A shirye muke mu mayar da martani mai tsauri ga duk wani hari - Iran
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa ƙasarsa a shirye take ta mayar da martani mai ƙarfi ga duk wani hari da za a kai mata, yayin da ya yi gargaɗi ga Amurka kan duk wata “kasada” da za ta iya ƙara tayar da rikici a yankin.
Araghchi ya bayyana hakan ne a tattaunawar waya da ya yi da ministan harkokin wajen Turkiyya da kuma babban kwamandan sojojin Pakistan, inda ya jaddada cewa Iran za ta kare kanta idan aka kai mata hari.
Haka kuma ya shaida wa ministan harkokin wajen Saudiyya cewa duk wani hari da Amurka ko Isra’ila za su kai, ko kuma wanda wasu ƙasashen yankin za su goyi baya, zai fuskanci martani mai tsauri daga Iran.
Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni ke nuna yiwuwar Amurka ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Iran, yayin da ofisoshin jakadancin Amurka a Bagadaza da Erbil suka gargadi ‘yan ƙasarsu da su kasance cikin shirin ficewa daga yankin Gabas ta Tsakiya idan buƙatar hakan ta taso.