Da gaske ne Amurka ta kawo karshen ‘kisan’ Kiristoci a Najeriya?

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya CAN

Asalin hoton, CAN

Bayanan hoto, Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya CAN
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihohi 19 na Arewacin Najeriya da Babban Birnin Kasar Abuja, da kuma hadin guiwar limaman kiristoci nakarkashin inuwar Ƙungiyar Ecumenical Synods of Bishops, Archbishops, Apostles and Senior Clergy, sun yi watsi da ikirarin Shugaban Amurka, Donald Trump, cewa sojojin Amurka sun kawo ƙarshen kashe-kashen Kiristoci a Najeriya.

Limaman sun bayyana ikirarin Trump a matsayin yaudara, da ƙarya da suka saba da abin da ke faruwa a ƙasa, suna gargadin cewa hakan na iya rage muhimmancin matsalar rashin tsaro da ƙasar ke fama da ita.

Yayin wani taro da aka gudanar a Washington ranar Juma'a, Mista Trump ya ce tsoma baki da Amurka ta yi a Najeriya ya taka muhimmiyar rawa wajen dakatar da hare-haren da ake zargin ana kai wa al'ummomin Kirista, musamman a yankunan da ke fama da ta'addanci da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi.

"Kamar yadda kuka sani, kwanan nan mun kai hari a Najeriya kuma mun dakatar da kisan kiyashin Kirista," in ji shugaban na Amurka.

Ya ce kafin hare haren na Amurka, lamarin ya yi muni matuƙa, yana mai cewa dubban mutane marasa laifi, ciki har da mata da yara da tsofaffi, sun rasa rayukansu a hare-hare masu muni.

"Najeriya na da yawan Kiristoci. Ana yi musu kisan gilla, dubban mutane ake kashewa, ciki har da yara, da mata da tsofaffi" in ji shi.

Trump ya ce matakin sojan da aka ɗauka ya raunana waɗanda ke da alhakin kai hare-haren sosai.

"Sun san cewa idan suka ci gaba, harin da za mu kai musu zai fi muni, suna tsoron hakan. Mun yi musu mummunan luguden wuta. Mun kashe shugabansu, mun kashe mataimakinsa na farko da na biyu," in ji shugaban Amurka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To sai dai da yake martani kan wannan ikirari, shugaban CAN na jihohi 19 na Arewa da Babban Birnin Tarayya, Joseph Hayab, ya ce maganar Trump ba ta dace ba, yana mai jaddada cewa har yanzu ana kashewa da kuma sace 'yan Najeriya, ba Kiristoci kaɗai ba, a jihohi da dama.

Hayab ya ce waɗanda suka fi dacewa su tantance ko an samu wani ci gaba a harkar tsaro su ne waɗanda matsalar rashin tsaro ta shafa da kuma Kiristocin Najeriya, yana mai cewa har yanzu ana ci gaba da kashe mutane da yin garkuwa da su a faɗin ƙasar.

Ya bayyana kalaman Trump a matsayin ikirarin siyasa, wanda ya samo asali daga bayanan da ba na gaskiya ba, da ya samu daga masu ba shi shawara waɗanda ba su fahimci yanayin tsaron Najeriya ba.

"Mutanen da ya kamata su faɗi ko Trump ya yi nasara su ne Kiristocin Najeriya ko na Arewacin Najeriya, ba Trump da kansa ba. Amma watakila yana samun bayanai daga inda bai dace ba''

"Ya kamata Trump ya bar waɗanda abin ya shafa su faɗi hakan, ba shi ba. Su ne suka fi dacewa su ce ko abin da ya yi ya samar da wani sakamako," in ji shi.

Duk da amincewa cewa kwanan nan Amurka ta kai wasu hare-haren soji kan 'yan ta'adda, shugaban CAN ya ce hakan bai kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa fararen hula ba.

A cewarsa "Dabarar da Amurka ƙarƙashin Trump ke amfani da ita ba ta isa ba, domin bayan da sojojin Amurka suka kai hari a Sokoto a watan Disamban bara, sai suka dakata na wani lokaci mai tsawo. Kwanan nan sun sake dawowa suka kashe wasu kwamandojin ISIS, amma har yanzu ana kashe mutane a nan kullum," in ji shi.

Hayab ya buƙaci gwamnatin Amurka ta mayar da hankali kan bayar da taimako na zahiri maimakon yin abin da ya kira ikirarin siyasa.

"Ba mu san waɗanda ke ba shi shawara ko labaran da ba gaskiya ba. Idan suna son kawo ƙarshen kashe farar hula a Najeriya da gaske, su daina farfaganda ko yaɗa labarai marasa tushe, su mayar da hankali kan gaskiyar abin da ke faruwa, domin ban yi tsammanin waɗanda abin ya shafa za su ji daɗin irin wannan ikirari ba.

"Ina ganin ya kamata a sanar da shi yadda abubuwa suke gudana, maimakon ya riƙa ikirarin abin da ba haka yake ba. Domin idan mutum har yanzu yana kwance a asibiti kana cewa ya warke, to ko dai an ba ka bayanan da ba daidai ba ne ko kuma ba ka fahimci ma'anar rashin lafiya ba.

"Muna son taimako, amma ba taimakon farfaganda ba. Muna son taimako na gaskiya, ba yaɗa labaran ƙarya ko bayanan da ba su dace ba. Waɗannan mutanen da har yanzu suke hannun 'yan bindiga a Oyo, Kwara da Kogi, me aka yi game da su? Har yanzu akwai mutane a Kwara, Katsina, Borno da sauran jihohi. Trump da mutanensa za su iya ba da labari mafi inganci.

"Muna son taimakon da zai kawo ƙarshen kashe-kashen da ake fama da shi, ba Trump ya riƙa yin ikirari domin amfanin siyasasarsa ba. Waɗanda ke ba shi bayanai ba sa ba shi sahihan bayanai," in ji shi.