KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 30/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 30 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Kwankwaso ya koma jam'iyyar ADC tare da magoya bayansa

    ...

    Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB

    Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam’iyyar haɗaka ta ADC tare da magoya bayansa bayan ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.

    An gudanar da bikin komawarsa ne a gidansa da ke Kano, inda shuwagabannin jam’iyyar da dimbin magoya bayansa suka hallara domin tarbar sa.

    Tsohon gwamnan ya kuma buƙaci magoya bayansa su yi rajistar jamʼiyyar, tare da samun katin zaɓe na ƙasa.

    A jiya ne Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga NNPP, yana mai cewa matakin na daga cikin kokarin haɗa kai da wasu jam’iyyu domin kawo sauyi a ƙasar.

    Ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a samar da hadin gwiwa tsakanin manyan ‘yan adawa, domin tinkarar kalubalen da Ƙasar ke fuskanta da kuma inganta shugabanci.

    Sai dai har yanzu ɓangaren NNPP ba su fitar da wata sanarwa mai karfi kan ficewar tasa ba.

  2. Trump ya sake cewe Amurka na tattaunawa ta gaskiya da Iran

    ....

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake cewa Amurka na tattaunawa ta gaskiya da Iran, wadda ka iya kai wa ga 'daukar matakin sojin idan har ba a cimma yarjejeniya ba'.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya bayyana Iran a matsayin “sabuwar gwamnati” ta Iran, wadda ya ce ta fi ta baya “yin tunani da hankali”.

    Trump ya ce an samu “gagarumin ci gaba”, amma ya kuma yi barazanar cewa “idan ba a cimma yarjejeniya nan kusa ba, ko kuma ba a buɗe mashigin Hormuz ga harkokin kasuwanci nan take ba,” Amurka za ta “lalata gaba daya” dukkan tashoshin wutar lantarki da tsibirin Kharg, da kuma wasu cibiyoyin tace ruwan tekun Iran.

    Ya jaddada cewa har yanzu Amurka ba ta lalata wadannan muhimman wurare “da gangan ba”.

    Trump ya kuma ce wannan mataki zai kasance martani ne ga “sojoji da sauran mutane da dama da Iran ta kashe a cikin shekaru 47 na mulkin tsohuwar gwamnatin da ya kira mai muni”.

    Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sake nanata cewa babu wata “tattaunawa kai tsaye” da ta gudana tsakanin Tehran da Washington tun bayan fara wannan rikici.

  3. Harin Iran ya haddasa gobara a matatar man Haifa da ke arewacin Isra'ila

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Wani sabon harin makami mai linzami da Iran ta kai ya haddasa gobara a wata matatar mai da ke Haifa a arewacin Isra’ila.

    Bidiyoyin da aka fitar sun nuna yadda wuta ta kama ɗaya daga cikin manyan tankunan matatar, inda kuma hayaƙi ya rika tashi sama.

    Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa wannan ne karo na biyu da Iran ke kai hari kan matatar mai ta Haifa a yayin wannan rikici na baya-bayan nan.

    Rahotanni sun ce an samu nasarar shawo kan gobarar.

    Hukumar kashe gobara ta Isra’ila ta shaida wa Reuters cewa wani tankin ajiyar mai ya samu illa sakamakon harin.

    Isra’ila da na da matatun mai guda biyu ne.

  4. PDP tsagin Wike ta zaɓi sabbin shugabanninta

    ....

    Asalin hoton, PDP

    Jam'iyyar PDP tsagin Mininstan Abuja, Nyesom Wike ta zaɓi Abdulrahman Mohammed a matsayin sabon shugabanta na ƙasa yayin da Samuel Anyanwu ya samu matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa.

    Mohammed da Anyanwu sun samu kujerunsu ta hanyar masalaha, tare da sauran mambobin kwamitocin jam'iyyar ta ƙasa guda 19 a babban taron jam'iyyar na shekarar 2026 da aka gudanar a babban filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a ranar Lahadi.

    Daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar da suka halarci taron akwai tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido da tsohon shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, da sauransu.

    Wike, wanda aka bayyana a matsayin jagoran jam'iyyar ta ƙasa ya ce an fara warkar da PDP daga matsalolin da take fuskanta.

    Ya tabbatar wa mambobi cewa PDP za ta shiga zaɓe a shekarar 2027.

  5. Abin da muka sani kan kashe-kashe a Jos

    ....

    Asalin hoton, X/Caleb Mutfwang

    Gwamnatin jihar Filato ta ayyana dokar hana zirga-zirga ta awa kwana biyu a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa bayan wani mummunan hari a ranar Lahadi, wanda bayanai suka ce ya yi sanadiyyar rayukan mutane da dama.

    Haka nan an samu mutane da yawa waɗanda suka samu rauni a harin wanda aka kai yankin Gari Ya Waye na unguwar Rukuba a birnin na Jos.

    Kwamishinar yaɗa labarai na jihar Filato Joyce Lohya Ramnap ta ce gwamnati ta yi Allah-wadai da "mummunan harin kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba".

    Sanarwar da kwamishinar ta fitar ta ce dokar ta fara aiki ne daga tsakar dare a ranar Lahadi, kuma za ta ci gaba da aiki har ranar ɗaya ga watan Afrilun 2026.

    Gwamnati ta ce ta ɗauki matakin ne domin daƙile taɓarɓarewar matsalar tsaro, sannan jami'an tsaro za su ci gaba da aiki domin gano waɗanda ke da hannu.

    Gwamnati ba ta fitar da alƙaluma game da mutanen da harin ya rutsa da su ba, sai dai rahotanni jaridun cikin gida sun ce an kashe aƙalla mutum 12 yayin da wasu da dama suka tsira da raunukan harbin bindiga, kuma suke samun kulawa a asibiti.

  6. 'Iran ta fara jerin hare-harenta na 87 kan mafakar sojin Amurka da Isra'ila'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta fara jerin hare-haren makamai da jirage marasa matuki karo na 87 kan maɓoyar sojojin Amurka da Isra’ila da cibiyoyin su.

    A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce dakarunta sun kai hari kan “cibiyoyin kula da zirga-zirgar jiragen Amurka a UAE da wurin ma’ajin kayan makamai da moɓoyar sojojin Amurka da Isra’ila ciki har da “tsofaffin sansanonin Amurka guda biyar da kuma cibiyoyin soji a kudanci da tsakiya da arewa.”

    Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun Iran ɗin sun kai hari kan wuraren Isra'ila da suka haɗa da “Haifa Bay, da Kiryat Shmona da Tel Aviv da Beersheba da Dimona da Al-Kharj da Juffair, da kuma Victoria.”

    Sanarwar ta ce "rundunar ta fara wannan jerin hare-haren ne tun farkon daren jiya kuma har yanzu yana ci gaba.”

    IRGC ta bayyana cewa wannan gagarumin hari an aiwatar da shi ne da “makaman masu linzami da suka haɗa da Imad, Qiyam, da Khorramshahr 4 da kuma jiragen sama marasa matuka.

  7. Gawuna ya ajiye muƙamin da Tinubu ya ba shi

    ...

    Asalin hoton, Abubakar Musa DK

    Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamnan Jihar na jam’iyyar APC a 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya ajiye muƙaminsa na Shugaban Hukumar Gudanarwar bankin bayar da lamunin gidaje na Najeriya.

    Sanarwar da tsohon mataimakin gwamnan ya fitar ta nuna cewa ajiye aikin zai fara ne daga gobe Talata, 31 ga Maris, 2026.

    A cikin sanarwar, Gawuna ya ce "na ajiye aikin ne domin bin umarnin shugaban ƙasa da ya buƙaci duk mai riƙe da muƙamin siyasa kuma yake son yin takara, ya ajiye muƙami domin yin biyayya ga dokar zaɓe".

    A cikin wasiƙar ta Gawuna wadda ya tura wa Sakataren gwamnatin Tarayya, Gawuna ya nuna godiya ga shugaba Tinubu kan amincewa da shi da ya naɗa shi a matsayin shugaban Hukumar Gudanarwar bankin bayar da lamunin gidaje na Najeriya.

    A makon da ya gabata ne aka yi ta raɗe-raɗin cewa tsohon mataimakin gwamnan, wanda ake wa kallon na hannun damar tsohon shugaban jam'iyyar APC ne ƙasa, Abdullahi Ganduje, cewa zai fice daga jam'iyyar APC, wadda ya yi takarar gwamna ƙarƙashinta a 2023.

    A watan Janairun 2024 ne kotun ƙolin Najeriya ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano duk kuwa da cewa a watan Satumban 2023 kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen jihar Kano ta ayyana Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

    Tun farko hukumar zaɓen Najeriya ta ayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar ta Kano da aka yi a watan Maris ɗin 2023, inda ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya zo a matsayi na biyu da ƙuri'u 890,705.

  8. 'Iran na shirin kafa sabon tsarin kula da Mashigar Hormuz'

    ...

    Asalin hoton, Corbis via Getty Images

    Iran ta bayyana shirin kafa sabon tsarin da zai kula da Mashigar Hormuz, wanda Majalisar Dokokin ƙasar za ta amince da shi cikin gaggawa, in ji ɗan majalisa, Alaeddin Boroujerdi.

    Alaeddin Boroujerdi ya ce "A ƙarkashin wannan sabon tsarin, ba za a ba kowanne jirgi damar wucewa ba sai da izinin Iran."

    Haka zalika, Boroujerdi ya ce Iran na shirin sanya haraji ga duk jiragen da ke wucewa ta mashigar.

    “Idan aka yi la’akari da tsaro da kuma samar da ayyuka ga jiragen da ke wucewa, akwai buƙatar a kafa tsarin karbar haraji na wucewa ta mashigar,” in ji shi.

    Ɗan majalisar ya kuma bayyana cewa “lokaci ya yi” da Iran za ta fice daga yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nulkiliya, inda ya ce yarjejeniyar ta rasa muhimmancinta bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

  9. Borno: Zulum ya sauke dukanin kwamishinoninsa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da sauke dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar nan take.

    Wannan matakin na zuwa ne domin samar da yanayi mai kyau ga duk wani memba da zai so tsayawa takarar muƙaman zaɓe a zaɓuɓɓukan gaba masu zuwa.

    Gwamna Zulum ya umurci dukkan kwamishinoni da su miƙa al’amuran ma’aikatunsu ga Sakatarorin Dindindin kafin ranar Jumma’a, 3 ga Afrilu, 2026.

    Wannan umurni zai tabbatar da cewa dukkan ayyuka da al’amuran gwamnati suna ci gaba da gudana ba tare da tangarda ba.

    A cikin sanarwar da ofishin Gwamnan ya fitar, Zulum ya yi godiya ta musamman ga kwamishinonin da suka sauka bisa sadaukarwa da jajircewa, da gudummawar da suka bayar wajen ci gaban jihar da hidimar al’ummar Borno.

    Ya bayyana cewa irin wannan himma ta taimaka matuƙa wajen ganin an samu cigaba a fannoni daban-daban na jihar.

    Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa matakin zai bai wa duk wanda ke da burin takara damar mai da hankali kan shirin neman muƙaminsa cikin sauƙi.

  10. Mun kai hari kan cibiyoyin kula da zirga-zirgar jiragen Amurka a UAE - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Iran sun bayyana cewa sun kai hari da jiragen sama marasa matuƙa kan cibiyoyin kula da zirga-zirgar jiragen Amurka da ke cikin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

    A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce daga daren jiya zuwa safiyar yau, an kai hare-hare kan na'urorin abokan gaba da ke UAE, waɗanda ke da alhakin gano da kuma daƙile makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

    Sanarwar ta kuma ƙara da cewa jiragen nasu sun kai hari kan wasu wurare da ke da alaƙa da sojojin Amurka a cikin ƙasar.

  11. Za mu kai hari kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila - Iran

    ...

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Hedikwatar Khatam al-Anbiya, wacce ita ce babbar cibiyar da ke kula da daidaita ayyukan rundunonin sojin Iran, ta yi barazanar kai hare-hare kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila da ke yankin.

    Mai magana da yawun hedikwatar, Ebrahim Zolfaghari, ya ce wannan mataki na ramuwar gayya ne inda ya zargi Amurka da Isra’ila da kai hare-hare kan gidajen fararen hula a birane daban-daban na Iran.

    A cewarsa, hare-haren da ake kai wa Iran sun haddasa asarar rayukan manyan kwamandojin soja da jami’ai a lokacin rikicin.

    Daga cikin waɗanda aka kashe har da Ali Khamenei, tsohon jagoran addinin Iran, wanda rahotanni suka ce an kashe shi a hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, ranar farko ta barkewar yakin.

  12. Wace jam'iyya Kwankwaso zai koma bayan fitarsa daga NNPP?

    ....

    Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB

    Tun bayan da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da ficewa daga jam'iyyarsa ta NNPP, masana da masu bibiyar siyasa ke ci gaba da hasashen jam'iyyar da zai koma.

    Cikin sanarwar ficewar ta sa, Sanata Kwanwaso ya ce matakin ya zama tilas ne la'akari da yanayin siyasar Najeriya ke ciki ''wanda ke bukatar haɗin kai''.

    ''Matakin ya zama tilas domin haɗa kai da wasu jam'iyyun don kawo wa ƙasarmu sauyi nagari'', kamar yadda Kwankwason ya bayyana.

    Tuni dai masana da masu sharhin siyasa suka fara bayayna hasashensu na inda Kankwason zai koma.

  13. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin ga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.