe ba ta samu wani babban rikicin manoma da makiyaya da ya haddasa asarar rayuka ko lalata dukiya ba tun bayan fara kakar noman shekarar 2026.

    A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan wani taron wayar da kan jama’a a Damaturu, KACRAN ta ce ƙara samun haɗin kai tsakanin manoma da makiyaya, tare da ƙoƙarin gwamnatin jihar na tabbatar da zaman lafiya, ya taimaka wajen hana manyan rikice-rikice.

    Ƙungiyar ta buƙaci manoma su guji kutsawa cikin wuraren kiwo da aka tanada da kuma hanyoyin da dabbobi ke bi, yayin da ta yi kira ga makiyaya su guji shiga gonakin da aka shuka da kuma lalata amfanin gona.

    KACRAN ta kuma buƙaci bangarorin biyu su rika kai rahoton duk wata matsala ga hukumomin da abin ya shafa maimakon ɗaukar doka a hannu ko yin hukuncin gaggawa ba tare da bin ka’ida ba.

    Ƙungiyar ta yaba wa Gwamna Mai Mala Buni, sarakunan gargajiya, shugabannin ƙananan hukumomi da jami’an tsaro bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

    Haka kuma, KACRAN ta yi kira ga sauran gwamnonin jihohi da su yi koyi da tsarin Yobe wajen warware rikicin manoma da makiyaya cikin lumana, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

  2. Senegal na tuhumar mutum 71 kan zargin luwaɗi

    Masu gabatar da ƙara a Senegal sun gurfanar da maza 71 a gaban kotu bayan bincike da aka gudanar a kansu kan zargin luwadi An janye tuhumar da ake yiwa mutum wasu kan wasu mutum 28.

    A watan Maris, Senegal ta kafa sabuwar doka da ta ƙara tsaurara hukuncin wasu laifuka.

    Tun daga lokacin, hukumomi sun kama fiye da mutum 100, ciki har da wasu fitattun mutane, bisa zarge-zarge daban-daban da suka haɗa da karya dokokin da kuma, a wasu lokuta, yaɗa cutar HIV da gangan.

  3. Mahaifin Lionel Messi, Jorge, ya rasu yana da shekara 68

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Jorge, mahaifin Lionel Messi, ya rasu yana da shekara 68 bayan fama da rashin lafiya na dogon lokaci.

    Jorge, wanda ya kasance wakilin ɗansa tun lokacin da Messi yake da shekara 14, ya rasu a wani asibiti da ke garinsu na Rosario, Argentina, da sanyin safiyar Asabar.

    Bayan raɗe-raɗin da aka yi kan lafiyarsa a lokacin gasar cin kofin duniya ta bana, iyalan Messi sun fitar da wata sanarwa cewa yana fama da “wani yanayin rashin lafiya”, amma ba su bayyana irin rashin lafiyar ba.

    Jorge ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa ɗansa ya zama ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasan ƙwallon ƙafa a tarihi.

    Ya kuma kasance a Qatar domin ganin Lionel Messi ya cimma burinsa na jagorantar Argentina zuwa lashe gasar cin kofin duniya karo na uku a shekarar 2022.

  4. Pezeshkian: Iran ta samu damar dakatar da hare-hare a Lebanon ne ta tattaunawa

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    A bikin cika shekara biyu da hawansa mulki, shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya kare ci gaba da tattaunawa da Amurka, yana mai cewa: “Idan za mu iya samun haƙƙinmu ta hanyar tattaunawa, me ya sa za mu yi yaƙi?”

    Ya ce Iran ba za ta ja da baya daga matsayinta ba, amma ya ƙara da cewa ci gaba da yaƙi wata hanya ce da, a cewarsa, Isra’ila ke son bi domin tilasta wa Iran miƙa wuya.

    Mista Pezeshkian ya kuma ce ta hanyar tattaunawa, Iran ta samu damar dakatar da yaƙi a Lebanon, da kuma sassauta wasu takunkumi da aka kakaba mata.

    A wani bangare na jawabinsa, ya ce an gayyaci shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya shiga tawagar da ke tattaunawa, kuma ya amince da gayyatar.

    Mista Pezeshkian ya ce wakilai daga bangaren shari’a, majalisa, rundunar soji da sauran hukumomi su ma suna cikin tawagar, domin nuna cewa, a cewarsa, “dukkanmu muna tare.”

    Ya kuma nuna takaici kan yadda wasu ke tozarta Mista Araqchi, yana cewa: “Ban san wace irin addini ce ke ba mutum damar yi wa wani ƙazafi, zagi ko tozarta shi ba.”

    A wani bangare na jawabinsa kuma, shugaban Iran ya soki mutanen da, a cewarsa, “ke yin tsokaci kan komai ba tare da cikakken bayani ba.”

    Ya ce mutanen da ke ba da shawarwari kan matsalolin tattalin arziki, siyasa da zamantakewa masu sarkakiya ba tare da isassun bayanai ba, “suna kai al’umma ga bata hanya.”

  5. 'Abin da ya sa muke so majalisar Najeriya ta dakatar da hutu'

    Majalisa

    Asalin hoton, BENJAMIN KALU

    Wasu gungun yanmajalisar wakilan Najeriya sun buƙaci majalisar tarayya ta dakatar da hutun da take yi domin gudanar da zaman gaggawa kan batutuwa da suka shafi ci gaban kasa.

    Yanmajalisar da suka fito daga jam'iyyu daban-daban sun kafa wata kungiya da suka kira Save Democracy Group mai rajin kare dimokuradiyya.

    Ƙungiyar ta bukaci shugabannin majalisun ƙasar guda biyu su kira zaman gaggawa domin tattauna batun aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 da 2025 da na 2026.

  6. An naɗa Sheikh Abdulƙadir Jiyali Sarkin Takutaha na ƙasar Hausa

    Ali Rabiu Sufi.

    Asalin hoton, Ali Rabiu Sufi.

    An naɗa Sheikh Abdulƙadir Jiyali a matsayin Sarkin Takutaha na Ƙasar Hausa, a wani biki da aka gudanar a Fadar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ranar Alhamis 6 ga Agusta 2026.

    Bikin naɗin ya samu halartar malamai, shugabanni da ɗimbin masoya Manzon Allah (SAW) waɗanda suka bayyana farin cikinsu da wannan karramawa.

    A jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Daura ya ce an yi naɗin ne bisa la’akari da gudummawar Sheikh Abdulƙadir Jiyali wajen cusa son Manzon Allah SAW a zukatan al’ummar Musulmi da ƙarfafa bin koyarwarsa.

    Ya kuma bayyana fatan cewa wannan sarauta za ta zama alheri ga al’ummar Hausa. A nasa jawabin, Sarkin Takutaha na Ƙasar Hausa, Sheikh Abdulƙadir Jiyali, ya gode wa Allah, sannan ya miƙa godiyarsa ga Mai Martaba Sarkin Daura da majalisar masarautar bisa wannan karramawa.

    Sheikh Abdulƙadir Jiyali ya roƙi Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa cikin adalci da amana, tare da sanya sarautar ta zama alheri ga Musulunci da al’ummar Hausa.

  7. An rantsar da sabon shugaban Colombia

    Colombia

    Asalin hoton, Getty Images

    An rantsar da sabon shugaban Colombia Abelardo de la Espriella inda ya sha alwashin murkushe abin da ya kira ta'addancin masu fataucin miyagun kwayoyi.

    An rantsar da shi ne a birnin Cali maimakon babban birnin kasar - wani sauyi da ke nuna alamar yaki da kungiyoyi da ke dauke da makamai a yankin.

    Wakilin BBC ya ce ya gabatar da jawabi ga dakarun kasar a wani sansani bayan rantsar da shi, inda ya bukaci tabbatar da doka da yanci a Colombia. Gwamnatin Trump da ke goyon bayan shugaban ta yi alkawalin ba shi tallafin tsaro na biliyoyin daloli

  8. Auren gata ga mutum 3,000 a Kano

    Bayanan bidiyo, Auren gata ga mutum 3,000 a Kano

    Auren gata ga mutum 3,000Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da Auren Gata ga mutum 3,000 (ma'aurata 1,500), tare da tallafin fara rayuwar aure.

    Daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren akwai Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da sauran manya a jihar.

  9. Muna da sharuɗɗa kafin buɗe mashigar Hormuz - Iran

    Hormuz

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran ya sake jaddada cewa sake buɗe Mashigin Hormuz zai dogara ne da wasu sharuɗɗa da dama, waɗanda suka wuce yarjejeniyar da Tehran ke tattaunawa a kai da Oman a halin yanzu.

    Abbas Araghchi ya ce Oman da Iran sun kusa cimma yarjejeniya kan wata sabuwar hanya da jiragen ruwa za su rika bi ta mashigin ruwan.

    Sai dai ya ƙara da cewa za a sanya wasu sharuɗɗa, ciki har da biyan diyya kan abin da Tehran ke cewa Amurka ta karya daga cikin yarjejeniyar da aka cimma a watan Yuni domin kawo ƙarshen yaƙin.

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

  10. 'Mutum 25 sun mutu, macizai sun sari wasu, mata biyu sun haihu muna wajen masu garkuwa'

    Bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Fiye da mutane 300 da aka yi garkuwa da su a hare-hare daban-daban a jihohin Kwara da Neja sun samu ƴanci bayan kusan shida, bayan wani ceto da fadar shugaban Najeriya ta bayyana a matsayin mafi girma da jami'an tsaro suka gudanar a rana guda.

    Daga cikin waɗanda aka ceto akwai mutum 163 da aka yi garkuwa da su a harin da aka kai kan al'ummomin Woro da Nuku a jihar Kwara a watan Fabrairu, inda aka kashe wasu mutane.

  11. UEFA ba ta biya wadda aka yi zargin muna soyayya ba - Infantino

    FIFA

    Asalin hoton, Getty Images

    FIFA ta ce shugabanta, Gianni Infantino, ya yi kakkausar suka tare da musanta wani zargi cewa UEFA ta biya wata mata da aka bayyana a matsayin masoyiyarsa, a lokacin da yake shugabantar hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai.

    Wani mai magana da yawun FIFA ya ce zargin, wanda jaridar Daily Telegraph ta Birtaniya ta wallafa, ba gaskiya ba ne ko kaɗan.

    UEFA ta tabbatar da cewa ta biya ma’aikaciyar da ake magana a kanta wani kuɗin sallama daga aiki, sannan ta dauki nauyin karatun MBA dinta, amma ta ce an yi hakan ne bisa ƙa’idojin da suke aiki a lokacin.

    Zargin ya fito ne a daidai lokacin da ake fama da tsamin dangantaka tsakanin FIFA da UEFA, musamman kan shirin Infantino da aka yi watsi da shi na sayar da hannun jari a gasar cin kofin duniya da sauran gasa.

  12. Amurka za ta kashe dala biliyan uku domin ƙera sababbin makamai

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Trump ta sanar da cewa za ta kashe dala biliyan uku a ayyukan haƙar ma’adanai masu muhimmanci da kuma samar da batura.

    Wannan na cikin wani ɓangare na zuba jari da nufin taimakawa wajen sake cike rumbunan makamai na Amurka bayan yaƙin da aka yi da Iran.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa sojojin Amurka sun yi amfani da adadi mai yawa na makamai masu linzami da kuma makamai masu linzami na kare sararin samaniya yayin yaƙin da suka shafe watanni biyar suna yi da Iran.

    Jami’an tsaro da ’yan majalisar dokokin Amurka sun yi gargadin cewa zai iya ɗaukar shekaru kafin a maye gurbin wasu daga cikin waɗannan makamai, saboda ƙalubalen da ake fuskanta wajen samar da su cikin gaggawa.

    Ana amfani da wasu ma’adanai kamar rare earth, tungsten, germanium da scandium wajen kera makamai masu linzami masu bin sahihin manufa, jiragen yaƙi, motocin sulke da kuma ingantattun na’urorin soji.

  13. Harin RSF ya yi ajalin aƙalla mutum biyar a Sudan

    sUDAN

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Sudan sun ce akalla mutum biyar aka kashe a wani hari da dakarun RSF suka kai a jihar Kordofan ta Arewa.

    Majiyoyin tsaro sun ce mayakan sun bude wuta kan mutanen kauyen Al Tamid bayan sun bijere wa wani yunkuri na satar dabbobinsu.

    An kai harin ne a kudancin birnin El-Obeid da aka yi wa kawanya inda fadan da ake gwabzawa ya raba dubban mutane da gidajensu.

  14. Trump ya soki kotun Amurka bisa dakatar da gini dala miliyan 400 a White House

    Donald

    Asalin hoton, EPA

    Donald Trump ya yi kakkausan maartani ga hukuncin da kotun daukaka kara ta Amurka ta yanke na dakatar da gina dakin taro na dala miliyan dari hudu a Fadar White House.

    Mista Trump ya ce hukuncin siyasa ce kawai kuma abin kunya ne ga kasa Wakilin BBC ya ce hkuncin kotun wani cikas ne ga matakin Trump na gina dakin taron Mr Trump ya ce zai daukaka kara zuwa Kotun Koli.

    A bara ne, Mista Trump ya rusa wani bangare na Fadar White House domin samar da wurin shirya taro. Kotun ta ce irin wannan gagarumin aiki ya kamata ya sami amincewar Majalisa.

  15. Harin mayaƙan Houthi ya kashe aƙalla 10 a Yemen

    Houthi

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani harin mayakan Houthi ya kashe akalla mutum 10 a birnin Marib na Yamen.

    Mayakan masu samun goyon bayan Iran da kuma ke rike da ikon babban birnin Yemen har zuwa yammacin Marib sun ce sun kai harin ne kan dakarun da ke samun goyon bayan Saudiyya.

    Sun kai harin ne kwana guda bayan kashe wasu dakarun gwamnatin Yemen da dama a wani hari ta sama da mayakan na Houthi suka kai a sasanonin soji na Marib da lardin Hadramawt bayan mutuwar wasu fararen hula 11 a wani harin na Houthi a yankin Najran na Saudiyya

  16. Amurka da Isra'ila ba su ci ribar yaƙi da mu ba - Iran

    Iran

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    A cikin wata sanarwa da rundunar dakarun juyin-juya-halin Iran (IRGC) ta fitar a yayin bikin ranar ƴan jarida, rundunar ta ce Amurka da Isra’ila ba su cimma manufofinsu ba a yaƙe-yaƙen baya-bayan nan da suka yi da Iran.

    Ta ce abin da ta kira “yarjejeniyoyin da aka cimma” ba komai ba ne illa “takardar miƙa wuya da Amurka ta yi ga halin da ake ciki a fagen daga da kuma ƙarfin Iran wajen tattaunawa.”

    Sanarwar ta kuma ce Washington ta fuskanci “tsaka mai wuya ta fuskar dabarun yaƙi” a yaƙin da take yi da Iran, sannan kuma an samu ɓaraka tsakanin ƙawayenta na ƙasashen Yamma.

    Sai dai IRGC ba ta bayyana takamaiman yarjejeniyoyin da take magana a kansu ba.

  17. Farawa

    Jama'a masu bibiyar wannan shafi na kai-tsaye daga BBC Hausa.

    A wannan shafi za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.