Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a fagen wasanni BBC Hausa na ranakun 27 ga watan Yuli, zuwa 2 ga watan Agusta2026

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran Gasar Kofin Duniya da aka kammala da kuma sauran labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 27 ga watan Yuli, zuwa 2 ga watan Agusta 2026.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Rogers da Palmer za su samar da sauyi a Chelsea - Alonso

    Kocin Chelsea Xabi Alonso ya ce shirinsa na haɗa ɗan wasan da suka saya £117m Morgan Rogers tare da Cole Palmer a cikin fili zani abu ne da zai samarwa ƙungiyar sakamakon da take so.

    Dan wasan tsakiyar shi ne wanda ya fi duk wani dan wasan Burtaniya tsada a tarihi, bayan sayen shi da Chelsea ta yi daga Aston Villa zuwa Stamford Bridge a makon jiya.

    Yanzu ɗan wasan na hutu ne bayan kammala gasar Kofin Duniya da ƙasarsa ta yi, kuma a gefe guda Chelsea sabuwar ƙungiyarsa ta fara wasannin share fagen kaka a Sydney.

    "A wannan hannun muna buƙatar gogaggun 'yan wasa kuma na yi imanin irin shi ba su da yawa a yanzu haka," in ji Alonso.

    Morgan Rogers ya sanya hannu kwantaragin shekara shida ne tare da Chelsea, kuma akwai zaɓin tsawaita kwantaragin idan ta ƙare.

  2. Chiesa na farin cikin da zamannsa a Liverpool amma yana buƙatar dama

    Dan wasan gaban Italiya Federico Chiesa ya dage kan cewa shi Liverpool ce kawai a gabansa yayin da ake ci gaba da yaɗa jita-jita kan makomarsa a kwallon ƙafa.

    A kaka biyu da ya buga a ƙarƙashin kulawar Arne Slota a Anfield, wasa biyu kacal ɗan wasan gaban ya fara a Premier ya kuma ci kwallo biyar ne kawai a wasanni 50 da ya buga a duka gasanni.

    Dan wasan mai shekara 28 ya koma Anfield ne daga Juventus ne kan kuɗi £12.5m a 2024 kuma kwantaraginsa zai ƙare ne a 2028, ya shaida wa jaridar La Gazzetta a watan Yuni cewa : " Idan ban samu damar buga wasa a kai a kai ba, zai nemi wani wurin na tafi."

    Amma bayan cin kwallo ɗaya da ya yi a wasan da suka yi na sada zumunta ranar Asabar da Sunderland ƙarkashin Araola ya shaida wa manema labarai cewa "Lokaci ya yi yanzu, ina farin ciki a Liverpool, ina son ƙungiyar da komai nata da magoya baya".

  3. Ina Vinicius ya nufa Arsenal ko Real Madrid ?

    Ko shakka babu akwai sauran taƙaddama a makomar ɗan wasan gaban Real Madrid Vinicius Jr.

    Dan wasan wanda babu ja yana cikin 'yan wasan kwallon ƙafa na duniya mafiya shahara gobensa ba ta bayyana ba ya zuwa yanzu.

    Dan Brazil ɗin zai shiga shekaarsa ta ƙarshe ne a kwantaraginsa da ƙungiyar ta Sifaniya, kuma irin waɗannan 'yan wasa ba a barin kwantaraginsu ta kai irin wannan lokaci ba tare da tsawaita ta ba.

    Ya koma Madrid ne yana da shekara 18 a 2018, ya ci kwafuna 14 ya zura kwallo 128 a wasa 375 da ya yi a ƙungiyar tasa.

    Rahotanni daga kasuwar saye da sayerwar 'yan wasan Turai na cewa darajar ɗan wasan za ta kai £200m.

    Madrid ta yi yunƙurin sabunta kwantaragin ɗan wasan ko kuma fara magana kan makomarsa ranar Litinin ɗin nan, sai dai har yanzu babu wata magana mai kwari kan hakan.

    Tuni Arsenal suka nuna muradinsu kan ɗan wasan, wanda wasu ƙungiyoyin Saudiyya suka riƙa nuna muradinsu kan shi.

    Kocin Gunners Mikel Arteta ya jima na son ɗaukar ɗan wasan da zai buga masa ɓangaren hagu wanda ya nuna kansa, kuma Vinicius ya nuna cancantarsa kan zaɓin.

    Tun bayan da ta rasa ɗan wasan da ta so ɗauka Morgan Rogers da Chelsea ta saya, Arsenal ta ƙara matsa ƙaimi kan ɗaukar ɗan wasan.

  4. Barkanmu da rana

    Masu bibiyar wannan shafi Muhammad Buhari Fagge ne ke fatan an tashi lashi, da fatan mun shiga sabon mako kalau.

    Za mu kawo muku rahotannin labaran wasanni da abubuwan da ke faruwa a kasuwar 'yan wasan nahiyar Turai.

    Me ake ciki tsakanin Real Madrid da Vinicius. Yaya batun Rashford kan komawar shi Manchester United. Me aka cimma tsakanin Madrid da Yan Diamonde. Barcelona ta hakura da Julian Alvarez kenan.

    Ku biyo mu domin samun cikakkun labaran.