KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 17/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 17/07/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Iran ta yi iƙirarin lalata wasu cibiyoyin Amurka a yankin Gulf

    Ɓarna

    Asalin hoton, Reuters

    Dakarun juyin juya halin Iran sun bayyana cewa sun lalata na;urorin sadarwar Amurka biyu a ƙasar Oman.

    Cikin wata sanarwar da rundunra ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta ce rundunar sojin ruwanta ta lalata na'urar da ke kula da sadarwar jirage a tashar ruwa ta Salalah da kuma wadda ke tashar Ghanem duka a Oman da safiyar yau Juma'a.

    Sanarwar ta jaddada cewa Iran za ta ci gaba da ɗaukar matakan martani, kuma mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon dakarun sojin ruwa na rundunar juyin juya halin.

    IRGC ta kuma ce ta kai hari kan sansanin sojin Amurka na Al-Tanf da ke kudancin Siriya.

    Rundunar ta ce ta kai harin ne a matsayin martani ga kisan sojojinta a harin Iranshahr.

    ''Dakarun sojin sama na rundunar IRGC sun kai hari kan sansanin sojojin Amurka na musamman a Al-Tanf, da na'urorin sadarwar jirage da kan jirage na musamman masu saukar ungulu da wasu sojojin na Amurka'', in ji sanarwar ta IRGC.

    To sai dai kakakin rundunar sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya, CENTCOM ya shaida wa kafar yaɗa labarai na Al Jazeera cewa hare-haren an Iran kan ƙasashen yankin Gulf ''ba su haifar da wani lahani da ayyukan sojojin ba''.

  2. Amurka ta ce ta kai hari kan ɗaya daga cikin tasoshin ruwan Iran

    Tashar ruwa

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin dillancin labarai na Iran, IRNA, ya bayar da rahoton cewa Amurka ta kai hare-hare kan na'urar lura da zirga-zirgar jirage a tashar ruwa ta Chabahar har sau uku da safiyar yau Juma'a.

    Rahoton ya ce hare-haren sun lalata ilahirin na'urar, amma ba a samu wata ɓarna ga jiragen ruwan ko sauran kayyakin da ke tashar ba

    Majiyoyi sun ce ƙarar manyan abubuwan fashewa ne suka lalata na'urar.

    IRNA ya ce tawagogin masana da masu bincike na auna yanayin, da nufin gyara na'urar domin ci gaba da gudanar da ayyuka a tashar.

    Babu dai labarin jikkata ko rasa rai a lokacin harin.

  3. Trump ya zargi China ta yin katsalandan a zaɓen Amurka na 2020

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi China da yin katsalandan mai yawa a zaɓen shekarar 2020, tare da iƙirarin cewa hukumomin leƙen asirin Amurka sun yi ƙoƙarin ɓoye abin da ya bayyana a matsayin yunƙurin Beijing na cutar da shi a siyasance a zaɓen wancan lokaci.

    A wani jawabi da ya yi wa al'ummar ƙasar, Mista Trump ɗin, wanda ya sha kaye a zaɓen a hannun Joe Biden, ya sake nanata zarginsa cewa an tafka maguɗi a zaɓen domin hana shi samun nasara.

    Gwamnatin China ta mayar da martani a sanarwar da ofishin jakadancinta da ke birnin Washington ya fitar tana mai cewa babu wani kutsen da ta yi a harkar zaɓen Amurka.

    Haka kuma bincike da shari'o'i da dama da aka gudanar a matakai daban-daban sun kasa gano wata hujja da ke tabbatar da zargin maguɗi a zaɓen.

  4. An ci gaba da musayar wuta tsakanin Iran da Amurka

    hari

    Asalin hoton, Reuters

    An kwana na shida a jere na musayar wuta tsakanin Amurka d Iran bayan karyewar yarjejeniyar tsagaita wuta da ɓangarorin biyu suka cimma.

    Amurka na kai hare-hare a wasu yankuna na ƙasar Iran, yayin da a nata ɓangare, ita ma Iran ɗin ke ci gaba da mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan wasu cibiyoyin Amurka a yankin Gulf.

    Kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun ce an ji fashe-fashe a birnin Bushehr, inda a nan ne tashar nukiliya ƙasar take.

    Haka kuma suna bayar da rahoton cewa mutum uku sun mutu, yayin da wasu tara suka jikkata, sakamakon hare-haren da aka kai kan wasu gadoji a wani gari da ke kusa da mashigin ruwan Hormuz.

    A farkon makon da muke ciki ne shugaba Trump ya yi barazanar kai wa gadoji da tashoshin wutar lantarkin ƙasar hari idan Iran ta ƙi ba da ikon Mashigin ruwa na Hormuz.

    Rundunar sojin Kuwait ta ce ta girke na'urar kare sararin samaniyarta domin tunkarar hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ke kaiwa.

  5. Assalamu alaikum

    Mabiya shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, haji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yui mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.