Sojojin Najeriya sun kama wasu da ake zargi da kai wa dakarunsu hari a Delta

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta ƙarƙashin rundunar Operation UDOKA sun sanar da kama wasu manyan mambobin wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ake zargi da kai wa sojoji kwanton ɓauna a ranar 4 ga Mayun 2026 a jihar Delta.
Harin ya yi sanadin mutuwar soja ɗaya tare da jikkata wani.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce bayan harin ne sojoji suka ƙaddamar da jerin samame bisa bayanan sirri domin kamo waɗanda suka aikata laifin da kuma ƙwato makaman da aka sace.
Hakan ya kai ga cafke waɗanda ake kira Chiboy, Marathon da Onowu bayan sun tsere zuwa garin Oleh da ke jihar Delta.
Sojojin sun ce waɗanda aka kama sun jagorance su zuwa maɓoyarsu da ke Aggah Plantation a jihar Rivers da kuma Umudike Plantation, inda aka ɓoye makaman da aka sace da sauran makaman da ake amfani da su wajen aikata laifuka.
A yayin samamen, an ƙwato bindigogi da alburusai da dama da sauran kayan aikinsu.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kan waɗanda ake zargin kafin gurfanar da su a gaban kotu, tare da jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.


















