Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne hatsarin sabon makamin da Iran za ta saya daga China?
- Marubuci, Ridaa Sabeti
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters game da ƙoƙarin Tehran na sayen makamai masu linzami na zamani daga China ya sake jawo hankali kan wani ɓangare na tsarin kare sararin samaniyar Iran wanda ba a yawan ba shi muhimmanci idan aka kwatanta da manyan tsare-tsaren kariya irin su S-300.
Wannan makami mai sauƙin nauyi, mai sauƙin ɗauka daga wuri zuwa wuri, kuma mai araha, an ƙera shi ne domin kai hari kan jiragen sama da kuma jiragen marasa matuƙa.
Waɗannan ƙananan makamai da ake kira MANPADS, an ƙera su ne domin harbo jiragen yaƙi da jirage marasa matuƙi da ke shawagi a ƙasa.
Suna da sauƙin ɗauka, ba su da tsada sosai, kuma ana iya amfani da su cikin gaggawa.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ambato wasu majiyoyi da ba a bayyana ba, inda suka ce Iran ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da darajarta take tsakanin dala miliyan 60 zuwa 70, domin sayen makamai 300 zuwa 400 na kariyar sararin sama da mutum zai iya ɗauka.
Rahoton ya ce yarjejeniyar ta ƙunshi makamai masu linzami na ƙasar China, wato QW-12 da FN-16.
Kamfanin dillancin labaran ya ƙara da cewa ana iya kai rukunin farko na waɗannan makamai Iran cikin makonni kaɗan ta hanyar Pakistan.
Sai dai gwamnatin China ta musanta rahoton, tana mai cewa "ba shi da tushe balle makama", yayin da sojojin Pakistan suka ce zargin cewa ƙasarsu na da hannu wajen jigilar makaman "ƙarya ne kuma ba daidai ba ne."
Sai dai wannan ba shi ne karo na farko da aka ambaci ƙoƙarin Iran na mallakar irin waɗannan ƙananan makaman ba.
A watan Fabrairun 2026, jaridar Financial Times ta ruwaito cewa Iran ta ƙulla wata yarjejeniya ta sirri da darajarta ta kai Yuro miliyan 495 domin sayen makamai masu linzami na Verba guda 500 da kuma wasu makamai masu linzami 2,500 daga Rasha.
Jaridar ta ce, an sanya hannu kan yarjejeniyar ne a watan Disamban 2025, a lokacin da ake tsaka da yaƙe-yaƙe.
Ko da yake ba a tabbatar da rahoton a hukumance ba, amma kafafen yaɗa labarai a Iran sun yaɗa shi sosai.
Iran ta daɗe tana ƙoƙarin ganin ta mallaki irin waɗannan makamai.
Cibiyar bincike ta Small Arms Survey ta bayyana a wani rahoto da ta fitar a shekarar 2024, cewa Iran ta shigo da makaman QW-1 da China ta ƙera a shekarun 1990, sannan ta shigo da QW-18 a farkon shekarun 2000.
Daga baya Iran ta fara harhaɗa waɗannan makamai a cikin gida, inda ta sanya musu sunayen Mithaq-1da Mithaq-2.
Iran na bayyana nau'ikan makaman Mithaq a matsayin makaman da ta ƙera da kanta.
Sai dai masana na cewa har yanzu ba a fayyace ba ko wane ɓangare ne ake ƙerawa a cikin Iran, da kuma waɗanne sassa ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Mene ne makamin MANPADS, kuma ya ake amfani da su a fagen yaƙi?
"MANPADS" a taƙaice kalma ce daga turancin "Man-Portable Air Defense System", wato tsarin makaman kariyar sararin sama da soja zai iya ɗauka da kansa.
Yana ɗauke da makami mai linzami da yake cikin bututun harba makami, na'urar harbawa, batirin samar da wuta da kuma tsarin sanyaya makami.
Mafi yawan waɗannan makamai masu linzami suna da na'urorin gano zafin makami.
Hakan na nufin suna gano zafin da injin jirgin yaƙi ko wasu sassan sa ke fitarwa, su kuma bi diddigin inda aka kai harin, sannan su bibiyi jirgin idan an harba su su daƙile.
Amfani da waɗannan ƙananan makaman kariyar sararin sama ba ya buƙatar manyan na'urorin sanya ido ko wata mota ta musamman.
Ƙananan tawagar sojoji za su iya kafa su kusa da filayen jiragen sama, titin saukar jirage, wuraren tsaunuka ko muhimman wurare, sannan suna da saurin barin wurin da aka harba makamin.
Justin Bronk, babban mai bincike kan sararin samaniya a Cibiyar Nazarin Tsaro ta Birtaniya ta Royal United Services Institute (RUSI), ya shaida wa BBC Persian cewa sabbin makaman MANPADS da China ta ƙera na iya zama barazana sosai ga jirage masu saukar ungulu na Amurka da Isra'ila, kuma suna iya zama haɗari ga jiragen yaƙi da ke shawagi a ƙasa.
A cewarsa, waɗannan sabbin makaman sun fi na baya iya bambance ainihin jirgin sama da na'urorin zafi da ake amfani da su domin ruɗar da makami.
Sai dai ya ce galibi irin waɗannan makamai suna da hatsari ne ga jiragen da ke tashi ƙasa da kusan ƙafa 15,000 (kimanin mita 4,500).
Saboda ƙanƙantarsu da sauƙin ɗaukarsu da kuma saurin kafa su ya sa suka zama masu wahalar ganowa ko lalatawa.
Amma MANPADS suna kare sararin samaniya ne a tazara mara nisa kawai, kuma ba za su iya maye gurbin manyan makaman kariyar sararin sama masu matsakaici ko dogon zango ba.
Cibiyar Fitar da Makamai ta Ma'aikatar Tsaron Iran ta bayyana cewa matsakaicin tsayin da makamai masu linzami na Mithaq-1 da Mithaq-2 za su iya kaiwa shi ne mita 3,500.
Samfuran makaman "Mithaq" da aka haɗa da fasahar China
Ba a samu cikakken bayani kan adadin makamai masu linzami na kariyar sararin sama da Iran take da su ko kuma cikakken tsarin da suke da shi ba.
Sai dai majiyoyi daban-daban sun bayyana cewa akwai wasu tsofaffin nau'ikan makamai da aka ƙera daga ƙirar Tarayyar Soviet ta da, da kuma China.
Amma makamai nau'ikan "Mithaq" da kuma wasu daga cikin nau'ikan "Sahand" su ne suka fi shahara kuma aka fi samun bayanai a kansu a cikin makaman na Iran.
Makaman "Strela-2" da waɗanda suka biyo bayansu makamai ne da tsohuwar Tarayyar Soviet ta ƙera. Ƙungiyar tsaro ta NATO ta sanya musu sunan SA-7, yayin da ake kuma kiran su SAM-7.
Wani rahoto daga Cibiyar Bincike ta Small Arms Survey ya bayyana cewa makamin Sahand na Iran wani nau'i ne da aka samo asali daga wannan rukunin makamai.
Rahoton ya ce Iran ta shigo da makamai masu linzami na QW-1 daga China a shekarun 1990, sannan ta sake shigo da QW-18 a farkon shekarun 2000.
Daga baya Iran ta fara harhaɗa wasu nau'ikan waɗannan makamai a cikin gida, inda ta sanya musu sunayen Mithaq-1 da Mithaq-2.
Cibiyar Makamai ta Ma'aikatar Tsaron Iran ta bayyana Mithaq-1 a matsayin wani "makamin kariyar sararin sama na ƙarni na biyu mai aiki a gajeren zango", wanda ke da tsarin bin diddigin abu ba tare da aika sigina ba.
Wannan na nufin cewa makamin ba ya aika saƙonnin sanya ido domin gano abin da yake nema, sai dai yana gano kuma ya bi zafin da jirgin sama ko wani abin hawa ke fitarwa.
Kamar yadda aka wallafa a shafin intanet na cibiyar, an ƙera Mithaq-1 ne domin "jiragen sama masu saurin tafiya a gejeren zango", da kuma jirage masu saukar ungulu da sauran jiragen da ke tafiya a hankali.
An kuma bayyana cewa ana iya amfani da shi wajen kare dakarun ƙasa da muhimman wurare.
Cibiyar ta ƙara da cewa soja zai iya ɗaukar makamin Mithaq-1 a kafaɗa, ana iya saka shi a kan wasu "na'urorin hawa" ko dandamali na musamman.
Shi kuwa Mithaq-2, tsarin kariyar sararin samaniya ne na zamani, wanda ake harbawa daga kafaɗa.
A cewar bayanan Iran, wannan makamin na iya "bambance siginar gaske da siginar bogi", sannan yana iya amfani da kyamarar hangen nesa da dare domin gano abin da ake son kai wa hari.