Dalilanmu na tsawaita wa'adin rijistar ƴan jam'iyyu - INEC

Farfesa Joash Amupitan

Asalin hoton, INEC/FB

Bayanan hoto, .
Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ce ta tsawaita wa'adin yi wa ƴa'ƴan jam'iyyu rajista yayin da zaɓen shekara mai zuwa na 2027 ke ci gaba da ƙaratowa.

INEC ɗin ta ce maimakon wa'adin farko da ta bayar na 21 ga watan Afirilun 2026, yanzu an mayar da shi zuwa 10 ga watan Mayun, 2026 matsayin ranar ƙarshe ta karbar rajistar ƴa'ƴan jam'iyyun na Najeriya.

Sai dai an buƙaci jam'iyyun da kar su wuce mako uku wato kwanaki 21 kafin gudanar da zaɓe fitar da ƴan takara.

Mai magana da yawun hukumar zaɓen, Zainab Aminu ta ce hukumar zaben ta fitar da sabon jadawalin ne bayan ƙorafi ko jan hankali da jam'iyyun siyasar ƙasar suka gabatar wa da INEC ɗin, shi ne ya sa suka ɗauki wannan mataki.

"Dogaro da sashen sabuwar dokar zaɓen 2026 sashe na 77 sakin layi na huɗu da ya buƙaci dukkan jam'iyyu su gabatar da rajistar ƴan jam'iyyarsu kwanaki 11 kafin gudanar da zaɓukan cikin gida, shi ya sa aka samar da wannan sauyi", in ji Zainab Aminu.

Hukumar zaɓen ta tsayar da 23 ga watan Afirilun zuwa 30 ga watan Mayun, 2026, wanda hakan ba ya rasa nasaba da dalilan da suka sa INEC sake tsawaita wa'adin zuwa 10 ga watan Mayun wajen karɓar rajistar.

Haka kuma ta ce akwai hukumce-hukumce da dokar zaben ta tanada, kan dukkan waɗanda suka gaza gabatar da rajistar ƴan jam'iyyar tasu a kan lokaci.

''Ita hukumar zaɓe na amfani ne da dokoki na zaɓe, da kuma na ƙasa da tanade-tanaden zaɓe, idan har kuma aka ce akwai doka to saba mata akwai hukunci da aka tanada"

To sai dai wasu na ganin wani babban ƙalubale da ke gaban hukumar zaɓen ta Najeriya shi ne rikicin da jam'iyyun siyasar Najeriyar ke fama da shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To amma ta ce: ''INEC ba ta da hurumin shiga cikin rikicin jam'iyyun, kuma ba ta da ikon shiga tsakani sai dai mu bayar da shawara gare su, da su tsaya su warware matsalolin da ke damunsu, domin idan har suka kai tsawon lokaci ba su warware ba, lallai hakan na iya shafar babban zaɓen da ita INEC ɗin ke son gudanarwa.''

A makon da ya gabata ne dai hukumar ta INEC ta ce shugaban hukumar ya miƙa wa jam'iyyun kundin tanade-tanaden domin su yi nazari a kai kuma su tabbatar da sun tafi daidai ta dokar zaɓe da aka sanya wa hannu ta 2026.

Dokat da ta haɗa da gudanar da zaɓukansu na cikin gida (na jam'iyyu), da yin rijista da kuma soke rijistar jam'iyyun siyasa, sai haɗakar jam'iyyu domin zama jam'iyya ɗaya gabanin zaɓe.

Sai dai kuma jim kaɗan bayan fitar da jadawalin ne sai, kuma aka jiyo, majalisar bayar da shawarwari ta jam'iyyu na cewa ba ta gamsu da jadawalin da INEC din ta fitar ba.

Hakan dai na zuwa ne yayin da hankalin dukkan jam'iyyun siyarasar ta Najeriya ya fara komawa kan daukar matakai na ganin sun yi nasara tare da dinke dukkan wata ɓaraka ko dai da suke fama da ita, ko suke hasashen na iya kunno musu kai.