Abin da muka sani kan kashe-kashe a Jos

Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang

Asalin hoton, X/Caleb Mutfwang

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin jihar Filato ta ayyana dokar hana zirga-zirga ta kwana biyu a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa bayan wani mummunan hari a ranar Lahadi, wanda bayanai suka ce ya yi sanadiyyar rayukan mutane da dama.

Haka nan an samu mutane da yawa waɗanda suka samu rauni a harin wanda aka kai yankin Gari Ya Waye na unguwar Rukuba a birnin na Jos.

Kwamishinar yaɗa labarai ta jihar Filato Joyce Lohya Ramnap ta ce gwamnati ta yi Allah-wadai da "mummunan harin kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba".

Sanarwar da kwamishinar ta fitar ta ce dokar ta fara aiki ne daga tsakar dare a ranar Lahadi, kuma za ta ci gaba da aiki har ranar ɗaya ga watan Afrilun 2026.

Gwamnati ta ce ta ɗauki matakin ne domin daƙile taɓarɓarewar matsalar tsaro, sannan jami'an tsaro za su ci gaba da aiki domin gano waɗanda ke da hannu.

Gwamnati ba ta fitar da alƙaluma game da mutanen da harin ya rutsa da su ba, sai dai rahotanni jaridun cikin gida sun ce an kashe aƙalla mutum 12 yayin da wasu da dama suka tsira da raunukan harbin bindiga, kuma suke samun kulawa a asibiti.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta buƙaci al'ummar yankin da abin ya shafa su zauna a gida.

Tuni dai gwamnati ta tura jami'an tsaro masu yawa zuwa yankin da abin ya faru.

Harin ya kawo cikas ga zaman lafiyar da aka samu a baya-bayan nan a birnin na Jos.

Filato, wadda jiha ce a arewa ta tsakiyar Najeriya na daga cikin jihohin da suka daɗe suna fama da matsalolin tsaro a ƙasar, inda ake samun hare-hare a kai a kai.

A shekarun baya an sha samun rikici mai nasaba da ƙabilanci da kuma addini a garin na Jos, babban birnin jihar Filato.

Duk da ƙoƙarin da hukumomi suke yi wajen samar da zaman lafiya, a alokuta daban-daban an sha samun rikice-rikice da ke haifar da sara ɗimbin rayuka.

Bayanan da aka samu sun bayyana cewa wasu mutane ne a kan babura suka kai harin na ranar Lahadi, inda suka kashe mutane a unguwar ta Rukuba.

Bayan harin kuma matasa sun datse tituna unguwar domin nuna damuwa kan harin, lamarin da ya sanya aka shiga fargabar yaduwar rikicin.

Hare-hare a arewa ta tsakiyar Najeriya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Maris 2025 – A ƙarshe-ƙarshen watan Maris an kashe kimanin mutum 52 a wani harin da aka kai a ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato.

Lamarin ya sanya mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu ya kai ziyara yankin, inda ya yi alƙawarin cewa gwamnati za ta tabbatar an kawo ƙarshen matsalar.

Sai dai duk da haka an ci gaba da samun hare-hare a jihar.

Afrilu 2025 – An kai wani hari a ƙaramar hukumar Bassa da ke jihar Filato, kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar wa BBC.

An kai harin ne da asubahin ranar Litinin 14 ga watan Afrilu.

Gwamnatin jihar ta ce ta ɗauki ƴan jarida zuwa yankin domin ganin abin da ya faru. Wani jami'in gwamnatin jihar Yakubu Ventim ya ce ''kimanin mutum 38 zuwa 50 ne aka kashe a ƙauyen.

''Sun kai hari ne na ba-zata, inda suka kashe akasari mata da yara".

Mayu 2025 – An kashe aƙalla mutum 10 sanadiyyar rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Riyom da ke jihar Filato.

Kafofin yaɗa labarai sun ce lamarin ya faro ne daga lalata gonaki da kisan shanu, inda daga baya kuma abin ya koma rikici tsakanin ƙabilun Berom da Fulani.

Bayanin dakarun rundunar Safe Haven y ace rikicin y afara ne daga ranar Litinin 12 ga watan Mayun 2025, sa'ilin da aka zargi wasu matasa da sacewa da kashe shanun da suka shiga wata gona a ƙauyen Dayan da ke ƙaramar hukumar Riyom.

An yi zargin cewa a matakin ramuwar gayya, makiyaya sun kai hari kan ƙauyen Danchindo da yammacin ranar 13 ga watan Mayu inda suka kashe kimanin mutum hudu.