Me zai faru idan Hamas ta zubar da makamanta?

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Ƙungiyar Hamas da ke Gaza ta amince da "zubar da duka makamanta" sakamakon cimma yarjejeniya da kwamitin zaman lafiyar da Trump ya kafa, bayan tattaunawa ''mai zafi'' ta tsawon watanni.
Yayin da yake bayyana matakin a matsayin ''kafa sabon babi'', kwamitin ya ce Hamas za ta zubar da makaman ne bayan janyewar sojojin Isra'ila daga Gaza.
To sai dai har yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba game da matakin.
Wani jami'in Amurka ya shaida wa masu aiko da rahotonni cewa Shugaba Trump zai yi ''matuƙar rashin jin daɗi'' idan Isra'ila ta ƙi amincewa ta fice daga Gaza - wata ƙa'ida da Isra'ilar da Hamas duka suka amince a lokacin cimma yarjejeniyar mai matakai 20 a watan a watan Otoban bara.
A Gaza kuwa, mutane ba su yi farin ciki da wannan mataki na Hamas ba, kamar yadda wakilin BBC Rushdi Abualouf, da ke aiko da rahotanni daga Alkahira ya bayyana.
''Bayan shekaru ana ƙulla yarjejeniyoyin tsagaita wuta da dama waɗanda suka gaza, Falasɗinawa da yawa sun rasa ƙwarin gwiwa kuma suna kallon duk wata sabuwar yarjejeniyar siyasa da shakku," kamar yadda ya rubuta.
"Mutane da yawa har yanzu ba su da cikakken ƙwarin gwiwa daga duka ɓangarorin Hamas da Isra'ila, kasancewar yarjejeniyoyin da aka ƙulla a baya sun sha watsewa ba tare da sun kawo wani gagarumin sauyi ga rayuwar al'umma ba."
Mene ne ke ƙunshe a cikin shirin?
Takardar yarjejeniyar mai shafuka huɗu da BBC ta gani ta nuna cewa za a aiwatar da shirin a matakai daban-daban, inda amincewar Hamas za ta kasance tana da alaƙa da janyewar sojojin Isra'ila a hankali daga Gaza, tare da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta Falasɗinawa da za ta samu goyon bayan rundunar ƙasa da ƙasa da
Jami'an Amurka sun ce an tsara shirin ne ta yadda ba za a dogara ga amincewa tsakanin Hamas ko Isra'ila ba, sai dai a tabbatar da cika alƙawuran da aka ɗauka. Don haka, ba ɗaya daga cikin ɓangarorin biyu da zai aiwatar da mataki na gaba, ba tare da ɗayan ya aiwatar da nasa sharaɗin ba.
Sun ce za a fara ne a karɓe makaman ƙananan ƙungiyoyin Gaza, kafin a fara zubar wa da lalata abin da suka kira kayayyakin Hamas ciki har da hanyoyin ƙarƙahin ƙasa n ajiyar makamai, da rumbunan makamansu da kuma wuraren ƙera su - matakin da suka ce zai ɗauki tsawon lokaci ana yi.

Asalin hoton, Reuters
Idan aka kammala duka matakan yarjejeniyar, sabuwar hukumar Falasdinawa za ta karɓe iko da duka makaman Gaza.
Amurka da jami'an kwamitin zaman lafiyar sun ce rundunar ƴansandan Hamas a Gaza za ta miƙa makamanta da hukumar da za ta karɓe ikon Gazar.
Daga nan sai a fara batun ''aikin lalata kayyakinta'', manyan makamai da za su ƙunshi ruguza hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da rumbunan ajiye makamanta da kwance ɗamarar mayaƙanta da ke kula da cibiyoyin.
Hakan zai faru cikin ƙwarewa. Sai dai ɗaya daga cikin tambayoyin da ake ci gaba da yi shi ne wane ne zai kula da makaman da aka karɓe tare da adana su.
Daga ƙarshe duka makaman da aka karɓe a Gaza za su koma ƙarƙashin ikon hukumar Falasdinawa.
Me zai iya faruwa a gaba?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Har yanzu ana ci gaba da ɗora ayoyin tambayoyi kan janyewar sojin Isra'ila.
Wakiliyar BBC ta Arewacin Amurka, Shaimaa Khalil, ta rubuta cewa: "Zuwa yanzu Firaministan Isra'ila Benjamin bai nuna cikakkiyar niyyar janye sojojin Isra'ila daga Gaza na har abada ba, domin yana fuskantar matsin lamba daga abokan haɗakar gwamnatinsa na ɓangaren masu tsattsauran ra'ayi na dama, waɗanda suka daɗe suna adawa da irin wannan mataki."
Ta ce har ila yau akwai tambayoyi da dama game da yadda za a aiwatar da shirin. Misali, wa sojojin Isra'ila za su miƙa wa ikon yankin yayin janyewarsu, da kuma ko yankin kariya da aka sani da Yellow Line zai kasance cikin wuraren da za a janye daga cikinsu.
Shi kuwa Abualouf cewa ya yi har yanzu lokaci bai yi ba da za a iya tantance ko za a aiwatar da yarjejeniyar yadda aka tsara ba.
amma ya ce idan yarjejeniyar ta tabbata kuma aka aiwatar da ita, za ta kasance "mataki na farko mai nagarta kuma abin dogaro" wajen kawo ƙarshen yaƙin Gaza, da ya shafe kusan shekaru uku yana yi.

Asalin hoton, Reuters
Matakin na Hamas na zuwa ne bayan da ta kammala gudnar da zaɓukan shugabanninta, inda aka zaɓi Khalil al-Hayya mazaunin Gaza a matsayin shugaban ƙungiyar.
Wasu jami'an Falasɗinawa da ke cikin tattaunawar sun ce suna ganin sabbin shugabannin Hamas sun shirya ɗaukar wani mataki da suka kira mafi muhimmanci a fanni siyasa da tarihin ƙungiyar, sakamakon tsananin halin ƙunci da matsalar jinƙai da Falasɗinawa sama da miliyan biyu ke fuskanta a Gaza.
A ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ne Hamas ta ƙaddamar da hari cikin Isra'ila inda ta kashe mutum 1,299 tare da yin garkuwa da 251.
Lamarin da ya sa IKsra'ila ta mayar da martani ta hanayr ƙaddamar da manyan hare-haren soji a Gaza, lamarin da ya yi sanadiyyar kisan mutum 73,290, ciki har da ƙananan yara 21,280, a cewar ma'aikatar lkafiyar Hamas da ke Gaza, wadda Majalisar Dinkin Duniya ke ɗaukar alƙalumanta a matsayin sahihai.
A watan Oktoban bara ne aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu. Amma ma'aikatar lafiyar Hamas ta ke aƙalla Falasɗinawa 1,168 ne Isra'ila ta ke tun daga lokacin ta hanyar hare-haren da take ƙaddamarwa a Gaza.
Nan ba da ''jimawa'' gaba ne Masar za ta karɓi baƙuncin tattaunawar masu shiga tsakani a yakin na Gaza, kamar yadda kafar yaɗa labaran Al-Qahera mai alaƙa ga gwamnatin ƙasar ta ruwaito a ranar Juma'a.
Masu shiga tsakani a yaƙin na Gaza sun haɗa da Masar da Amurka da Qatar da kuma Turkiyya.












