Iran ta ce ba ta wata tattaunawa da Amurka a halin yanzu
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce a halin yanzu babu wata tattaunawa da ke gudana tsakanin Iran da Amurka, duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa za a fara sabbin tattaunawa a yau Litinin.
Baghaei ya bayyana cewa a yanzu Tehran ta fi mayar da hankali kan tattaunawar da take yi da Oman game da mashigar Hormuz, wadda ta shafe kwanaki takwas tana gudana.
Ya ce duk wata fahimta da ake samu da Oman ba tana nufin an buɗe mashigin Hormuz ba har sai an tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.
Baghaei ya kuma jaddada cewa rufe mashigin Hormuz ya biyo bayan hare-haren Amurka da Isra'ila ne, ba saboda saɓani tsakanin Iran da Oman ba.
A cewarsa, Iran da Oman na tattaunawa kan wata sabuwar hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa.