Me ya sa Iran ke damuwa kan ƙawancen Isra'ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa?

Asalin hoton, Reuters
Ziyarar baya-bayan nan da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kai Abu Dhabi ta kara tayar da shakku a Tehran kan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Jami'an Iran da kafafen yaɗa labaranta sun bayyana taron a matsayin sabuwar hujja da ke nuna yadda haɗin gwiwar tsaro tsakanin Isra'ila da UAE ke ƙara ƙarfi domin tunkarar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wannan fargaba, tare da yadda Iran ke kallon Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a matsayin barazana ga tsaronta, ta ƙaru tun bayan yaƙin baya-bayan nan wanda Iran ta riƙa kai hare-hare kan sansanoni da kadarorin Amurka a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, ciki har da cibiyoyin samar da makamashi na ƙasar.
Sai dai rashin jituwar ya fi batun yaƙi kaɗai. Dangantaka rdaular da Isra'ila, kusancinta da Iran da mashigin ruwa na Hormuz mai muhimmancin dabarun tsaro, tsohon rikicin mallakar wasu tsibirai uku a Tekun Fasha, da kuma ɗimbin alaƙar tattalin arziƙin da ke tsakaninta da Iran, duk sun haifar da wata dangantaka mai sarkakiya.
A wannan dangantaka, rashin yarda mai zurfi na karo da gaskiyar cewa ɓangarorin biyu na buƙatar junansu ta fuskar tattalin arziƙi.
Me ya sa ziyarar Netanyahu ta fusata Tehran?
Bayan ziyarar da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kai Abu Dhabi a ranar 27 ga Satumba, inda ya gana da Shugaban ƙasar Mohammed bin Zayed Al Nahyan, kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baghaei ya gargaɗi ƙasashen yankin cewa amfani da ƙasarsu da Isra'ila za ta yi wajen kai hari kan Iran na iya haifar da "mummunan sakamako".
Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron Iran, Manjo Janar Mohsen Rezaei, ya yi magana da kakkausan harshe, inda ya ce: "Kamar yadda karɓar baƙuncin sansanonin sojin Amurka bai kawo musu tsaro ba, haka ma karɓar baƙuncin 'mahaucin Gaza' ba zai haifar da kyakkyawan sakamako ba."
A wani saƙo da ya wallafa a dandalin X, Rezaei ya kuma yi kira ga ƙasashen yankin da su yi watsi da abin da ya kira "ikrarin da ba shi da tushe" kan "tsibirai uku na Tekun Fasha waɗanda mallakar Iran ne."
Ambaton tsibiran a cikin wannan gargaɗi ba kuskure ba ne. Kwanaki kaɗan kafin haka, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sake nanata iƙirarinta kan tsibiran Abu Musa, da Greater Tunb da Lesser Tunb waɗanda Iran ke iko da su, a wani zama na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Tehran ta sake jaddada cewa ikon da take da shi a kan waɗannan tsibirai "ba abin tattaunawa ba ne."
Wani babban kanun labaran jaridar Vatan-e Emrooz ya ce: "Lokacin da shehunan Haɗaɗɗiyar Daular Larabnawa suka zama 'yan tsana na Trump da Bibi," inda ya bayyana ƙasar makwabciyarta a Tekun Fasha a matsayin "kamfanin sahyoniyanci na Daular ta Larabawa."
Sauran kafafen yaɗa labarai ma sun bayyana Abu Dhabi a matsayin mai sauƙaƙa haɗin gwiwar tsaro da Isra'ila ke jagoranta a watamanufa ta tunkarar Iran, tare da hasashen cewa ganawar na iya kaiwa ga samar da wata babbar haɗakar tsaro a yankin.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Me ya sa Tehran ke mayar da hankali kan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗaya daga cikin dalilan kai-tsaye shi ne yanayin ƙasa. Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa tana a ɗaya gefen Tekun Fasha da Iran, kuma tana maƙwabtaka da Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar safarar makamashi ta duniya wadda ta mamaye rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran a halin yanzu.
Haka kuma, Abu Dhabi na da manyan cibiyoyin sojin ƙasashen Yamma, yayin da Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ta gina tashoshin jiragen ruwa da wasu hanyoyin fitar da kayayyaki da ke kauce wa Mashigar Hormuz, musamman a yankin Fujairah.
A wajen Tehran, wannan yanayi babban ƙalubale ne ga tsaronta.
A lokacin rikicin, jami'an Iran sun sha zargin ƙasashen yankin Gulf da bai wa Amurka da Isra'ila damar amfani da ƙasarsu, sararin samaniyarsu ko sansanoninsu na soja.
A cikin ɗaya daga cikin jawabansa, Baghaei ya ce an yi amfani da "wuraren da ke kudancin gabar Tekun Fasha" wajen tsarawa da shirya hare-hare kan Iran.
Bayan haka, Iran ta ƙaddamar da jerin hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa a wurare daban-daban na Haɗaɗdiyar Daular Larabawa, inda ba sansanonin Amurka kaɗai aka kai wa hari ba, har da cibiyoyin fararen hula da kayayyakin more rayuwa na makamashi.
Jami'an Iran sun bayyana hare-haren a matsayin martani ga wuraren soja da suka ce suna da hannu a hare-haren da aka kai wa Iran, yayin da hukumomin Haɗaɗdiyar Daular Larabawa da wasu gwamnatoci suka musanta ikirarin Tehran.
Saboda haka, wannan rikici ya ƙara ƙarfafa shakkun Iran cewa Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ba wai kawai tana karɓar rundunonin sojin Amurka ba ne, har ma tana ƙara shiga cikin cibiyar haɗin gwiwar tsaro ta Amurka da Isra'ila.
Mene ne rawar tsibiran Gulf da kuma Yarjejeniyar "Abraham Accords"?
Rikicin kan waɗannan tsibirai uku ya fara ne tun shekaru da dama kafin kafa dangantakar da ake da ita yanzu tsakanin Isra'ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
A wajen Iran, waɗannan tsibirai suna wakiltar wani batu na ikon ƙasa da ba za a yi sulhu a kansa ba, kuma suna daga cikin muhimman ginshiƙai na matsayinta na dabarun tsaro a yankin Tekun Fasha.
UAE kuwa ta dage cewa tsibiran mallakarta ne da Iran ta ƙwace ba bisa ƙa'ida ba, kuma ta sha yin kira da a gudanar da tattaunawa ko kuma a nemi shiga tsakani na ƙasa da ƙasa.
A wannan yanayi, ta samu cikakken goyon bayan siyasa daga manyan ƙasashen Larabawa, ciki har da Saudiyya.
Sai dai Tehran ta sha nanata cewa tsibiran "wani ɓangare ne da ba za a raba da yankin Iran ba."
Ali Akbar Velayati, mai ba Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin ƙasa da ƙasa, ya rubuta a wani saƙo da ya wallafa a dandalin X a ranar 3 ga Oktoba cewa: "Ƙasar da rayuwarta ta siyasa ba ta kai ko rabin ƙarni ba ce yanzu take yin ikirari daga dandalin Majalisar Ɗinkin Duniya game da tsibiran da takardun tarihi da taswirori tun ƙarnuka da suka gabata suka nuna a matsayin na Iran."
Ya kuma sake jaddada cewa tsibiran na Iran ne, tare da sukar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa saboda karɓar baƙuncin Netanyahu.
Jin tsoro da fargaba ya ƙaru matuƙa bayan yarjejeniyar Abraham Accords da aka rattaba hannu a kanta a shekarar 2020.
Lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar, ta haifar da kakkausar suka daga jagoran Iran na lokacin, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya zargi Abu Dhabi da cin amanar "duniyar Musulunci, duniyar Larabawa, ƙasashen yankin da kuma al'amarin Falasɗinawa."
Ya ce UAE ta taimaka wa Isra'ilawa wajen "samar da mafaka a yankin."
Shekaru shida bayan haka, wannan matsayi ya dawo ya zama tushen muhawarar da ake yi a yanzu kan abin da ake kira "Isra'ila ta biyu".
Duk da ƙalubalen da yarjejeniyar ta fuskanta, musamman bayan yaƙin Gaza na 2023, a Tehran ana kallon tsarin daidaita dangantaka tsakanin ƙasashen Larabawa da Isra'ila a matsayin wani abin koyi mai haɗari.
Muhawarar da ta dabaibaye yarjejeniyar ta samu sabon salo na siyasa yayin da ta haɗu da faɗaɗɗiyar gasa kan tsaron yankin Tekun Fasha.
Shafin Pars Today, wanda ke da alaƙa da gwamnatin Iran, ya bayyana cewa dangantakar ta wuce iyakar hulɗar diflomasiyya da tattalin arziƙi zuwa haɗin gwiwa a fannonin "tsaro, leƙen asiri da soja."
A wani rahoto da ya wallafa ranar 1 ga Oktoba, shafin ya yi zargin cewa an samu haɗin gwiwar leƙen asiri tsakanin Isra'ila da Abu Dhabi a lokacin rikicin shekarar 2026, zarge-zargen da wasu 'yan majalisa da masu sharhi ma suka bayyana a bainar jama'a.
Yadda da dogaro da tattalin arziƙi ke haifar da ƙalubalen dabarun tsaro.
A nan ne ainihin matsalar da ke cikin wannan dangantaka take. Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa abokan hamayya ne ta fuskar tsaro, amma a lokaci guda su ma manyan abokan hulɗar kasuwanci ne.
Tun shekaru da dama, Dubai tana zama muhimmiyar ƙofa ta kasuwanci ga kayayyakin da Iran ke shigowa da su daga ƙasashen waje, da waɗanda ake sake fitarwa, da kuma muhimman mu'amalolin kuɗi, musamman saboda tsauraran takunkuman ƙasa da ƙasa da aka kakaba mata.
Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya buga a ƙarshen watan Mayu ya nakalto wani bincike da ya kiyasta darajar kasuwancin da ba na hukuma ba tsakanin Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kusan dala biliyan 16.
Rahoton ya ƙara da cewa wani babban kaso na muhimman kayayyakin da ake shigarwa Iran suna bi ne ta hanyoyin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Wannan alaƙar tattalin arziƙi ta ci gaba da dorewa duk da shekaru masu yawa na takun-saƙa a siyasance.
Sai dai yaƙin ya haifar da gagarumar tangarda ga waɗannan alaƙoƙi. A watan Agusta, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sanar da dakatar da duk wata harkar kasuwanci, ta kuɗi da sauran mu'amaloli da Iran har sai abin da hali ya yi, yayin da rikice-rikice ke ƙara tsananta a yankin.
Wannan na nufin cewa ƙalubalen dabarun tsaro da Tehran ke fuskanta ya ƙara zama mai tsanani.
Ko da yake masu ra'ayin rikau a Iran suna bayyana Abu Dhabi a matsayin "cibiyar adawa" ko ma "Isra'ila ta biyu", musamman idan shugabannin Isra'ila suka kai ziyara a can, UAE na ci gaba da kasancewa ƙasa mai kusanci da ita ta fuskar ƙasa, mai muhimmanci ta fuskar tattalin arziƙi, kuma mai taka muhimmiyar rawa a tsarin kasuwancin yankin wanda Iran kanta ke matuƙar dogaro da shi.
Wannan yanayi na iya bayyana dalilin da ya sa kalaman jami'an Iran ke ɗauke da gargaɗi ga Abu Dhabi, amma a lokaci guda suna kiranta da ta nisanta kanta daga Amurka da Isra'ila.
Babbar dabarar Iran ba ta ta'allaka ne kawai kan ziyarar baya-bayan nan da Netanyahu ya kai ba, har ma tana da alaƙa da ko Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za ta zama wani sashe na dindindin a tsarin tsaron yankin da Isra'ila ke jagoranta. Tsarin da Tehran ta shafe shekaru tana ƙoƙarin tarwatsawa, da kuma yadda za ta iya tunkarar wannan sauyi ba tare da cutar da muradunta na tattalin arziƙi da diflomasiyya ba.



























