Yaushe ne INEC za ta rufe shafin wallafa sunayen ƴan takara?

Peter Obi for middle, Atiku/Tinubu

Asalin hoton, Peter Obi/Atiku/Tinubu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (Inec) ta na jiran sunayen ƴan takara daga jam'iyyun siyasa daban-daban da za su fafata a babban zaɓen ƙasar na 2027. Amma yaushe ne wa'din da aka bai wa jam'iyyun zai ƙare ?

Daga Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peter Obi na Najeriya Democratic Congress (NDC) da Atiku Abubakar na di African Democratic Congress (ADC) da sauransu - sai INEC ta tabbatar ta kuma wallafa sunayen a matsayin waɗanda ta amince da su a matsayin ƴan takara a hukumance.

Ya dogara ne da ƙa'idodin dokar zaɓe ta 2026, don haka jam'iyyun da ba su gabatar da sunayen ƴan takara ba, zai yi wuya su fafata a zaɓen mai zuwa.

Yayin da ya rage saura kimanin wata shida a gudanar da babban zaɓen shugaban ƙasa, da na gwamnoni, da ƴan majalisar tarayya da na jihohi a shekarar 2027 – Inec jaddawalin zaben ya bayyana yadda komai zai gudana.

Tun daga watan Mayun 2026 ne jam'iyyun siyasa su ka kammala zaɓukan fidda gwani don zaɓar ƴan takara daban-daban da za su wakilci jam'iyyunsu.

Yayin da wasu jam'iyyun siyasa suka riga suka bayyana sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dattawa da na gwamna, wasu jam'iyyun na maƙale a kotu suna neman warware rikice-rikicen da suka yi musu dabaibayi.

Duk da haka, yayin da duk waɗannan abubuwan ke gudana, bisa dokar zaɓen ta 2026 jadawalin zaɓe ya bayyana a fili lokacin da ya kamata duk jam'iyyun su gabatar da cikakken jerin sunayen ƴan takararsu.

Wa'adin miƙa sunayen yan takarar jam'iyyu

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sashe na 29 (1) na dokar zaɓe ta 2026, ta tanadi cewa jam'iyyun siyasa su miƙa jerin sunayen ƴan takarar kwanaki 120 kafin zaɓen.

Yanzu, a cewar jadawalin zaɓen INEC, daga ranar 27 ga watan Yunin 2026 zuwa 11 ga watan Yuli ne wa'din gabatar da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da na majalisar tarayya.

Wa'adin miƙa ƴan takarar Gwamna da Majalisun Jiha zai fara daga 18 ga watan Yuli zuwa 8 ga watan Agusta 2026.

A cewar INEC, a shafinsu na Intanet ne za a iya gabatar da cikakkun bayanai na ƴan takarar kuma jam'iyyun siyasa za su yi amfani da lambobin shiga shafin domin shigar bayanan ƴan takaran.

A halin da ake ciki, INEC ta shirya bayar da horo na musamman ga dukkan jam'iyyun siyasa don koya musu yadda za suiya shigar da bayanai a shfin don kauce wa duk wani rikici.

Kwamishiniyar INEC ta ƙasa, May Agbamuche-Mbu, ta ce zaɓen ƴan takara muhimmin mataki ne a tsarin zaɓe.

"Samar da ƴan takara ya kasance ɗaya daga cikin muhimman matakai na tsarin zaɓe. Shi ne tublin da mu ke gina zaɓe a kansa, idan har ba samu an zaƙulo ƴan takara ba, babu wani babban zaɓen da za a iya gudanarwa."

Me ya rage wa INEC da jam'iyyu kan miƙa sunayen ƴan takara?

Bayan gabatar da fom ɗin tsayawa takara daga jam'iyyun siyasa, abin da zai biyo baya shi ne INEC ta wallafa cikakkun bayanai kan ƴan takarar.

Ya yi daidai da sashe na 29 (3) na dokar zaɓe ta 2026 wadda ta ta ce a fitar da jerin sunayen ƴan takara a cikin kwanaki 21 bayan an gabatar da su.

A ranar 1 ga watan Agusta ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za ta fitar da sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki yayin da za fitar da na gwamnoni da na majalisar jihohi a ranar 29 ga watan Agusta, 2026.

Daga an yi hakan, jam'iyyu za su iya fara yaƙin neman zaɓe gabanin zaɓukan 2027 da za a fara da na shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya, kafin na jihohi ya biyo baya.

Har ila yau, jadawalin INEC ya ba da damar jam'iyyun siyasa su sauya sunayen ƴan takara kamar yadda sashe na 31 na dokar zaɓe ta 2026 ta tanada muddin bai yi ƙasa da kwanaki 90 kafin zaɓen ba.

Jam'iyyun siyasa na da har zuwa ranar 22 ga watan Agusta da 19 ga watan Satumba domin janye duk wani ɗan takarar da suke son maye gurbinsu a kujerun tarayya da na jihohi.

Bugu da ƙari, bayan duk waɗannan, INEC za ta fitar da wani jerin sunayen ƴan takara da jam'iyyunsu na ƙarshe, aƙalla kwana 60 kafin zaɓen.

Ba za a yi wani sauyi kan wannan jerin sunayen na ƙarshe ba har zuwa ranar zaɓe, kuma jam'iyyun za su ci gaba da gudanar da yaƙin neman zaɓe.

Ko me zai faru da jam'iyyun da ke rikici a kotu?

A halin da ake ciki, an samu wasu jam'iyyun siyasa da ke da matsalolin da ya kamata su magance kafin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 kuma wasu shari'o'in na gaban kotu.

Dangane da ƙorafe-ƙorafen da ake da su bayan zaɓukan fidda gwani, INEC ta gargaɗi jam'iyyun siyasa cewa duk wani zaɓen fidda gwani da aka yi bayan wa'adin ranar 30 ga watan Mayu ba amintacce ba ne.

A watan Yunin 2026, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci INEC da ta soke rajistar jam'iyyun ADC da Action Peoples Party (APP) da Action Alliance (AA) da Accord Party (AP), da kuma Zenith Labour Party (ZLP).

Dalilin da ya sa kotu ta bayar shi ne a cewarta jam'iyyu sun kasa samun kujeru a babban zaɓe da zaɓukan cike gurbi ko kuma sun kasa cika mafi ƙarancin abubuwan da ake buƙata domin shiga zaɓe.

Duk dai a cikin watan na Yuni, kotun ɗaukaka Kara ta Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yanke na soke rajistar jam'iyyun siyasar.

Kotun ta ce umarnin da babbar kotun tarayya ta Abuja ta bayar ya saba wa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

Ga wasu lokutan, wasu jam'iyyu suna da ƴan takara da dama saboda ɓangarorin da ke cikin jam'iyyar.

Gabatar da jerin sunayen ƴan takara ga INEC da kuma wallafa su zai kawo ƙarshen shari'o'in waɗanda aka amince da su a matsayin waɗanda za su tsaya zaɓe a ƙarkashin inuwar jam'iyyar.

Jam'iyyar PDP na daga cikin jam'iyyun da ke da wannan matsalar ta ƴan takarar kujera guda daga ɓangarori daban-daban.