Yadda ɓeraye da ƙwari suka mamaye tantunan Falasɗinawa a Gaza

....
Bayanan hoto, Tarkacen shara sun taimaka wajen yaɗa yawan ɓeraya da ƙwari da ke addabar jama'ar Gaza.
    • Marubuci, Omaima Magdy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A Zirin Gaza, ba hare-hare ne kaɗai ke barazana ko haddasa haɗari ga rayuwar jama'a ba, domin yanzu akwai wata sabuwar matsala da ke fitowa daga ƙasa inda ɓeraye masu ɗauke da cututtuka ke mamaye sansanonin 'yan gudun hijira.

Wadannan ɓeraye na shiga cikin tantuna da daddare, suna lalata kayan mutane tare da barazana ga lafiyarsu, lamarin da ke ƙara tsananta wahalar da mazauna yankin ke ciki.

Kwanaki goma kacal kafin aurenta, wata budurwa mai suna Amani Abu Salmiya na zaune a cikin wata tanti a sansanin Sports Club da ke kudancin Gaza, tana duba ragowar kayan aurenta da ta kwashe watanni tana tanada da suka haɗa da kaya, shimfiɗu da sauran abubuwan da amarya ke buƙata amma ɓeraye sun lalata su.

.....
Bayanan hoto, Amani Abu Salmiya zaune a cikin tantin ta.

Ta ce: "Na nuna wa ƙawayena kayan aurena da na tara, komai ya riga ya kammala, amma washegari sai na ji ƙarar ɓeraye. Da na duba, sai na tarar yawancin kayan ɓerayen sun yaga su kuma sun cinye su." kamar yadda ta bayyana wa BBC News Arabic.

Ta kara da cewa, "Asarar ba ta tsaya ga kayan da suka lalace ba ne kawai, na ji zafin lalacewar kayayyakin sosai har cikin zuciyata. Na yi kokari matuƙa wajen haɗa waɗannan kayan aure. Kuma komai na da tsada amma duk da haka ba a tsira da su ba. Mun shirya kai kayan domin iyalan ango su gani amma abin da ya faru ya girgiza mu ƙwarai."

.
Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin kayan da ɓerayen suka lalata.

Duk da tsagaita wuta da aka sanar a watan Oktoban 2025, kusan mutane takwas cikin goma daga cikin miliyan 2.2 na al'ummar Gaza har yanzu na zaune ne a sansanonin gudun hijira, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Gidaje da dama sun lalace gaba ɗaya, yayin da kusan rabin yankin ke karkashin ikon sojojin Isra'ila.

Ana sa ran tantunan su zama mafaka na wucin gadi, amma a zahiri ƙasar da aka kafa su a kai ta zama wata sabuwar barazana ta yau da kullum, sakamakon yawaitar ɓeraye da ƙwari.

Tantunan ƴan gudun hijira

"Kwanan nan ma dai, ɓeran ya fito ya zo kanmu," in ji Amani.

"Muna kwashe dare muna sanya tubali da itace domin toshe wurare, amma duk da haka ɓerayen na ci gaba da shiga."

Wani mutum mai suna Basel Al Dahnoun, wanda ya tsere daga birnin Beit Lahia kusa da iyakar Isra'ila, na fama da ciwon koda da kuma ciwon suga.

Hakan ya sa bai ji lokacin da wani ɓera ke cizon yatsar ƙafarsa ba, sai da matarsa ta tashe shi bayan ta ga jini na fita daga ƙafarsa.

Basel Al‑Dahnoon da bandaji a ƙafarsa da ɓera ya ciza.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce: "Ƙafar da ciwon sugar ta shafa na bukatar kulawa ta musamman amma yanayin da muke ciki yana da matuƙar wahala," in ji mutumin mai shekaru 47.

"Ɓeraye da sauro sun mamaye ko'ina kuma haɗarin kamuwa da cututtuka na ƙaruwa yayin da lokacin zafi ke ƙaratowa."

Ya ƙara da cewa: "Rayuwa a cikin tantuna ya saka da wuya ake iya jure irin wannan yanayin. Ɓeraye da sauro suna kai mana hari ba tare da tsayawa ba. Yara na kuma suna kwana cikin tsoro saboda yadda suke ganin ƙwari masu yawa ke rarrafe a kusa da su."

Ya bayyana damuwarsa kan cewa: "Lamarin yana da hatsari domin waɗannan ɓeraye na iya yaɗa cututtuka masu tsanani. Ni kuma ina fama da matsananciyar rashin lafiyan jiki da kuma raunin garkuwar jiki."

A farkon watan Afrilu, Ministan Lafiya na Falasɗinawa Majed Abu Ramadan ya gargaiɗi cewa yawaitar ɓeraye a Zirin Gaza na ƙara haddasa barazana ga lafiyar jama'a, inda ya buƙaci Hukumar Lafiya ta Duniya ta gaggauta samar da kayan yaƙi da berayen.

Ma'aikatar lafiyar ta ƙara da cewa taruwar shara da tarkace ya taimaka wajen yaɗuwar ɓeraye da kuma ƙara yiwuwar yaɗuwar cututtuka masu tsanani ta hanyar cizo ko fitsari da kashin su, da kuma wasu ƙwari kamar ƙuda da ƙwari masu tsotsan jini.

....

Daga cikin manyan cututtukan da ake dangantawa da waɗannan ɓeraye akwai;

  • Zazzaɓin jini (hemorrhagic fever)
  • Annobar ƙuraje (plague)
  • Zazzaɓin cizon ɓera
  • Cutar salmonella.

Amma kuma ba ɓeraye kaɗai bane ke barazana ga lafiyar ƴan Gaza. Yayin da lokacin zafi ke ƙaratowa, an fara ganin wasu dabbobi masu jan ciki kamar macizai da kunama a wasu sansanonin.

A sansanin Chalets da ke tsakiyar birnin Gaza, wata yarinya na fama da wata cuta da ake zargin ta samu ne sakamakon cizon wani ƙwaro da ba a gane irin sa ba.

Mahaifiyarta, Ummu Ramez ta ce: "Likitoci sun gaya min cewa cutar virusi ce kuma tana iya ɗaukar kusan kwanaki 30 kafin ta wuce.

Yanzu kwanaki 17 kenan tana cikin wannan hali, muna dogara ga ikon Allah. Ina bata magani ne kawai domin rage radadi – amma tana kwance tana fama da zazzabi mai tsanani."

'Babbar barazana'

Likitã Mohammed Abu Afesh, daraktan ƙungiyar bada agajin lafiya ta Falasɗinawa a Gaza, ya shaida wa BBC cewa lamarin na ƙara tsananta.

Ya ce: "Yaɗuwar ɓeraye ta zama babbar barazana ga lafiyar jama'a, musamman yadda suke cin abinci da abun sha da mutanen ke amfani da su."

Ya kuma kara da cewa an riga an samu mutanen da suka ji kama da cututtuka sakamakon cizo ƙwari da ɓeraye kuma aka kai su asibitoci, duk da cewa ba a da cikakken ƙididdiga, amma ana ganin ƙaruwar lamarin.

Ya gargadi cewa ana ganin wasu nau'ukan ɓeraye da ba a saba gani ba a baya, kuma da yawa, abin da ka iya haifar da mummunan yanayi a wasu sansanoni.

Ya ce hakan na iya jefa rayuwar jama'a cikin hadari matuƙa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

Ya ƙara da cewa rashin hanyoyin magance ko yaƙar waɗannan ƙwari da ɓeraye na ƙara tsananta yanayin, sakamakon lalacewar muhimman abubuwan more rayuwa da kuma haramta shigo da magungunan kashe kwari.

Ya bukaci ƙungiyoyin ƙasashen waje su taimaka cikin gaggawa.

A yanzu haka, wasu matasa na ƙoƙarin magance matsalar da kansu ta hanyar amfani da magungunan gona da kafa tarko a cikin tantuna da kuma kwashe shara daga wuraren zama.

Tarkon kama ɓeya

Mahmoud Al-Amawi ya ce suna ƙoƙarin yaƙar ɓeraye da ƙwari da ƴan kayan da suke da su.

Sai dai yaƙin ya bar Gaza da tarin tarkace sama da ton miliyan 68, ciki har da tarkacen shara dayawa a cewar Majalisar Dinkin Duniya.