Porro na son komawa Barcelona, Chelsea ta dage kan Frenkie de Jong

Pedro Porro
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Zaman da ɗan wasan bayan Spain, Pedro Porro, ke yi a Tottenham na gab da zuwa ƙarshe, yayin da Barcelona ke zawarcin ɗan wasan mai shekara 27. (Sport)

Chelsea na shirin bai wa ɗan wasan tsakiya na Barcelona ɗan ƙasar Netherlands, Frenkie de Jong, kwantiragi mai tsoka idan har ta yi nasarar ɗaukar ɗan wasan mai shekara 29 a watan Janairu. (Football Insider)

Manchester United da Tottenham da Everton na sa ido kan ɗan wasan gaban Dinamo Zagreb da Croatia, Dion Beljo, mai shekara 24. (Teamtalk)

Liverpool na son ɗaukar ɗan wasan baya na gefen dama, kuma ta na zawarcin ƴan wasa irin su ɗan ƙasar Faransa Pierre Kalulu, mai shekara 26 daga Juventus, da kuma ɗan ƙasar Brazil Wesley Franca, mai shekara 23 da ke AS Roma (Tuttomercatoweb)

Tsohon kociyan Brentford da Tottenham, Thomas Frank, zai kasance ɗaya daga cikin manyan waɗanda ake ganin za su iya karɓar ragamar horar da Fulham idan ƙungiyar ta yanke shawarar korar Alvaro Arbeloa. (Talksport)

Arsenal da Chelsea na sa ido kan ɗan wasan tsakiyar Inter Milan da Faransa, Andy Diouf, mai shekara 23. (Caught Offside)

Brighton da Tottenham da Juventus da Atletico Madrid da Borussia Dortmund na cikin waɗanda ke zawarcin ɗan wasan bayan Benfica, ɗan ƙasar Portugal mai shekara 18, Daniel Banjaqui. (4-4-2.ch)

Ɗan wasan gaban Atletico Madrid kuma ɗan ƙasar Argentina, Julian Alvarez, mai shekara 26, na neman sabon wakilin ƴan wasa bayan ya kawo ƙarshen yarjejeniyarsa da Fernando Hidalgo sakamakon gazawar komawarsa ƙungiyar Barcelona a lokacin bazara. (Mundo Deportivo)

Bayern Munich na zawarcin ɗan wasan Barcelona, ​​Dani Olmo, mai shekara 28; daraktan wasanni na Bayern, Max Eberl, ya taɓa yin aiki tare da wannan ɗan wasan tsakiyar na Spain a ƙungiyar RB Leipzig. (Fichajes)