Ina ne tsibirin Larak na Iran da Amurka ta kai wa hari?

Asalin hoton, Reuters
Amurka da Iran sun yi musayar hare-hare bayan dakarun Amurka sun kai farmaki kan na'urorin harba rokoki guda biyu a tsibirin Larak da ke mashigar ruwa ta Hormuz.
Wannan shi ne harin farko da Amurka ta kai wa Iran tun bayan ƙarshen watan Yuli. Rundunar IRGC ta Iran ta ce harin ya kashe mutum biyu tare da jikkata wasu biyun, kuma ta yi alƙawarin mayar da martani da hukunta masu kai harin.
Rundunar Centcom ta Amurka ta ce ta ɗauki mataki na musamman kan wasu dakarun da take zargin suna shirin shimfiɗa nakiyoyi, lamarin da zai iya zama barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.
Iran ta ce ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka da ke Jordan.
Rundunar sojin Jordan ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami guda takwas a safiyar Litinin.
Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya kuma ba da rahoton cewa sojojin Iran sun kai hari da jirage marasa matuƙa kan wani sansanin soji a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wato UAE.
Sai dai Ma'aikatar Tsaron UAE ta musanta cewa an kai hari kan sansanin Al-Minhad, tana mai cewa rahotannin ba su da tushe. Duk da haka, UAE ta tabbatar da cewa ta harbo wani jirgi maras matuƙi.
Bayan harin Amurka, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa wasu bidiyoyin da aka ƙirƙira da fasahar AI a shafinsa na Truth Social, waɗanda suke nuna kamar ana lalata cibiyoyin mai na Iran.
Ɗaya daga cikin bidiyoyin ya ambaci tsibirin Kharg Island, wata babbar cibiyar fitar da man Iran, wadda Trump ya taɓa yin barazanar kai wa hari.
Ina ne tsibirin Larak?

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsibirin Larak wani ƙaramin tsibiri ne na Iran da ke cikin Mashigar Hormuz , a lardin Hormozgan na kudancin ƙasar.
Tsibirin yana kusa da tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas kuma yana bakin mashigar ruwa ta Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar makamashi ta duniya.
Kafin fara yaƙin, kusan kashi 20 na man fetur da iskar gas da ake amfani da su a duniya suna bi ta wannan mashigi.
Tun bayan fara rikicin a watan Fabrairu, zirga-zirga ta mashigar Hormuz ta fuskanci cikas sosai, abin da ya jawo sauye-sauyen farashin mai a kasuwannin duniya.
Rahotanni sun ce Iran na tilasta wa tankokin dakon mai su ratsa ta kusa da tsibirin Larak domin bincike, kuma tana karɓar kuɗin wucewa da ya kai dala miliyan biyu.
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, mai alaƙa da IRGC, ya ce an kai harin Larak ne ta amfani da jirage marasa matuƙa.
Daga baya, IRGC ta ce ta kai harin makamai masu linzami kan sansanonin King Hussein da Al-Azraq da ke Jordan a matsayin ramuwar gayya.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah-wadai da abin da ta kira "ta'addancin sojin Amurka a Larak", tana mai cewa harin da ta kai kan sansanonin Amurka a Jordan ya kasance matakin kare kai da ya dace.
"Ba ma neman yaki, amma za mu mayar da martani mai ƙarfi ga masu kai mana hari," in ji Shugaban Iran Masoud Pezeshkian.
Me ya sa yake da muhimmanci?
- Yana bakin ƙofar mashigar Hormuz, ɗaya daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya wajen jigilar mai da iskar gas.
- Matsayinsa yana ba Iran damar sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa masu wucewa ta mashigin.
- Tsibirin yana cikin jerin wuraren soji na Iran da ke kare yankin mashigar Hormuz.
Mashigar Hormuz
Mashigar Hormuz na tsakanin Iran da Oman ne.
Taswirar tekun ta nuna ɓangarorin da suke da kyau a tsaya, da wuraren da ba a so a tsaya da kuma tudun mun tsira a tsakanin ɓangarorin biyu.
Idan tankokin mai za su wuce, sai su wuce ta kusa da tsibirin Greater da Lesser Tunb - inda ake takun-saƙa tsakanin Iran da ƙasashen Larabawa kan mallakinsa.
Masana sun ce yaƙi na cikin abubuwan da suke jawo tsaiko a hada-hada ta mashigar kamar yadda ya faru a yakin Iran da Iran a shekarar 1980 zuwa 1988.
Hukumar ƙididdigar makamashi ta Amurka US Energy Information Administration (EIA) ta ƙiyasta cewa a farkon shekarar 2023 an yi dakon kusan ganga miliyan 20 na fetur a a kullum ta tekun.
Wannan ke nufin ana kasuwancin kusan dala biliyan 600 na makamashi duk shekara ta tekun.
Duk wani tsaiko a tekun zai iya jawo matsala a hada-hadar man fetur a duniya, wanda nan take za a iya gani ta hanyar tashin farashin man.
Farfesa Ahmad Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur da iskar gas da ke jami'ar Philomath da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Ya ce hanyar ruwa ce da ba ta girma sosai, amma take da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.
"Ita wannan mashiga hanyar ruwa ce wadda tsayinta bai wuce kilomita 33 ba, wadda ta a daidai ƙasar Iran. Kuma hanya ce da jiragen dakon ɗanyen man fetur ke wucewa a kullum."
Ya ce daga jiragen dakon man da ke wucewa ta hanyar, akwai na ƙasashen Saudiyya da Kuwait da Iraqi da sauransu.
"Kullum ana wucewa da gangar ɗanyen mai kusan miliyan 20. Kusan kashi 20 cikin 100 na ɗanyen mai da ake buƙata a duniya," in ji shi.
Masanin ya ƙara da cewa ƙasashen da aka hana fitar da su ne suka fi sayar da man fetur mai sauƙi a kasuwannin duniya, wanda a cewarsa hakan ke taimakawa wajen rage farahinsa.
"Su ne suka sayar da mai mai arha. Misali Iran, kowace ganga tana kashe mata dala 10 zuwa 15 ne, kuma haka sauran suke kashewa. Idan aka ce waɗannan ƙasashen ba sa fitar da mai, sannan kuma dama na sauran ƙasashen yana da tsada, sai farashinsa ya tashi."
Ya yi misali da ƙasar China, wadda ya ce kimanin kashi 90 na ɗanyen da take buƙata daga Iran take saye.
Farfesa Ahmad ya ƙara da cewa datse mashigar zai shafi duniya ne baki ɗaya, ba ma ƙasashen da yake yaƙin ba kaɗai.
"A duk lokacin da farashin mai ya tashi, tattalin arzikin duniya na girgiza, farashin kayayyaki na hauhawa. Wanda hakan ya nuna cewa kowa ma zai ji."
Ya ƙara da cewa ita kanta Iran da ta rufe mashigar za ta ji a jikinta, "saboda tana samar da aƙalla ganga miliyan huɗu a kullum wanda shi ne kashi biyar bisa 100 na ɗanyen man duniya," in ji shi, wanda ke nufin za ta samu ragowar kuɗin shiga.










