Magunguna shida da ke rage wa maza kuzari

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Bincike daban-daban sun gano cewa akwai wasu magunguna da ake yawan amfani da su da ke da tasiri mai yawa wajen rage ƙarfin maza.

A ƙasa akwai wasu nau'o'in magunguna da ya kamata maza su yi hattara da su domin ka da su rasa ƙarfinsu na maza.

Rayuwar jima'i na daga cikin muhimman buƙatun ɗan'adam, amma a wasu lokuta ana fuskantar matsaloli da ƙalubale a wannan fanni.

Akwai dalilai da dama da kan haifar da irin waɗannan matsaloli, amma wasu daga cikinsu na da alaƙa da amfani da wasu nau'o'in magunguna guda shida, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na ANI ya bayyana a wani rahoto na musamman da ya wallafa kan wannan batu.

Maganin rage raɗaɗi

Mutane da dama ba sa jinkirin amfani da magungunan rage raɗaɗi ko da kuwa ƙananan ciwo ne suke ji.

Amma ka san cewa waɗannan magungunan rage zafin na iya yin tasiri ga ƙarfin maza tare da rage ingancinsa yayin saduwa?

Wasu magungunan rage zafi na iya hana samar da ƙwayoyin halittar haihuwa tare da kawo cikas ga wasu muhimman sinadaran jiki da ke taka rawa wajen saduwar maza da mata.

Magungunan rage damuwa

Mutane da dama da ke fama da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa ko damuwa kan yi amfani da magunguna domin rage tsoro da tashin hankali.

Sai dai irin waɗannan magunguna na iya rage sha'awar jima'i.

Haka kuma, suna iya sa mutum ya rasa ƙwarin gwiwa ko sha'awar saduwa.

A wasu lokuta ma, suna iya haifar wa maza da matsalolin rashin ƙarfin maza gaba ɗaya.

Magungunan hana daskarewar jini

Magungunan da ake amfani da su wajen rage sinadarin cholesterol a jiki su ma na iya taka rawa wajen rage ƙarfin maza.

Masana lafiya sun ce irin waɗannan magunguna na iya yin tasiri ga yadda ƙwayoyin halittar haihuwa ke aiki.

Bincike: Wannan maganin da aka yi domin cutar zuciya to amma ya zama akasin hakan inda ya zama maganin matsalar rashin ƙarfin maza

Tanzaniya: Gwamnati ta amince da wasu magungunan ƙara ƙarfin maza

Bincike ya nuna cewa wasu magungunan da ake amfani da su wajen magance matsalolin kitsen jini ko toshewar jijiyoyin jini na iya haifar wa wasu maza matsaloli yayin saduwa da matansu.

Magungunan rage damuwa da baƙin ciki

Waɗannan magunguna, waɗanda aka fi sani da benzodiazepines, ana amfani da su sau da yawa wajen magance matsalolin damuwa da tashin hankali, ciki har da wasu irin matsanancin tsoro da mutum kan ji ko da babu wata barazana ta zahiri.

Sauran matsalolin da ake amfani da waɗannan magunguna wajen magancewa sun haɗa da rashin barci da kuma ciwon jiki.

Sai dai kuma, daga cikin illolinsu akwai yin tasiri ga aikin ƙwayoyin halittar haihuwa na maza tare da shafar sha'awa da yanayin motsin zuciya.

Magungunan hawan jini

Mutanen da ke amfani da magungunan rage hawan jini ma na iya fuskantar wata matsala, wato raguwar kuzari da ƙarfin jiki.

Waɗannan magunguna suna aiki kai tsaye kan jijiyoyin jini, sannan kuma suna tasiri ga tsarin jijiyoyin jiki.

Wasu masana sun kuma bayyana cewa waɗannan magunguna na iya haifar da wasu matsaloli da suka shafi gabobin haihuwa, ba ga maza kaɗai ba har ma da mata.

Magunguna toshewar hanci

Magungunan da ake iya saya kai tsaye ba tare da takardar likita ba, irin su magungunan buɗe hanci da rage cunkoson majina, su ma suna da wasu illa.

Daga cikin illolinsu akwai haifar da matsaloli wajen saduwar aure ga maza da mata.

Ku je ku ga likita

Yi magana da likitanka idan kana zargin wani magani da kake amfani da shi yana yin tasiri mara kyau ga ƙarfin jima'inka ko sha'awarka ta saduwa.

Ka da ka daina shan kowane irin magani da kanka ba tare da tuntuɓar likita ko ƙwararren ma'aikacin lafiya ba tukuna.