Fenerbahce ta shirya ɗaukar Rashford, PSG na neman Torres

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Fenerbahce ta shirya gabatar da tayi mai gwaɓi domin ɗaukar ɗanwasan gaban Manchester United da Ingila mai shekara 28, Marcus Rashford. (Sun)

Ɗanwasan gefen Ivory Coast mai shekara 19 Yan Diomande, ba zai halarci sansanin atisayin RB Leipzig ba, yayin da ƙungiyar ta haƙiƙance kan farashin £111m da ta sanya wa Real Madrid kan ɗanwasan (Athletic - subcription required)

Arsenal ta fara tattaunawa da Newcastle a kan cinikin ɗanwasan tsakiyar Brazil mai shekara 28, Bruno Guimaraes, wanda ta ke fatan saye a kan £70m ko £80m. (Telegraph - subscription required)

Paris St-Germain ta ƙara ƙaimi a zawarcin ɗanwasan gaban Barcelona da Sifaniya mai shekara 26 Ferran Torres. (Fichajes - in Spanish)

Liverpool ba ta da aniyar sayar da Cody Gakpo mai shekara 27, duk da zawarcin da Tottenham ke yi wa ɗanwasan faban na Netherlands. (Mail - subscription required)

Sunderland ba za ta sayar da ɗanwasan gaban Haiti mai shekara 25, Wilson Isidor ba, duk da matsin lambar da ta ke fuskanta daga West Ham a kan shi. (Sky Sports)

Mai tsaron ragar Barcelona da Jamus mai shekara 34, Marc-Andre ter Stegen na shirin komawa Ajax a matsayin aro na tsawon shekara ɗaya. (Sport - in Spanish)

Aston Villa za ta gabatar da tayin £30m a kan ɗanwasan tsakiyar Barcelona da Sifaniya mai shekara 19, Marc Bernal (Sun)

Ɗanwasan gaban Real Madrid da Brazil mai shekara 20, Endrick ya ɗauki hankalin Roma, kuma ƙungiyar Italiyan na fatan sayen shi kafin a rufe kasuwa cikinkin ƴanwasa. (Fichajes - in Spanish)

Manchester United ta shaidawa ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 22, Toby Collyer cewa zai iya barin ƙungiyar a bana, yayin da wasu ƙungiyoyin ƙaramar gasar Ingila ke bibiyar shi.(Sun)