Sojojin Najeriya sun gano da lalata masana'antar ƙera makamai a Kebbi

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun gano tare da lalata wata haramtacciyar cibiyar ƙera makamai da ake zargin tana da alaƙa da ayyukan ta'addanci a jihar Kebbi.
A wata sanarwa, jami'in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja ya fitar, ya ce dakarun rundunar sashe na 2 sun kai samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka kutsa wurin da ake zargin ana amfani da shi wajen ƙerawa da safarar makamai.'
''Dakarunmu sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyar ƙirar gida, sannan suka kama mutane biyu da ake zargin masu ƙerawa da safarar makamai ne,'' in ji shi.
Mista Danja ya ce an gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, inda ya ƙara da cewa hakan babban ci gaba ne a ƙoƙarin da suke yi na dakile hanyoyin samar da makamai ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma tarwatsa cibiyoyinsu a yankin Arewa maso Yamma.
Rundunar ta ƙara da cewa ''mutane biyu na tsare a hannun sojoji, inda ake musu tambayoyi domin gano sauran waɗanda ke da hannu a lamarin, da masu ɗaukar nauyinsu da kuma hanyoyin da ake bi wajen samar da makaman.''




























