Makomar Martinez a Man United ba tabbas, Getafe na son Sancho

Lisandro Martinez
Bayanan hoto, Lisandro Martinez
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Babu tabbataci kan makomar ɗan wasan Manchster United Lisandro Martinez, biyo bayan suka da ya ke fuskanta daga shugabancin ƙungiyar, da yasa yanzu ake shakku kan tsawaita kwantaranginsa da ke shirin ƙarewa a kakar wasannni mai zuwa. (Sky Sports)

Manchester United da Arsenal na sa ido kan ɗan wasan Newcastle United Bazoumana Toure, duk da cewar dan wasan bai jima da komawa Newcastle ɗin a wannan kaka. (CaughtOffside)

Getafe na son dan wasan Ingila Jadon Sancho inda kwantaranginsa ta ƙare, sannan suna neman yadda za su hadu da ɗan wasan don tattauna albashi da sauran buƙataun da zai gabatar musu. (DAZN, via Mundo Deportivo)

Mai hororar da ƴan wasan Real Madrid Jose Mourinho, ya ce ba sai ɗan wasan Brazil Endrick ya bar ƙungiyar ba a mastyin dan wasan aro ba a watan Janairu ba, kuma yana da yaƙinin cewar zai zama babbar nasara ga ƙunhiyar da ke taka leda a gasar ta La Liga. (TNT Sports Brazil, via the Athletic)

Tsohon mai horara da Wolves da Nottingham Forest Vitor Pereira na shirin komawa cikin jagororin gasar Firimiya, duk da alaƙanta shi da ƙungiyar Fulham.(Talksport)

Mai horar da ƴan wasan Brighton Fabian Hurzeler na cikin masu harar da ƙungiyoyin da ke buga gasar Firimiya da ya fita daban, wanda idan har Manchester United ta ɗauke shi zai iya maye gurbin Michael Carrick. (The Sun)

Haka kuma tsohon kociyan Chelsea Antonio Conte da Julian Nagelsmann, na ci gaba da jan hankula daga jagororin Manchester United's bosses. (Talksport)

Liverpool ta ƙara ruɓanya aniyar ta na ganin ta ɗauko Gilberto Mora, inda take fatan kamala cinikinsa da Club Tijuana nan da watan Janairu kan dan wasan. (Teamtalk)

Leeds na gabarar na fargabara rasa ɗan wasan Bosnia and Herzegovina Tarik Muharemovic, a kaka mai zuwa , inda Bayern Munich ke cikin jierin ƙungiyoyin da ke son ɗan wasan. (Football Insider)

Barcelona na sa ido kan Nicolo Tresoldi, da ya ci wa Club Brugge ƙwallaye uku a wasan su da Inter Milan on Tuesday. (Fichajes)