Me ya sa da wuya mu manta masoyanmu na farko?

xxx

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Mutane da dama ba su taɓa mantawa da masoyansu na farko, kuma suna daga cikin abubuwan da suka fi tunawa akai-akai.

Amma me ya sa ake samun haka, muna tuna soyayyarmu ta farko dalla-dalla ko bayan gomman shekaru? Me ya sa tunanin ta/shi ke samun gindin zama a can cikin maƙurar zuciyarmu.

Ƙwaƙwalwarmu na matuƙar riƙe abubuwa a lokacin da muke matasa

Mutane da dama na fara soyayya ne lokacin da suke tsakanin shekara 10 zuwa 19, lokacin da kwakwalwa take kan ganiyar dauka da adana abubuwa. “A irin wadannan shekaru ne kwakwalwarmu ta fi kowane lokaci rike abubuwan da suke faruwa dalla-dalla,” in ji Catherine Lovey, farfesar ilimin yadda jiki ke aika sakonni a jami’ar West Minister da ke Birtaniya.

Ta bayyana cewa kuma kwakwalwa ta fi rikewa da adana bayanai da suka shafi abubuwa masu taba zuciya. Ta yi bayanin cewa a duk lokacin da wani abu ya faru a karon farko a rayuwar mutum, hakan na sosa rai, abu mai tsananin dadi ko kuma radadi, kwakwalwa ta fi rike irin wadannan abubuwa kuma ya zuuna a cikinta na lokaci mai tsawo, in ji farfesar.

Haka nan kuma idan muna yawan tuno abin da ya faru, abin ya fi zama a cikin tunaninmu na tsawo lokaci. Shi ya sa abubuwa masu sosa zuciya suka fi zama a cikin tunanin dan’adam na tsawon lokaci.

A duk lokacin da muka sake tuno da abin muna kara dabbaka shi ne a cikin kusurwar da yake a kwakwalwarmu,” in ji Lovey.

Me ya sa sinadaran balaga suke da matukar tasiri a soyayyarmu ta farko?

Idan wani abu ya faru na matukar jin dadi ko kuma wani na radadi mai kona zuciya, irin yadda muke jin masoyanmu na farko na da matukar tasiri. Catherine Lovey ta ce musamman a tsakanin shekara 10 zuwa 19 akwai wani sinadarin da kwakwalwa ke saki wanda yake karade jiki, wanda ke sanyawa ka ji abu ya shigar maka a rai sosai.

Na farko ana samun karin sinadaran jiki masu motsa sha’awa - kamar estrogen da testosterone - wadanda suke sanyawa mu ji muna son kusantaka.

Daga nan kuma idan aka fara soyayya, kwakwalwa tana sakin wasu sinadarai da ke isar da wasu sakonni, ciki akwai sinadaram serotonin da dopamine da oxytocin, wadannan sinadarai ne da suke da alaka da son kusanci da nishadi da kuma neman zama tare da wani mutum a koda yaushe.

.

Asalin hoton, Getty Images

Soyayyar farko na da muhimmanci wajen cusa ƙauna a zuciya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Alaka ta tsakanin mutum da mutum tushe ne na ci gaban rayuwa da kuma wanzuwarmu a doron kasa.

Ga yara matasa, alakar soyayya ta farko da za su yi abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwarsu, domin a lokacin ne za su ci karo da wata alaka da za ta kusantar da su da wani daban wanda ba daga cikin iyalinsu yake ba.

Catherine Lovey ta bayyana soyayyar farko a matsayin “daya daga cikin abu mafi muhimmanci a rayuwar mutum wanda ya shafi alaka ta mutum da mutum.” A lokacin ne muke koyon yadda za mu amince da wani bare,” in ji ta. “Lokaci ne na shiga wata sabuwar rayuwa.”

Ta ce soyayyar farko ba shiga zuciya kadai take yi ba, a’a, wani mataki ne na ilimin gina alakar kauna, wani abu da yake koya wa mutum yadda zai aminta da wani mutum daban, ya ji yana so kusantakar shi kuma wani mataki na alaka tsakanin mutum da mutum.

A shekarar 1993, wata kwararriya kan tunanin ɗan’adam Dr. Nancy Kalish ta yi nazari kan mutane daban-daban a fadin duniya wadanda suka sake koma wa tsoffin masoyansu bayan tsawon shekaru.

Mafi yawan waɗanda suka koma wa tsoffin masoyansu sun rabu da masoyan da suka haɗu da su ne daga baya ko kuma abokan zaman su sun rasu.

Daga cikin waɗannan mutane, wasunsu sun koma soyayyar gadan-gadan cikin makonni ƙalilan, kuma abin mamakin ma shi ne kashi 72% na mutanen sun auri juna.

Samuwar intanet ta sauƙaƙa yadda tsoffin masoya ko abokai suke sake haɗuwa da juna bayan rabuwa. Duk da cewa soyayyar ta baya wataƙila ba ta yi ƙarfi sosai ba, amma ta yi matuƙar tasiri a zuciya.

Akwai masoyan farko da ba a iya mantawa da su

Kate da Gunther sun haɗu ne a shekarar 1989 yayin da dukkaninsu suke hutu a Devon da ke Ingila. Sun kamu da soyayya nan take.

Gunther ya koma Jamus amma duk da haka sun riƙa ziyaratar juna da kuma tura wa juna wasiƙa.

Kate ta ce bayyana wa Gunther cewa ba za ta ci gaba da rayuwa da shi ba shi ne "abu mafi wahala a rayuwarta". Sun rabu bayan bayan shekara biyu suna soyayya.

Shekara 30 bayan haka Kate ta ga wata wasiƙar Gunther a cikin akwati, kuma daga nan ne tunaninsa ya sake dawowa sabo a zuciyarta.

"Na sharɓi kuka," in ji ta, "na ce a cikin zuciyata 'na ci amanar mutumin kirki ba tare da wani dalili ba.'"

Ta nemo adireshin kamfanin iyalin Gunther inda ta rubuta masu wasiƙa, duk da ba ta tsammanin samun amsa.

Sai Gunther ya amsa, Kate ta ce "sai na ji wayata tana ƙara da ƙarfe 12:36 na rana, a ranar 22 ga watan Nuwamba, sai zuciyata ta buga lokacin da na ga lambar ƙasar Jamus."

Sun kwashe sama da wa ɗaya suna magana, sannan bayan wasu ƴan makonni Guther ya hau jirgi ya tafi Manchester domin haɗuwa da Kate. Ta ce "lokacin da na gan shi, sai ka ce ba mu taɓa rabuwa ba."

Daga baya sun yi aure bayan da Gunther ya ba ta zobe a tsaunin da suka taɓa hawa tare shekaru 30 da suka gabata.

"Ba a kodayaushe ne kake samun irin wannan damar ba," in ji Kate, "amma yanzu ina ganin shi kullum, ba na da na sanin haka." Shi ma Gunther ya amince da hakan, inda ya ce "ba zan ƙara rasa ta ba."