'Yadda haihuwar tagwaye ta janyo min matsala da mijina'

Catherine Mugure ta haɗu da mutumin da ya zama abokin zamanta a Jami'a.
    • Marubuci, Asha Juma
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Nairobi
    • Aiko rahoto daga, Nairobi
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Catherine Mugure ta haɗu da mutumin da ya zama abokin zamanta a Jami'a.

Daga bisani ta ɗauki ciki, lamarin da ya tilasta mata dakatar da karatunta na wani lokaci.

Saboda tsauraran matakan tarbiyya da iyayenta suka ɗora mata, irin wanda iyaye da yawa ke yi domin kyautata makomar ƴaƴansu mata, Catherine ta ce ba ta da wani zaɓi face ta koma ta zauna tare da abokin nata.

Daga nan ne su biyun suka yanke shawarar fara rayuwa tare.

A cewar Catherine, mijin nata shi ne babban amininta, mutum wanda take raba komai da shi.

Ta ce ta yi imanin cewa shi ne mutumin da take son ta shafe rayuwarta tare da shi.

Sai dai akwai wani abu guda da, a cewarta, abokin zaman nata ya tsana musamman.

"Ya kan ce ba zai taɓa son yin soyayya ko zama tare da budurwa mara taɓa namiji ba. A lokacin ni haka nake, amma saboda kalamansa ban taɓa gaya masa gaskiyar hakan ba," in ji Catherine.

Ta ce har yau ba ta fahimci dalilin da ya sa abokin zaman nata yake ƙin ra'ayin zama tare da budurwa mara taɓa namiji ba, amma ba ta so ta yi wani abu da zai iya kawo cikas ga dangantakarsu.

A bikin zagayowar ranar haihuwarta, Catherine ta amince da ba shi kanta.

"Hakan ya sa na rasa alfaharin da nake yi cewa ba namijin da ya taɓa sanina, da hakan kuma na samu juna biyu,''

"Duk da cewa mun yi rigima da shi a lokacin da ya fahimci cewa ni budurwa ce, ban taɓa sanin namiji ba, wannan shekarar ta kasance abu mai muni a gareni. Hakan ya sa dole muka yanke shawarar zama tare domin samun ɗan da ke cikina'', in ji ta.

Lokacin da naƙuda ta yi, Catherine ta haihu ba tare da wata matsala ba.

Sai dai mijinta ba ya tare da ita a lokacin, kuma daga nan ya fara nuna wasu halaye na daban da suka ba ta mamaki.

"Ya kan yi shaye-shaye sannan ya dawo gida cikin talatainin dare. A duk lokacin da muka yi magana a kan batun yakan ce na cutar da shi,'' kamar yadda ta yi bayani.

Rikicin da ke tsakaninsu ya ƙara tsananta, har ta kai ga Catherine ta yanke shawarar tserewa daga gida karo na farko. A lokacin, jaririnta na da kimanin watanni shida da haihuwa

Ta haihu ne a lokacin da take da shekara 21 a duniya.

A lokacin da suke samun saɓani, mijinta kan sha gaya mata cewa idan har ta yanke shawarar barin gidansa, kada ta yi ƙoƙarin tafiya da ɗan nasu, yana yi mata barazanar kisa idan ta aikata haka.

Rayuwa ta ci gaba kamar yadda aka saba, ba tare da mijinta ya san cewa Catherine na shirya yadda za ta bar gidan a asirce ba.

Daga bisani ta nemi izinin zuwa ziyartar iyayenta, kuma mijin ya amince. Sai dai kafin ta tafi, ya tambaye ta ko za ta bar masa ɗansu.

"Idan kana so in bar maka yaron, zan iya bar masa. Amma ina son in je in tattauna da mahaifina domin ya taimaka mini na koma jami'a in ci gaba da karatuna."

Da haka ne ta tattara ta koam gidan iyayenta tare da labarta musu halin ta tsinci kanta a gidan mijin nata.

'Haɗuwarmu a karo na biyu'

Catherine ta rufe wayarta na an wani lokaci kafin ta sake buɗe ta bayan wasu watanni.

Inda ta fara aiki a wani kantin sayar da wayoyin hannu a matsayin jami'ar talla, ashe sanadiyyar sake haɗuwarta da tsohon mijin nata kenan.

"Ina ta kiran kwastomomi domin tallata musu wayoyi Kwatsam sai na hango mijina, abin ya ba ni mamaki matuƙa. Ban yi tsammanin zan gan shi ba, kuma ina ganin shi ma bai yi tsammanin zai gan ni ba."

A ranar, ya nemi ta sayar masa da waya. Daga nan ya fara zuwa wurinta kusan kullum. Har suka saba zama tare suna shan kofi.

A haka kuma har Catherine ta sake ɗaukar wani juna biyun.

"Mun sake komawa zama tare cikin sauƙi domin yana kula da dukkan buƙatunmu."

Daga nan ma'auratan suka yanke shawarar dawo da ɗansu na fari, wanda ke zaune tare da kakarsa, domin su ci gaba da rayuwar aurensu.

Sai dai duk da wannan dama ta biyu da suka samu ta sake gina iyalinsu, matsalolin da ke tsakaninsu ba su kau ba.

Bayan wani lokaci, saɓanin ya sake ɓarkewa a tsakaninsu. Kamar yadda ya faru a baya, daga ƙarshe ma'auratan suka sake rabuwa karo na biyu.

'Yadda na sake ɗaukar juna biyu karo na uku'

.

Kodayake dangantakarsu ta kasance cike da ƙalubale da matsaloli, tsohon mijin Catherine bai taɓa daina kula da 'ya'yansa ba.

Wannan ya ba shi damar ci gaba da zuwa ziyartar iyalinsa a duk lokacin da ya ga dama.

Haka ne ya sa Catherine ta sake samun ciki na uku daga wannan mutumin.

"Bayar da duk abin da na sha tare da ɗana na fari da na biyu, na riga na yanke shawarar cewa ba zan sake haihuwa da shi ba.

Bayan na yi gwaji, sai aka tabbatar cewa na sake samun ciki, karo na uku."

A lokacin, Catherine tuni tana fama da matsalolin lafiya. Tana da ciwon sukari da hawan jini. Duk da haka, ta yanke shawarar zubar da cikin.

Amma da ta je asibiti, likitoci suka ba ta wani labari da ba ta taɓa tsammani ba.

"Ba za a iya zubar da wannan cikin ba. Idan kika yi ƙoƙarin hakan, rayuwarki na cikin haɗari. Kina ɗauke da tagwaye kuma kina fama da cutar fibrosis," in ji likitan da ya bayyana mata.

Daga wannan lokaci ne komai ya sauya.

Duk da cewa likitoci sun shawarce ta da ta ci gaba da dakon cikin har zuwa lokacin haihuwa tare da kula da kanta sosai, tsohon mijinta ya nuna matuƙar rashin jin daɗi da ya ji cewa tana ɗauke da tagwaye.

"A danginmu babu tarihi na haihuwar tagwaye. Haka nan a danginku ma babu. Don haka waɗannan yaran ba nawa ba ne."

Wannan martani ne ya fara jefa Catherine cikin wani sabon yanayi na wahala.

Yayin da cikinta ya kusa wata shida, ta fara alamun naƙuda, alamar cewa za ta haifi jariran tun kafin cikar lokaci.

Aka garzaya da ita asibiti, inda aka yi mata tiyatar haihuwa tare da ciro jariran, kamar dai yadda aka yi mata.

An haifi tagwayen, amma ba da daɗewa ba wani abin baƙin ciki ya faru: washegarin haihuwar, ɗaya daga cikin jariran ya rasu.

"An ce in je sashen kula da jarirai domin in ga 'ya'yana. Da na isa, sai na ga ɗaya daga cikinsu kwance a kan teburi. Ya riga ya rasu. Ɗayan kuwa yana cikin koshin lafiya."

Daga nan mijinta ya watsar da su a asibiti.

"Mijina ya guje ni saboda na haifi tagwaye, kuma tun daga wannan lokacin bai sake dawowa ba har zuwa yau," in ji Catherine.

'Yadda na warke daga rabuwa da mijina'

.

Bayan sallamartata daga asibiti, Catherine ta fuskanci ɗaya daga cikin lokuta mafi tsanani a rayuwarta.

"Na kusa rasa hankalina. Har ma na kai ga tunanin kashe yarana uku. Amma Allah Ya ba ni ƙarfin gwiwar ci gaba da rayuwa."

Game da ɗaya daga cikin tagwayen da ya rayu, ta ce likitoci sun shaida mata cewa watakila ba zai daɗe da rayuwa ba saboda yana fama da matsalar zuciya.

Sai dai duk da hasashen da aka yi, yaron yanzu yana da shekara uku a duniya.

Catherine ta kuma aike da saƙo ga sauran iyaye mata da ke fuskantar irin wannan jarrabawa.

"Kada ku taɓa yanke ƙauna, ƙarfinku yana cikin yadda kuke kallon rayuwa da kuma irin tunanin da kuke yi."

A yau, Catherine ta samu damar ci gaba da rayuwarta. Duk da ƙalubale da wahalhalun da ta sha a baya, tana ci gaba da tafiyar da rayuwarta tare da mayar da hankali wajen kula da tarbiyyar 'ya'yanta.