Makamin linzami mafi haɗari da nahiyar Afrika ta mallaka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A karon farko sojojin Aljeriya sun tabbatar da mallakar makami mai linzami na Iskander mai gudun wuce sa a, inda suka saki wani hoton bidiyo lokacin da suka harba makamin yayin atisayen soji.

An yi amannar sojin ƙasar sun mallaki makamin tun shekaru masu yawa a baya, amma rashin tabbacin da ba a samu ba ya sa sojin ƙasar ba su sanar da sayan sabbin makamai ba.

Ana yi wa makamin Iskander kallon wanda ya fi kowanne ƙarfi yanzu a duniya, kuma a yanzu ƙasashe biyu kacal ake da rahoton an kai shi Armenia da Algeria daga Rasha, yayin da Korea ta Arewa da Ta Kudu suka harba irin makamin, inda ake tsammanin suma sun samu nasu ne daga Rasha.

Makamin mai linzami yana cin kilomita 500 kuma yana kai wa ga inda aka hare shi ba tare da kuskure ba, yana tafiya cikin tsananin gudu, wanda hakan ya sa yake da wuyar a kakkaɓo shi.

An gabatar da makamin na Iskander ne bayan ɓarkewar rikicin da bai yi ƙarfi ba tsakanin sojoji Morocco da wasu ƙungiyoyin 'yan ta da ƙayar baya.

Makami mai linzami na Iskander

Makamin Iskandar da aka gabatar shi ne na bayan nan da aka samar mafi gudu da haɗari a Afrika da yankin Larabawa, kuma yana ɗaya daga cikin makamai masu haɗari da Rasha suka samar a 'yan shekarun nan.

Wasu ƙarin makamai da Aljeriya suka samu sun haɗa da makami mai linzami na S-400 mai cin dogon zango, akwai nau'in tankokin T-90 da suka samu cikin ɗaruruwan adadi, Pantsir-SM motar da ke kare hare-haren sama, akwai Class Kilo wanda na sojojin ruwa ne, akwai kuma na nau'in CX-1 da suka saya daga China, da dai dauransu.

Aljeriya ma na da yarjejeniyar sayan jirgin yaƙin Su-57 daga Rasha - a matsayinta na babbar abokiyar huldar kasuwancin Rasha mafi ƙarfi a Afrika - sai dai maganar sayan makaman da yawa haka ba a tabbatar da shi ba a hukumance.

Algeriya ta ƙara yunƙurin yawan makamanta ne tun bayan da ƙungiyar tsaro ta NATO ta kai hari kan makwabciyarta Libya a 2011.

Libya ta yi watsi da sabunta dakarun samaniyarta su zama na zamani haka kayayyakin kariyarta na sararin samaniya, wanda hakan ya janyo mata koma baya mai yawa lokacin da irin waɗannan raunukan suka zo.

Wannan ya sa Aljeriya da Masar sun samunta ma'ajiyar makamansu da za su zama cikin shirin ko ta kwana saboda barazanar duk wani hari daga ƙasashen Yamma.

Ina makamin Iskander ya samo asali?

Makamin 9K720 ƙirar Iskander Rasha ce ta samar da shi a ƙarshen zamanin Tarayyar Soviet.

Ya maye gurbin makamin Oka mai linzami kuma aka fara amfani da shi a hukumance tsakanin sojinRasha a 2006.

A hukumance kuma an fara samar da shi ne bayan wata dokar soji ta amince da shi ta ƙarƙashin majalisar ministoci ta Tarayyar Soviet a watan Disambar 1988.

An tsara shi ne domin tsarin ratsawa ko ina, zai iya kauce wa duk wata na'urar tsaron samaniya ya kuma samun abin harinsa ba tare da kuskure ba.