Ko za a iya daidaitawa tsakanin Wike da gwamnonin APC?

Wike
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Kalaman da Ministan Abuja Nyesom Wike ya yi ga gwamnonin APC kan samar wa Shugaba Tinubu ƙuri'in jihohinsu.

A lokacin da yake jawabi a yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, Wike ya gargaɗi gwamnonin APC kan sakaci a zaɓen da ke tafe.

"Ina so in faɗa muku cewa, idan ba ku kawo wa shugaban ƙasa ƙuri'un jihohinku ba, kuma ya yi nasara, kada ku ce mun yi nasara. Ba batun ni ne shugaba, ko sakatare ko mamba a wannan kwamiti ba. Muhimmin abin da ya kamata shi ne shugaban ƙasa ya yi nasara," in ji Wike.

"Na ma gaya wa Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa cewa, idan shugaban ƙasa bai yi nasara a Legas ba, kada ya ce mun yi nasara," in ji shi.

Kodayake Ministan Abujan, wanda ɗan jam'iyyar hamayya ta PDP ne na ci gaba da bayyana kansa a matsayin babban mai goyon bayan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, alaƙarsa da wasu gwamnonin jam'iyyar APC na ci gaba da fuskantar ƙalubale da saɓanin ra'ayi kan yadda ake gudanar da harkokin siyasa da gina ƙawance.

Tun a baya, Wike ya sha yin musayar yawu da wasu gwamnonin APC, musamman kan batun ƙawancen siyasar da ake wa laƙabi da "rainbow coalition", wanda ya haɗa mutane daga mabambantan jam'iyyu da muradun siyasa.

Sabbin kalaman na Wike sun sake tayar da wannan muhawara.

Wannan ya sa ake ci gaba da tambayar ko yaushe alaƙa za ta kyautata tsakanin Wike da gwamnonin na APC.

Me gargaɗin Wike ke nufi?

Dr Ibrahim Baba Shatambaya, Malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ya ce gargaɗin Wike ga gwamnonin APC, wani abu ne na sarƙaƙiya da ba a saba ganinsa a siyasar Najeriya.

''Bakon abu ne a fagen siyasar ƙasar nan a ce wani ɗan jam'iyyar hamayya ya yi kaka-gida a jam'iyya mai mulki ta yadda har ya ta kai yana yi wa wasu jiga-jigan jam'iyya mai mulki gargaɗi'', in malamin jami'ar.

Ya ƙara da cewa wannan sabon abu ne dai zai iya bijiro da wasu abubuwa da za su iya shafar shirye-shiryen jam'iyya mai mulki na yaƙin neman zaɓe.

''Wannan abu zai iya janyo wa jam'iyyar APC matsala a shirinta na zaɓen 2027'', kamar yadda ya yi ƙarin bayani.

Wane tasiri kalaman za su yi ga zaɓen 2027?

Wasu na ganin irin waɗannan kalamai na ƴansiyasa musamman masu fada a wurin Shugaba Tinubu, za su tilasta wa gwamnonin yin duk mai yiwuwa don ganin sun kawo wa shugaban ƙuri'in jihohinsu, ta kowane hali.

To amma Dr Shatambaya ya ce ba haka batun yake ba, domin kuwa a cewarsa wasu daga cikin gwamnonin an APC ba za su iya kawo wa shugaban ƙuri'un jihohin nasu ba, koda kuwa me za su yi.

''Idan ka duba dama daga cikin waɗannan gwamnoni suna da matsala da mutanen jihohinsu'', in ji shi.

Masanin siyasar ya ce wasu da yawan daga cikin gwamnonin suna jagorantar mutanen da suka gaji da mulkin APC a matakin tarayya.

''Don haka ba na ganin wannan gargaɗi na Wike zai yi wani tasiri ga zaɓen an 2027'', kamar yadda ya yi ƙarin bayani.

Ya ce wasu gwamnonin ma sun sha samun saɓani da Wike, don haka ba lallai ma su mayar da hankali wajen tallata shugaban ƙasar a jihohinsu ba.

Me ya janyo rashin jituwa tsakanin Wike da gwamnonin APC?

Rashin jituwa tsakanin Wike da wasu gwamnonin APC ya samo asali ne daga ƙoƙarin ƙawancen siyasa na Rainbow Coalition da Wike ya so jam'iyyarsa ta PDP ta ƙulla da APC, wani abu da gwamnonin APC suka bijirewa.

Dr Shatambaya ya ce mutane da dama na ganin Shugaba Tinubu ya fi martaba Wike fiye da wasu gwamnonin APC da ake ganin su ke riƙe da jama'a.

''Duk da kasancewarsa ministan Abuja, da ake yi wa kallon kamar matsayin gwamna, amma kasancewarsa ba ɗan yankin Abuja, ba shi da tasirin da zai iya kawo wa Tinubu ƙuri'un mutanen Abuja'', in ji shi.

Masanin siyasar ya ce gwamnoni na da tasiri sosai a siyasar Najeriya don haka bai kamata wani ya riƙa yi musu gargaɗi ba.

''Yanzu idan ka duba falsafar siyasar Najeriya, duk wata rawa da shugaban ƙasa zai yi, zai yi ne da bazar gwamnonin jam'iyyarsa saboda tasirinsu'', in ji shi.

Yaushe za a kyautata alaƙa tsakanin Wike da gwamnonin?

Dr Shatambaya ya ce da alama lokaci ya fara ƙurewa game da batun kyautatuwar alaƙa tsakanin Wike da gwamnonin na APC.

''Dama shugaban ƙasa ne kawai ake ganin zai iya sansanta ɓangarorin biyu, to shi kuma yanzu abubuwa sun yi masa yawa, har ma yana cewa ba kowace jiha zai je ba'', in ji shi.

Malamin jami'ar ya kuma ce muddin ba wannan ɓaraka aka ɗinke ba, to hakan zai ci gaba da yin tasiri a tafiyar siyasar ɓangarorin biyu.

Zuwa yanzu dai shugaba Tinubu bai taɓa tsoma baki ba game da rikicin gwamnonin nasa da kuma Minista Wike.