Seriki Abbas: Tarihin yadda kasuwancin bayi ya kasance a Najeriya

Sarƙoƙi
Bayanan hoto, Sarƙoƙin da ake ɗaure bayi da su
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Atlantika, ƙasaitaccen teku ne mai haɗa nahiyoyi. Amma can a ƙarƙashinsa, wani labari ne na baƙar wahala da azabtarwa da keta haƙƙin bil'adama.

Wannan na cikin muhimman wuraren tarihin cinikin bayi a Najeriya. Tsakanin ƙarni na goma sha biyar zuwa na goma sha tara, dubban ƴan Afirka ne suka bi ta nan.

Kafin a kai su bakin teku, ana tsare bayi a gidaje. Maza da mata da yara suna shafe kwanaki ko ma makonni cikin ƙunci da ƙangi da mafi munin wulaƙancin rayuwa. An raba iyalai da juna, an ƙwace musu asalinsu da martabarsu, an kuma kwashi ƴancinsu an wurga cikin teku, tun ma kafin tafiyarsu ta fara.

A bakin Tekun Atlantika, a garin Badagry da ke kudu maso yammacin Najeriya, iskar teku na kaɗawa a hankali a tsibirin Gberefu.

Yana da wuya mutum ya yi tunanin cewa wannan bakin teku mai cike da tarihi wanda a yanzu yake haifar da natsuwa ya taɓa kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da suka fi tayar da hankali a tarihin bil'adama.

Ƙarni bayan ƙarni da suka gabata, dubban ƴan Afirka da aka bautar sun tsaya a wannan wuri bayan doguwar tafiya mai cike da azaba daga ƙauyuka daban-daban na Yammacin Afirka. An ɗaure musu hannaye da sarƙoƙi, an sauya musu suna da makomarsu.

A gabansu akwai jiragen ruwa da ke jiran su domin kai su Turai da nahiyar Amurka. A bayansu kuma akwai ƙasarsu ta haihuwa, wadda da yawa daga cikinsu ba za su ƙara gani ba har abada.

Bautar bayi

Yayin da yake tsaye tsakanin tsofaffin sarƙoƙi masu tsatsa da sauran kayayyakin tarihi a Gidan Adana Kayan Tarihin Bayi na Iyalan Mubee, mai kula da gidan tarihin, Simon Stone, wanda aka fi sani da Cornerstone, ya yi bayani cikin damuwa da jimami.

"Ko wane kayan tarihi da ke nan yana ɗauke da labari. Amma gidan Seriki Abbas ne ya fi taɓa zuciya. Idan ka ga inda aka tsare bayi da kuma sarƙoƙin da suka shafe fiye da shekara 500, hakan yana Sanya wani irin raɗaɗi a zuciyar mutum," in ji shi.

Sai ya yi ɗan shiru kafin ya ci gaba da bayani yana nuna tsofaffin sarƙoƙin.

"Kamar yadda kuke gani, har yanzu alamun wannan tarihi na nan. Waɗannan sarƙoƙi da wannan gida hujjoji ne na zahiri da ke tabbatar da abin da ya faru. Duniya ta san wannan tarihi na ƙangin bauta."

A cewarsa, Badagry ba gari ba ne kawai kamar saura, inda ya ƙara da cewa wata cibiyar tarihi ce da ke ci gaba da wanzuwa.

"Kamar yadda kuke gani," in ji shi, "Badagry ta kasance ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwancin bayi. Akwai gidajen tarihi, tekun da ake tafiya da bayin. Waɗannan duk sun taka muhimmiyar rawa a lokacin cinikin bayi, sai kuma tekun Atlantika. Wannan ne ya sa Badagry take da matuƙar muhimmanci."

Yadda ake kasuwancin bayin

Barracoon
Bayanan hoto, Ɗakunan da ake ajiye bayi kafin a tafi da su
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An tsara tsarin cinikin bayi ne cikin wani irin yanayi mai tsanani da tashin hankali.

Ana kamo maza da mata da yara daga ƙauyukan cikin ƙasa, sannan a tilasta musu yin tattaki zuwa Badagry, inda ake miƙa su ga dillalan bayi.

Daga nan ne kuma ake loda su cikin jiragen ruwa domin tsallaka Tekun Atlantika, tafiyar da ba ta da dawowa.

Tun da farko, Simon Stone ya nuna yadda ake ɗaura manyan kacar ƙarfe mai nauyin tsakanin kilo 15 zuwa 20 a wuyar bayi. Ya kuma nuna rodin da ake ƙonawa ana amfani da su wajen yi wa bayi tambarin Alamar mamallakarsu ta hanyar ƙona fatarsu, sannan ya bayyana irin azabar da ake yi wa waɗanda suka yi yunƙurin tserewa.

"Bayi ba su da wata suna. Sun kasance suna amfani da sunayen masu gidansu ne."

Har ma yin magana laifi ne a zamanin.

Saboda tsoron kada bayi su shirya tawaye, masu iyayen gidansu sukan saka wa wasu bakin sakatar ƙarfe da ke hana su magana. Sai dai duk da haka, hakan bai hana su samun hanyar sadarwa ba a tsakaninsu, ''sai suka koma amfani da alama da motsin jiki wajen sadarwa."

Daga cikin abin da ya fi ɗaga hankali a harkar akwai yadda ake tislata musu shan ruwa.

Stone ya bayyana yadda ake kawo bayi rukuni-rukuni, mutum 20 a lokaci guda, hannayensu ɗaure a baya, sannan a tilasta musu su sunkuya domin shan ruwa daga wani makaken bokitin ƙarfe sau ɗaya kacal a rana. Kaifin bakin kwanon yakan yanke musu wuya, jini ya zuba a cikin ruwan.

''Amma hakan nan za sus ha ruwan saboda ba su da zaɓi. Duk wanda ya ƙi shan ruwan, ba zai sake samun wani ruwan ba sai kuma gobe."

A kasuwar Vlekete ce ake zuwa cin kasuwar bayi, wadda rahotanni suka bayyana ta a matsayin kassuwa mafi girma a Afirka ta Yamma.

A duk ranar kasuwa, ana zuwa a baza bayi, dillalai su saya, sannan waɗanda suka yi kwantai a mayar da su cikin rami.

''Ramin babu rufi, ida ana ruwa haka zai buge su duk da cewa a yanzu an yi rufi, sannan a ciki fitsari da bahaya."

A cikin gidan Seriki Abbas William da ake kira Brazilian Barracoon, ana tsare bayin a ɗakuna masu matuƙar ƙunci kafin a tura su cikin jiragen ruwa. A baya gidan na da ɗakuna 40, amma yanzu biyu ne kawai suka rage.

A gidan ne aka adana bayin da aka saya daga kasuwa, suna jiran ranar da za a kwashe zuwa teku domin tafiya.

Sai kuma wurin da ake kira "Point of No Return" wato babu dawowa. A nan za a zuba bayi cikin jiragen ruwa domin tafiya zuwa can ƙasashen ƙetare. Mafi yawansu, wannan ne karon ƙarshe da suka taka mahaifarsu Afirka.

Rawar da ƴan Najeriya suka taka

Seriki Abbas
Bayanan hoto, Seriki Abbas Williams

A duk lokacin da ake maganar cinikin bayi, an fi ambaton turawan mulkin mallaka, duk da cewa suna da ma'aikata, kamar masu iya magana ke cewa 'da ɗan gida a kan ci gida."

"A wasu lokuta Turawa ne suka tilasta mutane da bindiga. Amma a wasu lokutan kuma, wasu ƴan Afirka ne suka sayar da ƴan'uwansu ga masu cinikin bayi."

Ɗaya daga cikin mutanen da tarihin Badagry ya fi ambatawa shi ne Seriki Williams Abass, wanda tsohon gida adana bayinsa ya koma gidan tarihi.

A cewar Margaret, mai kula da gidan tarihin, an kama Abass tun yana ɗan shekara shida aka sayar da shi a matsayin bawa. Daga baya ya samu 'yancinsa, ya yi karatu a Brazil, sannan ya koma Badagry.

Amma maimakon ya dawo a matsayin wanda aka zalunta, sai ya zama ɗaya daga cikin manyan dillalan bayi a garin.

Labarinsa na nuna irin yadda tsarin ya kasance mai rikitarwa, inda wasu daga cikin waɗanda suka taɓa zama bayi suka rikide zuwa masu taka rawa a tsarin da ya taɓa bautar da su.

A cikin gidan tarihin akwai kayayyakin da ke nuna yadda aka mayar da rayuwar ɗan Adam tamkar wata haja ta kasuwanci.

An ce ana iya musanya babbar bindiga guda da bayi kusan 100. Ƙaramar bindiga kuma tana da darajar bayi 40. Haka kuma lema, giya da sauran kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje sun kasance cikin abubuwan da ake musanya da rayuwar mutane.

Yaya batun biyan diyya?

Lemar Seriki Abbas
Bayanan hoto, Lemar da aka yi musayar bayi 10 da ita

Har yanzu gadon bautar da aka yi wa ƴan Afirka na ci gaba da tasiri a muhawarar da ake yi a sassa daban-daban na duniya. Ana ƙara samun kira a Afirka, ƙasashen Caribbean da kuma tsakanin 'yan asalin Afirka da ke zaune a ƙetare, ciki har da a Majalisar Ɗinkin Duniya, kan batun biyan diyya.

Stone ya yi magana kan wannan batu cikin taka-tsantsan.

"Tarihin bautar da aka yi wa mutane yana da zurfi ƙwarai, har mutane da yawa ba su fahimci yadda tsarin ya kasance ba."

Ya amince cewa Turawa ne suka ƙirƙiro tare da faɗaɗa cinikin bayi ta Tekun Atlantika, amma ya kuma yarda cewa wasu ƴan Afirkasun taka rawa a wasu ɓangarorin wannan tsarin.

A ganinsa, abin da ya fi muhimmanci fiye da diyya shi ne "ƴan Afirka mu samu ƴanci cikakke," in ji Stone.

"Amma idan za a biya diyya ta kuɗi, ina ganin ya kamata a bai wa baƙaƙen fata na Amurka."

Tafiyar dawowa gida

Atlantika
Bayanan hoto, Tekun Atlantika da ake ban-kwana domin tafiya

Yayin da yamma ke ƙaratowa a tsibirin Gberefu, Tekun Atlantika ƙara lumshi yake yi da ɗaukar hankali mai kallo.

Tekun da a da jiragen bayi ke bi suna kwashe mutane daga Afirka, shi ne yanzu ke dawo da zuriyarsu domin neman asalinsu.

Wasu na zuwa daga Brazil. Wasu kuma daga ƙasashen Caribbean, Turai da Amurka.

Da yawa daga cikinsu kan tsaya su yi shiru a gaban wurin da ake kira "point of no return" wasu sukan zubar da hawaye, wasu su yi addu'a, yayin da wasu ke durƙusawa suna taɓa yashin bakin teku suna tadabburi.

A zamanin da, wannan bakin teku shi ne wuri na ƙarshe da dubban ƴan Afirka suke sallama kafin a tilasta musu shiga ƙangin bauta.

A yau kuwa, mutane na tafiya a wannan hanya suna nishaɗi suna ɗaukar hoto tare da hira, sannan su je su dawo.