Yadda wasu manoma ke cikin damuwa saboda rashin samun ruwan sama a Jigawa

Asalin hoton, Getty Images
Manoma a jihar Jigawa sun bayyana damuwa kan yadda rashin samun isasshen ruwan sama ke nakasa shukar da suka yi, har abin ya fara jefa masu fargabar yadda noman na bana zai kasance a yankin nasu.
Yanzu haka dai, manoman wasu wurare a jihar Jigawa na ganin irin abin na da masu iya magana kan ce, ''Allah daya gari bamban''.
Domin kuwa yayin da ake ta makaka ruwan sama a wasu wuraren, wasu wuraren kuwa suna ta fama da kamfarsa.
Wani manomi da matsalar ta shafa a yankin karamar hukumar Dutse ya shaidawa BBC cewa a yanzu sun koma ga Allah'
''Wani yanki za a yi ruwa, wani yanki ba ruwa, ma'ana za a iya ruwa a cikin gari, idan kuma ka je wajan daji za ka iya samu ba ruwa'' in ji shi.
Ya kuma yi Karin haske kan hanyoyin da suke bi wajan yin shuka.
''Bine gaskiya mu ke yi, gonakin da na ke nomawa, a gaskiya gona daya na iya shukawa a yanzu haka, na shuka gero ne saboda shi gero yana da lokaci''
Ya ce sauran kayan amfani goma suna buhu kuma suna fargaba tsuntsaye ko kwari za su iya afkawa shukar da suka yi
''Muna fuskantar wannan kalubale yanzu haka, wata ta tsiro, wata bata tsiro ba kuma wadda ta tsiro yabanyarta ta na cikin kalubale'' in ji shi
Manomin ya yi ikirarin cewa yawancin mutane basa iya zuwa gona saboda yanayin da amfani yake ciki kuma da dama daga cikinsu sun yi asarar amfanin gonarsu
''Yawancin sun yi asarar amfaninsu,irin kamar gyada da take tsada yanzu a wannan lokaci, za ka ga mutum ya shuka gyada amma ta riga ta kone kuma wannan rashin ruwan ya jefa manoma da dama cikin tashin hankali'' in ji shi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai masana harkar noma sun ce akwai mafita, idan dai har za a bi shawarwarin da suka kamata.
Farfesa Shehu Musa Alhaji, na sashen tattalin arzikin noma da kiwo na jami'ar Bayero ta Kano, ya yi karin bayani game da irin wannan matsala
''Sanin kowa ne cewa yanayi ya riga ya canza kuma ya zo da abubuwa da yawa, lokacin da ake sa ran ruwa zai zo sai ka ga bai zo a inda ake sa ran zai ba.Wani lokaci ma a inda ba a tunanin ruwan kuma sai ya zo, sai kaga ya zo a inda b aa tunanin zai zo''
''A wannan gabar manoman nan da shukarsu ta bushe, to bai kamata su sake shuka ba sai sun tabbatar damina ta kankama, kasa ta jika sannan sai su nemo iri na zamani wanda baya daukar dogon lokaci misali wanda ba zai kai kwana 120 ba''
Sannan su nemi iri wanda kwari da cututtuka basu cika damun irinsa ba kuma su rika taamali da malaman gona da suke kusa da su, su rika basu shawara in ji shi
Wannan lamari dai yana nuni ne da irin yadda sauyin yanayi ke ci gaba da zama gagarumar barazana, musamman ma yadda abin ya shafi harkar noma da samar da abinci a Najeriya, kuma yake matukar bukatar a kara matsa kaimi wajen shawo kansa.











