Fitattun Malamai 6 da suka riƙe muƙaman siyasa a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A baya-bayan nan wata sabuwar muhawara ta ɓarke a Najeriya game da dacewa ko rashin dacewar shigar malaman addini fagen siyasar ƙasar.

A duk lokacin da aka yi maganar riƙe muƙaman gwamnati a Najeriya, mutane da dama kan yi tunanin ƴan siyasa ko jami'an gwamnati, waɗanda a lokuta da dama akan naɗa su domin sakayyar wata hidima da suka yi a siyasance.

To sai dai fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na ƙasar Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya ce malamai na da rawar da za su taka musamman domin kawo gyara a fagen siyasar ƙasar.

Kodayake an fi sanin malaman Musulunci da wa'azi da koyar da addini, tarihin Najeriya ya nuna cewa wasu daga cikinsu sun taka muhimmiyar rawa wajen jagorancin gwamnati.

A cikin wannan muƙala mun zaƙula waus daga cikin fitattun malaman addinin musulunci da suka riƙe muƙamai a Najeriya.

Sheikh Ali Isa Pantami

Farfesa Ali Ibrahim Isa Pantami ya kasance kan gaba a misalan malaman addinin da suka shiga gwagwarmayar siyasa a Najeriya.

Malamin addinin wanda shi ne babban limamin masallacin Juma'a na Annur da ke Abuja, ya ri ka muƙamin Ministan sadarwa da tattalin arziki daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Kafin wannna lokaci tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa shi shugaban hukumar fasaha da NITDA.

A yanzu haka malamin na takarar gwamnan a jihar Gombe da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Sheikh Jabir Sani Maihula

Dokta Jabir Sani Maihula fitaccen malamain add in muslunci ne da aka fi jin amon sunansu a wuraren da'awa.

Ya kasance malamin jami'a inda ya zama shugaban sashen koyar da ilimin addinin Musulunci a jami'ar jihar Sokoto.

A shekarar 2023 ne gwamnan jihar, Ahmad Aloiyu ya naɗa shi muƙamin kwamishinan harkokin addinin na jihar.

Naɗa shi matsayimn kwamishinan bai hana shi gudanawar da harkokinsa na koyarwa ba, inda har yanzu yake gudanar da majalisinsa na karatu.

Yanzu haka kuma malamin shi ne babban limamin masallacin Juma'a na Sultan Sa'ad Abubukar da ke birnin Sokoto.

Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan

Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan na ɗaya daga cikin fitattun malaman Addinin Muslunci da suka taɓa riƙe manyan muƙaman gwamnati a Najeriya.

A watan Oktoban 2024 ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa shi matsayin shugaban hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON.

A watan Fabrairun 2026 ya sauka daga muƙamin nasa, bayan ɓarkewar wata dambarwa a hukumar NAHCON.

Sheikh Pakistan ya kasance tsohon shugaban hukumar jindaɗin alhazan jihar Kano, kafin a naɗa shi babban shugaban hukumar na ƙasa.

Farfesa Ishaq Olanrewaju Oloyede

Tsohon shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun na Najeriya na daga cikin fitattun malaman musulunci da suka riƙe muƙaman gwamnati a ƙasar.

Fitaccen malamin addinin musluncin ɗan asalin jihar Ogun da ke kudu maso yammcin Najeriya ya kasance tsohon shugaban jami'ar Ilorin.

Farfesa Oloyede ya taɓa riƙe mu kamin shugaban kungiyar shugabannin jami'oin Najeriuya tsakanin 2011 zuwa 2012.

A shekarar 2016 ne tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya na da sh shugaban hukumar JAMB, mai shirya jarrabawar shiga manyan makarantun ƙasar, mu kamin da ya rike har zuwa 31 ga watan Yulin 2026.

Sheikh Jamilu Albani

Sheikh Jamilu Abubakar Albani da aka fi sani da Sheikh Jamilu Albani Samaru, na daga cikin fitattun malamn addini da suka shahara a fagen siyasa a arewacin Najeriya.

Ya fara shiga harkokin siyasa bayan da aka naɗa shi muƙamin shugaban harkokin addinai ta jihar Kanduna a 2019.

A shekarar 2023 ya tsaya takarar ɗan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Garin Zariya, inda kuma ya yi nasara.

Sai dai daga baya ya ajiye mu kamin tare da tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukumarsa ta Sabon Gari, inda kuma ya yi nasara.

Sheikh Abdullahi Abba Zariya

Fitaccen malamin Addinin Musulunci ne, mahaddacin Alƙur'ani wanda ya yi fice a fagen tafsiri.

Alaramma Abdullahi Abba Zariya ya kasance mai jan baƙi ga Sheikh Pantami a lokacin Tasfirin Ramadan a Masallacin Juma'a na Annur da ke Abuja.

Yanzu haka Alaramman shi ne mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zariya da ke jihar Kaduna.

Malamin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun makarantar Al'qur'ani da ake yawan sauraron ƙira'arsu.

Baya ga waɗannan akwai kuma wasu fitattun malaman addinin Musuluncin da suka riƙe muƙaman gwamnati a kasar da suka haɗa da:

  • Sheikh Ibrahim Khalil
  • Sheikh Nura Adam Gwale
  • Sheikh Halliru Maraya

Ko ya dace malaman addini su riƙa shiga siyasa?

Wasu na ganin cewa ya kamata malamai su shiga siyasa domin taimakawa wajen magance matsalolin da ake samu a fagen siyasar.

Daya daga cikin masu wannan ra'ayi shi ne fitaccen malamin nan na arewacin Najeriya, Sheikh Ahmad Mahmad Gumi, wanda a cewarsa gara malamin da ya shiga siyasa da nufin gyarata maimako tsayawa kan buzu ana kiran gyaran.

A tattaunawarsa da BBC, Sheikh Gumi ya ce tsarin shugabanci, addinin musulunci ne ya zo da shi.

Ya ce yana da kyau malaman addinin su shiga siyasa, saboda ba su da wani abun aibi da yake boye wa mutane.

Shehin malamin ya ce shigar malamai siyasana daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen tsaftace siyasa Najeriya.

Ya bayar da misali da kasashen Saudiyya da Iran, inda ya ce a Saudiyya sarakunan ƙasar na aiki hannu da hannu da makamai, a ƙasar Iran kuma ya ce malaman ne ma suke tafiyar da siyasar ƙasar.

A nasa ɓangare Dakta Ibrahim Baba Shatambaya malami a sashen kimiyyar nazarin siyasa ta Jami'ar Danfodiyo da ke Sokoto, kuma mai nazari kan harkokin siyasar Najeriya ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa dama ciki har da malamai domin su shiga harkokin siyasa.

''Kamar yadda kowane dankasa ke da haƙƙi haka su ma malamai, musamman idan malaman za su aiwatar abin da suke yawan kiraye-kiraye a kan mumbarinsu'', in ji shi.

Ya kara da cewa malamai mutane ne da ake yi wa kallon tsaron Allah, masu son vci gaba, masu son yin adalci, to idan suka shiga siyasa suka aiwatar da duk wannan, to ba shakka siyasar ƙadsar za ta inganta.

''Matsalar da za a samu shi ne idan sun shiga siyasar sun cire rigar malunta sun saka riga gurɓatatun ƴansiyasa, to nan ne shigar malamai ke da matsala'', in ji malamin jami'ar.