Wace ce Aisha Achimugu da kotu ta ƙwacewa kadarori na biliyoyin kuɗi?

Asalin hoton, EFCC
Tun ranar Alhamis ɗin nan sunan fitacciyar ƴar kasuwar nan ƴan Najeriya, Aisha Achimugu ya yi ta yawo a kafafen yada labarai da na sada zumunta bayan wata kotu a Abuja ta bayar da umarnin ƙwace kadarorinta da miƙa su ga gwamnati.
Wata babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke zamanta a Apo, Abuja, ce dai ta bayar da umarnin ƙarshe na ƙwace kadarorin da ake alaƙantawa da 'yar kasuwa, Aisha Achimugu, tare da mayar da su hannun gwamnatin tarayya.
Kadarorin da aka ƙwace sun haɗa da kawa da darajarsu ta kai naira biliyan 4,645,170, 294.9.
Haka kuma, kotun ta ƙwace motoci 11 na alfarma da darajarsu ta kai naira biliyan 4.293, da kuma dala 50,000 na Amurka da naira miliyan 30 a tsabar kuɗi.
Mai shari'a Jude Onwugbuzie ne ya bayar da umarnin a ranar Alhamis, 16 ga Yulin 2026, bayan yanke hukunci kan bukatar da Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati, EFCC ta shigar domin a tabbatar da ƙwace waɗannan kadarori har abada a kuma miƙa su ga gwamnatin tarayya.
Shin wace ce Aisha Achimugu?
Wace ce Aisha Achimugu?

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
Aisha Sulaiman Achimugu ƴar kasuwa ce kuma fitacciyar mai hannun jari a Najeriya. Ita ce shugabar kamfanin FELAK Concept Group, wani rukuni na kamfanoni da ke aiki a fannoni kamar man fetur da iskar gas, injiniyanci da harkokin ruwa da fasahar sadarwa.
Aisha Achimugu ƴar asalin ƙaramar hukumar Ofu da ke Jihar Kogi ce amma kuma an haife ta a garin Kuje da ke babban birnin tarayya.
Ta karanci fannin akanta a Jami'ar Jos kafin ta ci gaba da karatun gudanar da kasuwanci.
Achimugu ta yi suna a harkokin kasuwanci da ayyukan taimakon jama'a, inda take gudanar da gidauniyar SAM Empowerment Foundation.
Haka kuma an san ta da kasancewa daya daga cikin fitattun mata masu tasiri a harkokin kasuwanci a Najeriya.

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
Me ya sa aka ƙwace kadarorin Aisha Achimugu?

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukumar EFCC ta ce bincikenta ya gano cewa biliyoyin nairori da kuma miliyoyin daloli sun riƙa shiga da fita cikin asusun bankuna da kamfanonin da ke da alaƙa da 'yar kasuwar.
A cewar hukumar, binciken ya kuma nuna cewa manyan kuɗaɗen da suka bi ta kamfanonin da ake dangantawa da Misis Achimugu ba a bayyana su a matsayin kuɗaɗen shiga ba a cikin bayanan kuɗi da aka gabatar wa Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS).
EFCC ta bayyana cewa daga baya jami'anta sun aiwatar da sammacin bincike a gidan Misis Achimugu, inda suka gano kuma suka ƙwato kayan ƙawa masu tsada, motoci na alfarma da kuma kuɗaɗe, waɗanda daga baya suka zama batun shari'ar ƙwace kadarori.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa yayin da ake yi mata tambayoyi, Misis Achimugu ta cike fom ɗin bayyana kadarorinta amma ba ta bayyana kayan adon, motocin da kuɗaɗen da aka gano ba a matsayin wani ɓangare na kadarorinta.
Bisa ga sakamakon binciken da ta gudanar, EFCC ta kafa hujjar cewa kuɗaɗen da aka gano a asusun da ke da alaƙa da 'yar kasuwar ba halastattu ba ne.
Hukuncin da kotun ta yanke a ranar Alhamis shi ne sabon mataki a jerin shari'o'in da suka shafi kadarorin Misis Achimugu.

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK

Asalin hoton, efcc/facebook











