Wane zaɓi zai rage wa Isra'ila idan Amurka da Iran suka cimma yarjejeniya?

Amurka

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Saeed Jafari
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Ana ta ƙoƙari domin ganin an cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran domin a tsagaita wuta, sannan a wani ɓangaren kuma ana cigaba da tattaunawa kan abin da yarjejeniyar ke nufi ga ƙasar Isra'ila.

Yanzu babbar tambayar ita ce shin za a cimma yarjejeniyar, sannan kuma ana tambayar me Isra'ila za ta yi, ko kuma wane zaɓi zai rage mata idan har Iran da Amurka suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta?

A kafofin watsa labaran Isra'ila, masana tsaro suna tafka muhawara kan hanyoyin da Isra'ila za ta bi da matakan da suka kamata ta ɗauka.

Wace yarjejeniya ce Isra'ila take fargaba?

Daga cikin manyan abubuwan da suke ɗaga hankali ga Isra'ila akwai sake tsara yarjejeniyar JCPOA, wadda ta taƙaita shirin nukiliyar Iran, amma ta amince Tehran ta cigaba da samar da makamai da jirage marasa matuƙa da wasu fasahar zamani.

Jaridar "The Times of Israel" ta ruwaito a kwanakin baya cewa Isra'ila na fargabar idan aka cimma yarjejeniya, ba za ta samu asalin muradun da suka sa ta shiga yaƙin ba.

Jaridar ta ƙara da cewa a yanzu ba dole ba ne burin Isra'ila ya kasance samun "cikakkiyar nasara" face samun tabbaci daga Amurka a kan daƙile shirin nukiliyar Amurka da kare ta daga barazanar Hezbollah.

Sai dai kuma babu tabbacin hanyoyin da Isra'ila za ta bi domin samun nasarar abin da take so ɗin.

Danny Citrinovich, wani mai bincike a cibiyar nazarin tsaro ta Isra'ila kuma tsohon shugaban sashen sa ido kan Iran a cibiyar nazarin harkokin leƙen asiri ta Isra'ila ya wallafa a shafinsa na X-N cewa yarjejeniyar da ake shirin shiga tsakanin Amurka da Iran "babban ƙalubale ne ga Netanyahu."

Sai dai ba kowa ba ne a Isra'ila yake da irin wannan tunanin, inda wasu ke ganin kowace irin yarjejeniyar aka cimmawa ba ta da amfani matuƙar ba a cimma nasarar fara yaƙin tun a farko ba.

Zaɓi na farko: Tsaiko ga shiga yarjejeniyar

Ɗaya daga cikin zaɓin da Isra'ila da shi shi ne ta tabbatar ta yi ƙafar-rago ga cimma yarjejeniyar.

A wata muƙala da cibiyar nazarin tsaro ta Isra'ila ta fitar a ranar 6 ga watan Mayu, tsohon mai ba shugaban Isra'ila shawara kan tsaro Yaakov Amidror ya ce babban abin da ya kamata Isra'ila ta nema shi ne dakatar inganta sinadarin Uranin da taƙaita samar da makamai masu linzami.

Sai dai wasu masana na gani giɓin da ke tsakanin muradun Isra'ila da abin da gwamnatin Amurka ke nema na ƙara faɗaɗa.

Ilan Berman, mataimakin shugaban cibiyar tsare-tsare kan harkokin wajen Amurka ya bayyana a wata tattaunawarsa da BBC cewa Isra'ila ce za ta iya shiga tsaka mai wuya idan aka cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran, musamman idan yarjejeniyar ta ƙunshi taƙaita harkokin Isra'ila a Lebanon da ma yaƙi da Hezbollah.

Berman ya ƙara da cewa akwai yiwuwar dole Isra'ila ta haƙura ta amince da abubuwan da Amurka ta samar daga yarjejeniyar.

Iran da Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Maimaita abin da ya faru da yarjejeniyar JCPOA

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani zaɓin ga Isra'ila shi ne wataƙila ƙasar ta waiwayi abin da ta shiga bayan yarjejeniyar JCPOA ta 2015.

A lokacin wancan yarjejeniyar, gwamnatin Benjamin Netanyahu ta samu saɓani da shugaban Amurka na wancan lokacin Barack Obama.

A watan Maris na shekarara, ya yi jawabi a gaban majalisar Amurka bayan ƴan jam'iyyar Republican na majalisar sun gayyace shi, inda ya bayyana cewa yarjejeniyar ta JCPOA babbar barazana ce ga wanzuwar Isra'ila.

A lokacin ne ƙungiyoyi da cibiyoyin kamun-ƙafa, musamman AIPAC suka fara ganganin yaƙi da yarjejeniyar JCPOA. A lokacin ne wasu kafofin Amurka suka ruwaito cewa AIPAC ta kashe miliyoyin daloli wajen ɗaukar nauyin tallace-tallace da kamun-ƙafa a majalisar Amurka da sauran ƴansiyasa domin dakatar da yarjejeniyar.

Duk da cewa ba ta samu nasarar hana shiga yarjejeniyar ba, masu alaƙa da Isra'ila a ciki da wajen ƙasar sun cigaba da adawa da ita, inda har Netanyahu ya taɓa bayyana yarjejeniyar da "bala'i,", sannan suka cigaba da matsa lamba har Trump ya fice daga yarjejeniyar a 2018.

Yanzu masana a Isra'ila na fargabar sabuwar yarjejeniyar da za a shiga za ta fi muni da illa ga Isra'ila a kan ta JCPOA, saboda yanzu Iran za ta hau teburin sulhu ne da yaƙinin cewa yaƙin ma bai ba Amurka abin da take so ba, don haka za ta buƙaci ƙarin abubuwa da yawa.

Isra'ila na da zaɓin jinkiri da ɗaga tattaunawa kan duk wata matsala da take da tsauri da muhimmanci zuwa gaba.

Wannan ne zai iya ba Isra'ila dama ta yi amfani da salon da ta yi amfani da shi a lokacin JCPOA.

Zaɓi na 2: Tabbatar da ƴancin "ci gaba da yaƙi"

Wani zaɓi da Isra'ila ke da shi shi ne tabbatar da ƴancinta "na cigaba da yaƙi," domin cigaba da kai hare-hare a Iran da wasu wuraren daban a yankin.

Michael Rubin, wani mai bincike a cibiyar kasuwanci ta Amurka kuma tsohon jami'i a hedkwatar tsaron Amurka ya ce idan ba a saka Iran a cikin yarjejeniyar ba, lallai dukkan matsalolinta a teburin sulhun za a bar su.

Sai dai ya yi amannar cewa ba dole ba ne Isra'ila ta amince da yarjejeniyar da ba tare da ita aka shiga ba, kuma ba ta sanya hannu ba.

Rubin ya ƙara da cewa idan Isra'ila na tunanin Iran na barazana ga wanzuwarta, "babu abin da zai hana ta kai mata hari," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, "Trump na tunanin shi ne yake da wuƙa da nama wajen samar da zaman lafiya."

Haka kuma ko a cikin ƙasar, ba kowa ba ne ya amince da cigaba da yaƙin a matsayin hanya mai ɗorewa.

Jaridar Haaretz ta ruwaito cewa ba tare da taimakon Amurka ba, Isra'ila ba za ta iya daɗewa tana yaƙin ba, musamman idan Washington ta fifita hanyar diflomosiyya.

Zaɓi na uku: Komawa yaƙin sunƙuru

Idan sabuwar yarjejeniyar ta hana Isra'ila cigaba da kai hare-hare, za ta iya komawa yaƙin sunƙuru.

Za ta iya cigaba da yaƙin ta hanyar farfaganda da amfani da fasahar zamani da kisan ɗauki ɗaiɗai da daƙile wasu matakan Iran da sauran su.

Kafar Ynet wadda take da alaƙa da Isra'ila ta bayyana a wani rahoto da ta yi a ranar 22 ga watan Maris na 2026 cewa shugaban Mossad Cif David Barnia ya shaida wa Netanyahu kafin fara yaƙin cewa za su iya haifar da tashin-tashina a ƙasar Iran

Sai dai mai sharhi kan harkokin yankin, Raz Zimet ya bayyana cewa Iran na da tsarin gwamnati mai kyau, wanda ke taimaka mata wajen daƙile matsalolin cikin gida da zarar sun tashi.

Zaɓi na huɗu: Mayar da hankali kan Hezbollah da sauran ƙungiyoyi

Bayan batun nukiliya, daga cikin manyan matsalolin Isra'ila game da Iran akwai fafutikar ƙarfin iko a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman yaƙi da ƙungiyoyin da suke samun goyon bayan Iran kamar su Hezbollah ta Lebanon da wasu a Syria da Yeman da Iraq.

Hukumomi a Iran sun nanata buƙatar a sanya Lebanon a cikin duk wata tattaunawa da za a yi domin tsara shiga yarjejeniya. Wannan zai iya taƙaita yunƙurin baza ikon Isra'ila kan ƙungiyoyin, amma sai dai babu tabbacin ko gwamnatin Netanyahu za ta ɗabbaƙa abin da amince.

Wannan ya sa wasu masanan suke ganin a irin wannan yanayin, Lebanon da Hezbollah za su taka muhimmiyar rawa wajen cimma yarjejeniyar.

Max Abrams, masanin harkokin siyasa kuma farfesa a jami'ar Northeastern University da ke Amurka ya bayyana cewa a yanzu Isra'ila na nuna alamar miƙa wuya ga dukkan sharuɗɗan da Trump ya gindaya.

Abrams ya ce ba ya tsammanin Netanyahu zai ƙi amincewa da abubuwan da Trump zai tsara a game da yaƙin

Sai dai ya ƙara da cewa za a iya cigaba da samun saɓani a tsakanin Lebanon da Hezbollah da Iran, inda ya ce yana tunanin Isra'ila za ta iya cigaba da aikinta na soji ko da kuwa hakan zai illata alaƙar Amurka da Iran.

Ƙalubalen Isra'ila

Mace

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Sai dai duk da zaɓukan da Isra'ila ke da su, ƙasar na fuskantar ƙalubale masu yawan gaske.

Duk yaƙin da aka yi, yana buƙatar kuɗaɗe, sannan yana taɓa tattalin arziki da kuma ƙalubalen ƙaruwar dogara da Amurka da Isra'ila ke yi, musamman wajen makamai da siyasa.

Jaridar The Guardin ta Birtaniya ta ruwaito a ranar 25 ga Mayu ta ruwaito cewa, "yanzu Isra'ila ta dogara ne kacokam kan shugaban Amurka," kamar yadda ta ruwaito daga marubucin kafar Yedioth Ahronoth, Nahum Barnia.

Akwai kuma masu yaƙinin cewa ko da an shiga yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka, ba dole ba ne yaƙin ya tsaya.

Cibiyar nazarin tsaro ta Isra'ila ta wallafa a wani nazari ta yi game da yaƙin, inda ta ce hare-haren Amurka da Isra'ila za su taƙaita cigaba da shirin nukiliyar Iran, amma kuma a wani gefen ta ce hakan ba zai daƙile barazanar Iran baki ɗaya ba.

Sharhin ya ƙara da cewa yarjejeniyar za ta iya taƙaita shirin nukiliyar Iran, amma kuma za ta taƙaita yunƙurin Iran na cigaba da yaƙi.

Sai dai ana tunanin gwamnatin Isra'ila za ta iya amincewa da yarjejeniyar ko da kuwa ba haka ta so, inda dole ta koma teburin shawara da tunanin wasu hanyoyin da za ta bi da Iran.

Ta wannan hanyar za ta iya amfani da tsarin matsin lamba ga Amurka da yaƙin-sunƙuru da mayar da hankali kan Hezbollah..

Amma lallai idan aka samu nasarar cimma yarjejeniyar tsakanin Amurka da Iran, babbar tambayar da za a yi Netanyahu, shin wace nasara ya ci daga yaƙin?

Ba a wargaza Iran ba bayan yaƙin, sannan har yanzu tsarin gwamnatin na cigaba da gudana daidai, inda har zuwa yanzu babu wata tankiya da aka samu bayan samun sabon jagoran addinin ƙasar.

Sannan kuma yaƙin ya nuna cewa Iran za ta iya amfani da mashigar Hormuz wajen takure tattalin arzikin duniya.

Don haka masu sukar Netanyahu za su iya Isra'ila ba ta samu wata nasarar shiga yaƙin ba.