Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko sabuwar haɗakar hamayya ta G-100 za ta iya kawar da Tinubu a 2027?
Wasu fitattun 'yan Najeriya 100 da suka haɗe ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna G-100 sun yi kira ga 'yan takarar shugaban kasar na jama'iyyun hamayya su dunkule wuri guda tare da tsayar da dan takara guda da zai kalubalanci shugaba Bola Tinubu na APC a zaben 2027 da ke tafe.
A cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai shafuka bakwai, ƙungiyar ta ce ta haka ne kaɗai za a iya kauce wa abin da ya faru a zaɓen 2023 da ya gabata, da ake ganin rashin haɗa kan 'yan hamayya ne ya sa APC samun nasara.
Malam Salihu Lukman, tsohon shugaban ƙungiyar gwamnonin jama'iyyar APC - wanda shi ne kakakin ƙungiyar - ya shaida wa BBC cewa, dalilinsu na yin wannan kira shi ne, halin da kasar take ciki da kuma abin da ya kira haɗarin da ke tattare da makomarta idan gwamnatin Tinubu ta ci gaba da kasancewa a mulki a wa'adi na biyu.
Ya ce: ''Na farko halin da kasar nan ta shiga hali ne na kaka-ni-ka-yi. Duk wanda ke kaunar kasar nan hankalinsa ba a kwance yake ba.
''Kuma mun yi imani duk masu neman takarar nan da manyan shugabanniu wannan abin ya dame su yanda ya damu kowa da kowa. Shi ya sa muka ce gara mu yi kira gare su a daure a dubu halin da kasar ke ciki.''
''Kuma a kawar da kwadayin shugabanci, ya zamana kowa ya dawo hankalinsa abin da za a yi a ceto kasar nan ne a gabansa,'' in ji shi.
Dangane da yadda wasu ke ganin kamar 'yan hamayyar sun makara da wannan shiri ganin cewa jam'iyyun sun mika wa hukumar zabe sunayen 'yan takararsu, ya ce har hanzu ba a makara ba.
Kakakin ya ce har yanzu akwai lokacin da za a iya yin wannan hadaka kasancewa sai a watan Janairu na 2027 za a yi zaben, saboda haka ya ce akwai sauran lokacin.
Ya yi bayani da cewa: ''Na farko lokaci bai kure ba, muna da watanni nawa daga nan zuwa lokacin zabe? Zaben nan ba za a yi shi ba sai a watan Janairu.
''Na biyu ba wai kawai za a zo tashi daya a ce wani ya janye ba. Za mu matsa musu ne su kulla kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu ta yadda za su samu kwanciyar hankali da junansu har su ga cewa eh ya kamata wani ya janye.''
Lukman ya yi gargadi kan abin da ya ce kasar za ta iya fadawa ciki idan har aka yi sake gwamnatin APC ta Tinubu suka ci gaba da mulki.
'' Don wannan gangancin da muke neman yi kowa ya yi tunani. A ce yau an yi zabe, mun yi hatsarin da ake gudu a ce APC da Shugaba Asiwaju za su ci gaba na wani shekara hudu, a yanda suka sa kasar nan ciki shekara uku, ya ishi kowa ishara a tashi tsaye a yi duk abin da ya kamata.''
Kakakin ya yi nuni da abin da ya ce kuskuren da suka yi a baya, inda suka daura irin wannan aniya amma suka sakarwa 'yan takarar abin a hannunsu inda suka fara kokarin hadewa wuri daya amma kuma abin ya lalace.
A kan haka ya ce ba za su sake irin wannan sakacin ba, yana mai cewa a yanzu za su yi tsayuwar daka a kai tare da 'yan takarar don a cimma wannan manufa.
Malam Lukman ya yi gargadi da abin da ya faru a 2023, da ya ce rabe-rabeb kan 'yan takarar na hamayya, inda suka ki dunkulewa su mara wa dayansu baya ya sa suka rasa gaba daya, APC ta ci zaɓe.
''Rabe-raben kawunansu da suka kasa hadin kai shi ya taimaka don lokacin ina APC, shi ya taimaka har muka ci zabe. In da sun hada kai su ukun nan suka fitar da dantakara daya da na yi imani watakila ba Asiwaju ne a kan mulki yau ba.
Jigon na 'yan hamayya ya kuma yi nuni da cewa a yanda ake tafiyar masu zabe da dama ba su da niyyar yin zabe domin suna ganin kusan ba amfanin zaben wajen samar da wani sauyi da suke buƙata.
Amma ya ce idan aka yi wannan haɗaka ta fitar da dan takara daya na hamayya muytane za su samu kwarin gwiwa na fita yin zaɓen domin suna ganin za su iya samun nasara ta wanda suka zaba.
Shin wannan yunƙurin zai iya tabbata?
Masana harkokin siyasa na ganin cewa cimma irin wannan haɗaka ba abu ne mai sauƙi ba, saboda yadda yawancin jagororin jam'iyyun adawa ke fifita muradunsu na kashin kai fiye da amfani ɗaya.
Masanin harkokin siyasa a Najeriya, Dakta Ibrahim Baba Shatambaya, ya ce duk da cewa haɗakar za ta iya zama wata hanya mai kyau ta ƙarfafa adawa, amma ba ya ganin za ta tabbata cikin sauƙi.
"Wannan haɗaka idan har za a samu yin ta, abu ne mai kyau. Za ta taimaka wajen samar da adawa mai ƙarfi da za ta riƙa sanya gwamnati mai ci cikin taka-tsantsan da kuma yi mata burki," in ji shi.
Sai dai ya ce babban ƙalubalen shi ne yadda shugabannin jam'iyyun adawa ke fifita muradunsu.
"Abin takaici shi ne yawancin ƴan adawa sun karkata ne wajen son ransu. Kowa na ganin shi ne ya kamata ya jagoranta, kuma wannan na hana a samu matsaya guda."
Dakta Shatambaya ya ƙara da cewa idan har shugabannin jam'iyyun adawa ba su fahimci cewa babu wata mafita face su haɗa ƙarfi da ƙarfe ba, akwai yiwuwar abin da ya faru a zaɓen 2023 ya sake maimaituwa a 2027.
Ya kuma yi nuni da cewa ko a wannan lokaci da hukumar zaɓe ta INEC ta fara wallafa sunayen ƴan takara, har yanzu ba lallai ne burin haɗakar ya tabbata ba, idan ba a warware sabanin da ke tsakaninsu ba.
A cewarsa, idan har jam'iyyun adawa suka iya kauda bambance-bambancensu su dunƙule waje guda, za su samu damar fito da sabbin dabarun wayar da kan masu kaɗa ƙuri'a da kuma gina wata adawa mai ƙarfi.
Amma ya yi hasashen cewa idan hakan bai faru ba, to tamkar sun share wa jam'iyya mai mulki hanya ne domin ta ci gaba da riƙe madafun iko bayan zaɓen shekarar 2027.