Me ya sa muryar mace ta sha bamban da ta namiji?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Muryar ɗan Adam wata aba ce ta musamman ƙwarai. Tana isar da saƙo kan halin da mutun ke ciki, tana kuma nuna iko, kuma tana ɗauke da ainihin mutumtakarmu.

Kafin mu fahimci kalmomin da wani ke furtawa, galibi cikin daƙiƙa guda kawai za mu iya tantance ko mai magana namiji ne ko mace.

Waɗannan bambance-bambancen da ke tsakanin muryoyin maza da mata ba su faru haka kawai ba. Sakamako ne na sauye-sauyen halitta da tsarin jiki da kuma tasirin sinadaran ƴan aike na hallitu wato hormones da ke faruwa yayin da mutum ke girma.

Domin fahimtar dalilin da ya sa maza da mata ke da muryoyi mabambanta, dole ne mu fara kallon babbar cibiyar samar da sauti a jiki, wato maƙogwaro ko akwatin murya (larynx), da kuma jijiyoyin murya (vocal folds) da ke samar da sautin a cikinsa."

"Sauye-sauyen da ke faruwa lokacin balaga"

A lokacin ƙuruciya, muryoyin yara maza da mata suna da kamanceceniya sosai. Jijiyoyin muryarsu (vocal cords) kusan iri ɗaya ne ta fuskar girma, wanda ke sa zurfi da sautin muryoyinsu su kasance kusan iri ɗaya.

Mafi girman bambance-bambancen murya na bayyana ne a lokacin balaga, galibi sakamakon tasirin sinadaran hormones a jiki."

A lokacin balaga ne ake samun manyan sauye-sauyen da ke shafar murya, musamman sakamakon karuwar sinadaran hormones da ke sauya tsarin maƙogwaro da jijiyoyin murya."

A wajen maza, karuwar sinadarin testosterone a lokacin balaga na sa maƙogwaro (larynx) ya ƙaru sosai. Yayin da maƙogwaron ke girma, yana matsawa gaba, lamarin da ke haifar da fitowar da ake gani a wuya, wadda aka fi sani da kwadan makoshi (Adam's apple).

Yayin da sashen cikin maƙogwaron ke ci gaba da girma, jijiyoyin murya da ke cikinsa suna ƙara tsawo da kuma kauri.

Wadannan sauye-sauyen ne ke sa muryar maza ta ƙara kauri kuma ta ragu daga sautin yaro zuwa muryar baligi."

A bangaren mata kuwa, duk da cewa su ma suna fuskantar sauye-sauyen murya a lokacin balaga sakamakon tasirin sinadaran estrogen da progesterone, girman maƙogwaro (larynx) ba ya ƙaruwa sosai kamar yadda yake ga maza.

Maƙogwaron mata na ƙaruwa ne kaɗan kawai, kuma girma da siffarsa suna ci gaba da kasancewa kusan kamar yadda suke kafin balaga.

Saboda haka, jijiyoyin muryar mata ba sa tsawaita da kauracewa sosai, lamarin da ke sa muryarsu ta ci gaba da kasancewa da sauti mai ɗan kaifi idan aka kwatanta da ta maza.

"Domin fahimtar wannan, za mu iya ɗaukar misali da igiyar jita."

Za a iya fahimtar bambancin da ke tsakanin muryar namiji da ta mace cikin sauƙi idan aka yi amfani da misalin wata na'urar kiɗa kamar jita ko fiyano.

Igiyoyi masu kauri da tsawo kan fitar da sauti mai zurfi da nauyi, yayin da sirarun igiyoyi masu gajarta ke fitar da sauti mai kaifi.

Haka lamarin yake a wajen jijiyoyin murya na mutum. Jijiyoyin sauti masu tsawo da kauri kan samar da murya mai zurfi, yayin da waɗanda suka fi sirantaka ke samar da murya mai ɗan kaifi."

Jijiyoyin sauti a da ke cikin maƙogwaron namiji kan kai tsawon tsakanin milimita 17 zuwa 25.

Saboda suna da tsawo da kauri, suna karkarwa ne a ƙananan matakan mitar sauti , galibi tsakanin hertz 100 zuwa 120, wato sau 100 zuwa 120 na karkarwa a duk daƙiƙa guda.

Wannan ƙananan matakin karkarwa ne ke ba muryar maza zurfi da kaurin sautin da aka saba ji."

Hanyar da sauti ke bi

Maƙogwaro (larynx) na ɗaya daga cikin abubuwan da ke haifar da bambancin murya tsakanin maza da mata. Amma ba shi kaɗai ba ne.

Hanyar murya (vocal tract), wadda ta haɗa da maƙoshi (pharynx), baki da hanci, na aiki kamar wata na'urar ƙara sauti ta halitta.

Yayin da sautin da jijiyoyin murya ke samarwa ke ratsa waɗannan sassan, ana ƙara masa armashi tare da sauya kamanninsa, wanda ke ba kowane mutum irin muryarsa ta musamman.

Dalilai na al'ada da zamantakewa"

Duk da cewa gado daga iyaye shi ne babban abin da ke tasiri wajen samuwar murya, halaye da ɗabi'un mutane ma na taka rawa wajen yadda murya ke kasancewa.

Masana sun ce maza da mata kan sauya yadda suke magana ba tare da sun ankara ba domin dacewa da abin da al'umma ke kallon ya kamata ga namiji ko mace.

Misali, maza kan yi ƙoƙarin yin magana da murya mai kauri domin nuna ƙarfi da namijin hali, yayin da mata kan fi amfani da sautin murya mai laushi ko mai ɗan kaifi domin dacewa da abin da al'ada ke dangantawa da halayen mata.

Saboda haka, baya ga dalilan halitta, al'adu da yanayin zamantakewa ma na taimakawa wajen ƙarfafa bambance-bambancen da ake samu tsakanin muryoyin maza da mata."