Tottenham na zawarcin Osimhen, Chelsea na bibiyar Chavarria

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tottenham ta gabatar da tayin £55m kan ɗanwasan gaban Galatasaray mai shekara 27, Victor Osimhen, amma ƙungiyar ta Turkiyya ta nemi a ƙara farashin zuwa aƙalla £65m. (Caught Offside)

Ɗanwasan tsakiyar Newcastle da Brazil mai shekara 28, Bruno Guimaraes, ya shirya yin gwajin lafiya domin fara taka leda a Arsenal, a kan kwangila da ta kai £80m. (Athletic - subscription required)

Atletico Madrid na tunanin shiga zawarcin ɗanwasan tsakiyar Manchester City Jack Grealish, amma tana fuskantar barazana daga Everton da Aston Villa masu bibiyar ɗanwasan Ingilan mai shekara 30. (Sun)

Tottenham ta yi tattauna mai armashi da ɗanwasan gaban Liverpool Cody Gakpo, amma ƙungiyar ta ce ba ta da aniyar sayar da ɗanwasan mai shekara 26. (Teamtalk)

Mai tsaron ragar Braga mai shekara 24, Lukas Hornicek ya tsallake gwajin lafiya domin fara taka leda a Newcastle. (Mail - subscription required)

Hull City ta kusa ƙulla yarjejeniyar ɗaukar ɗanwasan gaban Nice mai shekara 22, Mohamed-Ali Cho, a kan £17m. (L'Equipe)

Chelsea ta gabatar da sabon tayi kan ɗanwasan baya mai shekara 28, bayan Rayo Vallecano ta ƙi amincewa da tayin farko na £12.8m da ƙungiyar ta yi wa ɗanwasan Sifaniya Pep Chavarria,. (Teamtalk)

Hull City ta kusa kammala cinikin ɗanwasan bayan Australia mai shekara 18, Lucas Herrington, daga Colorado Rapids a kan £17m. (Sun)

Ƴanwasan Real Madrid biyu, Gonzalo Garcia mai shekara 22 da kuma Cesar Palacios mai shekara 21 sun yi gwajin lafiya a Fulham bayan ƙullar yarjejeniyar sayar da su ga ƙungiyar. (Sky Sports)

Hull City ta shirya yi wa Rangers da Cardiff City shigar sauri wajen sayen ɗanwasan tsakiyar Norway mai shekara 20 Jens Hjerto-Dahl, daga Tromso.(Mail - subscription required)