Mun fasa kai hari kan wurare uku a Ukraine saboda ta nemi afuwa - Iran

Asalin hoton, IRNA
Iran ta ce ta shirya kai hari kan wurare uku a Ukraine bayan wani hari da aka kai wa jirgin kasuwancinta, amma daga baya ta dakatar da shirin bayan Ukraine ta nemi afuwa inda ta ce harin ba a yi shi da nufin tayar da rikici da Tehran ba.
Babban mai ba wa jagoran Iran shawara kan harkokin soji, Mohsen Rezaei, ya ce bayan tattaunawar da aka yi tsakanin ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu, Ukraine ta bayyana cewa harin wani ɓangare ne na yaƙinta da Rasha, ba da niyyarta ta kai wa ƙasar hari ba.
Rezaei ya kuma yi iƙirarin cewa hare-haren jiragen sama marasa matuƙi da makamai masu linzami da Iran ta kai kan sansanonin Amurka sun taimaka wajen daƙile duk wani shirin farmakin da Amurka za ta iya kai wa.
Game da mashigar Hormuz kuwa, ya ce Iran ba za ta amince da buɗe wata hanyar jiragen ruwa da ba ta ƙarƙashin ikonta ba, yana mai gargaɗin cewa za ta kai hari kan duk wani jirgin da ya bijirewa umarninta."

















