Waziri Allah Bar Sarki: Mutumin da ya mulki Kano shi ba sarki ba

Asalin hoton, Zuri'ar Gidan Sarkin Kano Dabo/FACEBOOK
- Marubuci, Khalifa Shehu Dokaji
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 9
A tsarin tafiyar da mulki a kasar Hausa, sarki shi ne wanda ke jagorantar al’umma, umarnin sa ake bi kuma wajibi ne kowa ya yi masa biyayya.
Sai dai game da haka akwai wani abu da ya saba da al’ada wanda ya faru a kasar Kano, wanda ya kunshi wani basarake da ake kira Waziri Allah Bar Sarki.
A tarihin masarautar Kano akwai sunaye da dama da suka yi fice saboda rawar da suka taka a harkokin mulki, siyasa da gudanar da masarauta.
Inda tarihin masarautar kuwa ba zai cika ba sai an taɓo batun Waziri Allah bar Sarki, wanda tarihin rayuwarsa ya kasance abin tattaunawa tsakanin masu bincike da masana tarihi tsawon shekaru.
Wasu masu nazari da masana tarihi na yi masa kallon mutum mai basira wanda ya taka rawa wajen daidaita al'amuran masarautar ta Kano a wani mawuyacin lokaci, yayin da wasu ke danganta tarihin rayuwarsa da tsarin sarautun bayi da ake da shi tun daga tsohuwar Kano.
Barista Murtala Bashari wani masanin tarihi kuma mai bincike da ke Kano, ya ce 'Allah-Bar-Sarki ya yi fice a zamanin da ya yi Wazirci a Kano, wajen inganta tsarin gudanarwa a masarauta, da kawo sabbin tsare-tsare wajen ajiye kayan abinci da rarraba su, da ƙarfafa alaƙar masarautar Kano, da malamai da 'yan kasuwa,' a cewar masanin tarihin.
Barista Bashari ya ce babban abin da ya sa har yanzu ake tuna Allah-Bar-Sarki shi ne yadda ya samu karɓuwa daga fannoni daban-daban na al'umma.
"Ko bayan an cire shi daga sarauta, mutane da dama a cikin masarauta da wajenta sun ci gaba da ganin girmansa. Wanda hakan ya sa har yau sunansa bai gushe daga tarihin Kano ba." In ji Barista Bashari.
Wane ne Waziri Allah Bar Sarki?

Asalin hoton, Zuri'ar Gidan Sarkin Kano Dabo/FACEBOOK
Sunan Waziri Allah Bar Sarki shi ne "Muhammad ibn Ibrahim ibn Muhammad Allah Bar Sarki wanda kuma asalinsa mutumin garin Farin Dutse da ke ƙasar Gwaram, a tsohuwar jihar Kano, wadda yanzu ta koma jihar Jigawa.
A cewar masanin tarihi Barista Murtala Bashari '’Mahaifin Waziri Allah-Bar-Sarki Malam Ibrahim, fitaccen malami ne a zamaninsa a wannan garin. In da ya ke da ɗalibai masu ɗimbin yawa a makaranta, sannan Allah ya ba shi arzikin shanu, da tsuntsaye a gidansa.
Waziri Allah bar sarki ya fara karatu ne a gaban mahaifinsa, tare da sauran ƴan‘uwansa, sai dai “ya tsinci kansa a Kano ne zamanin sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi kafin hawan Sarkin Kano muhammad Bello", a cewar Bashari.
Yadda ya shiga Kano

Asalin hoton, Zuri'ar Gidan Sarkin Kano Dabo/FACEBOOK
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Waziri Allah-Bar-Sarki ya biyo bayan wani samame da mayaƙan Kano suka kai a yankin Bauchi a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi.
"A lokacin mayakan na kan hanyar su ta komawa Kano bayan sun dawo daga Bauchi, sannan suka yada zango a Ruwan Dutse, garin su Waziri Allah-Bar-Sarki, inda a nan suka haɗu da shi Allah-Bar-Sarki, kuma a lokacin ya na ƙaramin yaro ne, da shekarunsa ba su wuce takwas zuwa tara ba."
Masanin ya ce "Barde Abdu shi ne ya ɗora shi a kan dokinsa ya taho da shi Kano saboda yana ƙarami."
Duk da cewar mahaifinsa ya yi ta kira gare su da su, kar su tafi da shi, saboda shi yake fatan ya zama magajinsa, amma suka ƙi suka tafi da shi.
"Bayan sun isa Kano aka shigar da su cikin gidan Sarki don a gabatar da su ga Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi. "
Sai dai Barista Murtala Bashari ya yi wani jan hakali cewar '’Wata ruwayar wadda ke haifar da muhawarar ita ce cewar an kai Allah-Bar-Sarki Kano ne a matsayin bawa'’.
Sai dai ya ce akwai hujjoji da dama da ke nuna cewa ba a taɓa ɗaukarsa kamar yadda ake ɗaukar bayi ba.
Ya kara da cewa tsarin rayuwar da aka ba shi bayan isar su Kano ta sha bamban da wanda ake bai wa bayi.
"A ƙa'ida ba wani bawa da ake bari ya zauna tare da 'ya'yan sarki, ya kwana da su, ya ci abinci tare da su ko ya yi wasa da su. Babu wannan a tsarin Kano."
Sannan ya ce 'hanyar mallakar bawa a masarautar Kano da sauran masarautu, ya haɗa da:
- Samun kyautar bawa, kamar yadda wasu sarakunan ko attajirai suke bayarwa
- Sai kuma yadda wasu masana tarihi ke cewar a ƙarni na 19 a ƙasar Kano ana yin samame domin kamo mutane a mayar da su bayi.
- Sai kuma Waɗan ake siye
- Sai waɗanda aka ciyo a yaƙi.
Rayuwa a gidan Sarki

Asalin hoton, Zuri'ar Gidan Sarkin Kano Dabo/FACEBOOK
Barista Bashari ya ce daya daga cikin abubuwan da suka sauya rayuwar Waziri Allah-Bar-Sarki bayan da aka kai su gidan sarki shi ne abin da ya faru a ranar da aka kai shi fada.
Masanin tarihin ya ce bayan an tattaro yaran da aka kamo domin a gabatar da su ga sarki, lokacin sallar azahar ya yi, kasancewar yadda ya taso cikin tarbiyya, inda mahaifinsa shi yake koya masa addini da salla.
"Da lokacin azahar ya yi sai kawai ya tashi ya yi kiran salla, inda wannan kiran sallah ya j hankalin sarki har yake tambayar wane ne ke kiran sallah a nan kuma? Bayan an sanar da shi wanda ya yi ɗin sai ya sa aka kawo shi gabansa", in ji Bashari.
Ya kuma ce wannan tattaunawar da Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ya yi da Waziri Allah-Bar-Sarki ita ta ja hankalin sarkin da har ta kai ga ya nuna sha'awar zamansa a kusa da shi.
"Da ya yi magana sai Maje Karofi ya fahimci cewar yana da tarbiyya da ilimi, sai ya ce a bar masa shi."
Masanin tarihin ya ce bayan haka ne aka ba shi matsuguni a cikin gidan sarki., aka bai wa Uwar Waje Ka'iyya, ta rike shi, to daga nan ne ya shiga cikin 'ya'yan sarki yana rayuwa tare da su."
Bashari ya ce wannan ma yana daga cikin dalilan da suke ganin bai kamata a ce an sa shi a jerin bayi ba.
Ya ce daga baya ma mahaifiyar Sarkin Kano Abbas ta gane cewa ta san iyayensa, kasancewar ta mutuniyar ƙasar Fagam ce da ke Jigawa.
Allah-Bar-Sarki ya shiga aikin fada

Asalin hoton, Getty Image
Ganin yadda Waziri Allah-Bar-Sarki ya ke kula da bai wa tsuntsayen Sarki abinci, da tsayin lokacin da ake ɗauka ba tare da an sanar da sarkin cewar abinci ya ƙare ko kaji, ko talotalo, ko sauran tsuntsaye da sarkin ke kiwonsu ba su mutu ba ya sa sarki ya ƙara jansa a jika.
To wannan amana ce ta sa aka fara ba shi wasu manyan nauyuka.
"Sarki ya ga yadda yake aiki da gaskiya sai ya ba shi sarautar Galadiman Rumbu."
Barista Bashari ya bayyana cewa Galadiman Rumbu shi ne mai kula da harkokin abinci na cikin gida.
"Shi ne yake kula da duk abin da ya shafi rarraba kayan abinci a cikin gidan sarki."
Daga nan ne, kuma aka sake ɗaga darajarsa zuwa Sarkin Hatsi.
"Shi ne yake kula da duk wani abinci da za a shigo da shi fada. Shi ne yake saya, shi ne yake tsara yadda za a rarraba shi."
Masanin kuma ya ce 'aiki da gaskiya da adalci ya sa Allah-Bar-Sarki ya samu karɓuwa a tsakanin jama'a. Yan kasuwa suna son yin hulɗa da shi saboda ya na ciniki, kuma shi ma zai yi shi cikin adalci", In ji shi.
A cewarsa, hakan ya ba shi babban matsayi a tsakanin malamai da 'yan kasuwa.
Zaman sa Dan Rimin Kano

Asalin hoton, Getty Image
A zamanin Sarkin Kano Abbas ne Allah-Bar-Sarki ya shiga cikin sha'anin mulki musamman na fada saɓanin na kula da abinci zuwa sarautar manyan bayin Sarki da ake da su a Kano wato uku.
'Da aka cire Ɗan Rimi Manuhu sai Sarkin Kano Abbas ya naɗa Allah-Bar-Sarki a matsayin Ɗan Rimi, duk da cewa sarautar tana cikin sarautun bayi, alhalin shi bai taso cikin bauta ba, sannan ba bawa ba', in ji masanin tarihin.
"Sannan a wasu lokuta akan bai wa waɗanda ba bayi ba irin waɗannan sarautu idan Sarkin da ke mulki ya ga irin amanarsa da kusanci da yake da shi da masarauta."
A lokacin da Turawan mulkin mallaka suka iso Kano, Allah-Bar-Sarki ya kasance cikin mutanen da suka fi mu'amala da su.
"Dama aikin Ɗan Rimi shi ne kula da baƙi da isar da saƙonni. Da Turawa suka zo sai ya kasance ya na hulɗa da su, a haka ne har ya samu damar koyon turancin Ingilishi, inda sukan yi magana da shi kuma su fahimci juna", wanda hakan ya ƙara masa ƙima da daraja a Idon Turawa.
Yadda Allah bar Sarki ya zama Wazirin Kano

Asalin hoton, Getty Image
Wani babban ƙalubalen da Allah-Bar-Sarki ya fuskanta shi ne lokacin da Turawa suka yi yunƙurin sake fasalin tsarin yadda masarautar Kano ke gudanar da harkokin mulki.
Kuma wannan na daga cikin kalubalen da masarautar Kano ta taba cin karo da su a tarihi.
A lokacin da turawa suka yi yunƙurin sauke Wazirin kano na wanchan lokaci, wato marigayi Sarkin Kano Abdullahi Bayero (Sarki Alhaji) akwai shirin da zai rage ikon sarki, kuma ya ƙara wa Waziri ƙarfi.
Barista Murtala Bashari ya ce an yi zagin cewar marigayi Sarkin Kano Abdullahi Bayero (Sarki Alhaji), saboda zargin da suke yi masa na cewar idan aka yi umarni, ko aka tattauna wani abu da shi, sai ya je ya sanar da mahaifinsa.
"Suna ganin shi jininsa ne shi ne suka nemi da ya sauya waziri, wanda ba shi da alaƙa da shi, wanda hakan ne ya sa sai ya bayar da Allah- Bar-Sarki, kasancewar tare suka taso kuma amininsa ne, ba tare da cewa rasdan na da masaniyar abin da suka shirya ba"
Bashari ya ce 'akwai Dr Kergil wanda shi ne baturen rasdan din Kano, shi ma gwamnatin sama ta wancan lokacin ke kokawa kan yadda ba sa samun sakamako da ake buƙata wanda shi ne ya kawo tsarin bai wa waziri ƙarfi da mayar da shi kula da harkokin gudanarwa da aka san sarki da yi,' a cewar masananin tarihin.
"Tsarin da ya kawo sai ya sa abin zama bambarakwai, hakan ne ya sa Sarki Abbas ya janye jikinsa daga wasu abubuwa, inda daga nan ne sai Dr Kergil ya fara tunanin mayar da Allah Bar Sarki zuwa Sarkin Kano.
Daga nan ne sai turawa suka koma ba shi dukkan wani aiki da sauran daraja da Sarki ke da shi", a cewar Barista Murtala Bashari.
Duk da hakan shi kuwa bai fasa zuwa ya sanar da Sarki dukkan abun da ake ciki ba.
Masanin tarihin ya ce ”a zamansu na farko sai da Allah bar sarki ya shaida wa Sarki Abbas cewar tunda sun shiryo rashin kirki, zai ajiye musu wazirin ya tafi amma Sarkin Kano Abbas ɗin ya hana shi”.
Haka kuma ya ce duk da cire shi daga sarauta, hakan bai shafi dangantakar da ke tsakaninsa da marigayi Sarkin Kano Abbas ko kadan ba.
Masanin tarihin ya ce 'bayan sauke Waziri Allah-Bar-Sarki daga sarauta an ba shi gida a unguwar Daneji, kuma har zuwa karshen rayuwarsa, Sarkin Kano kan aika a kira shi domin tuntuɓa ko shawarwari kan harkokin da suka shafi mulki da na aminantaka.
Me ya bari a tarihin Kano?

Asalin hoton, Getty Image
Murtala Bashari ya ce '’Waziri Allah-Bar-Sarki ya rasu a shekarar 1917, sannan Sarkin Kano Abbas ya rasu bayan shekara biyu a 1919.’'
Sannan ya ce Allah-Bar-Sarki ya bar ƴaƴa da jikoki masu yawa waɗanda har yanzu suke da alaƙa da masarautar Kano.
Haka kuma wani abu da ake danganta Waziri Allah-Bar-Sarki da shi, shi ne yadda ya kawo sauyi da gyara a tsarin yadda ake rabon kayan abinci a gidan sarki, da ƙarfafa dangantakar masarautar Kano da malamai, da ƴan kasuwa, da inganta tsarin sadarwa tsakanin fadar Sarki da hakimai, zuwa dagatai da sauran al'umma.
Har ila yau, zuriyarsa na ci gaba da taka rawa a cikin masarautar Kano tsawon shekaru da dama bayan mutuwarsa.










