Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • Sadis Buba

Rahoto kai-tsaye

Daga Ibrahim Yusuf Mohammed da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Ana tuhumar wata fitacciyar ƴar TikTok da kashe saurayinta a Dubai

    Detained in Dubai

    Asalin hoton, Detained in Dubai

    Wata fitacciyar ƴar TikTok mai shekara 23 daga Gravesend da ke Kent a Birtaniya, Brooke George, na fuskantar tuhuma kan zargin kashe saurayinta a Dubai.

    Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam a Haɗaɗɗiyar Daular Laraba mai suna Detained in Dubai, ta ce tana iya fuskantar hukuncin kisa ta hanyar harbi idan aka same ta da laifi.

    Ƙungiyar ta ce George na fuskantar tuhuma ne kan zargin daɓa wa wani mutum wuƙa har lahira, wanda suka fara soyayya bayan sun haɗu ta yanar gizo.

    "George ta ce ta ɗauki wuƙar ne domin kare kanta a yayin da saurayin nata ya ke ƙoƙarin illata ta," in ji ƙungiyar.

    Ƙungiyar ta buƙaci a bayar da belinta tare da duba lamarin.

    An kama George, wadda tsohuwar ma'aikaciyar kamfanin John Lewis ce, a safiyar ranar 22 ga Yuni, kuma daga baya aka gurfanar da ita bisa zargin kisan kai.

    Idan aka same ta da laifi, tana iya fuskantar hukuncin kisa ƙarƙashin dokokin UAE.

    Yayin da ake tsare da ita a ofishin ƴansanda na Bur Dubai, George ta yi zargin cewa an tilasta mata cire kayanta gaba ɗaya a gaban jami'an ƴansanda maza ba tare da wata jami'ar mace a wurin ba, abin da ta bayyana a matsayin abin kunya da kuma tayar da hankali, kamar yadda ƙungiyar Detained in Dubai ta bayyana.

  2. CBN ta umurci bankuna su kulle asusun mutanen da ke da alaƙa da ta'addanci

    CBN

    Asalin hoton, @cenbank

    Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi su rufe asusun kwastomomin da ake zargi da ɗaukar nauyin aiyukan ta'addanci.

    A wata sanarwa da Daraktan Sashen Kula da Ka'idojin Bankuna na CBN, Olubunmi Ayodele-Oni ya sanya wa hannu, bankin ya ce umarnin ya biyo bayan sabbin sunayen da Kwamitin kula da ƙa'idojin sanyaTakunkumi na Najeriya da kuma Hukumar Kula da Kadarorin Ƙetare na Ma'aikatar Baitulmalin Amurka suka fitar.

    A baya bayan nan Amurka ta sanya sunayen mutum uku da kamfanoni shida da ake zargi da alaƙa da ɗaukar nauyin ƙungiyar ISIS, ciki har da masu gudanar da kasuwancin canjin kuɗaɗe a Najeriya.

    Bankin na CBN ya umarci dukkan cibiyoyin kuɗi da su gaggauta rufe da duk wani kuɗi, kadarori ko wasu albarkatun tattalin arziki da mutanen ko kamfanonin da aka sanya wa takunkumi ke da su ko suke iko da su, ba tare da sanar da su ba.

    Haka kuma ya umarci bankunan su tantance dukkan kwastomominsu, da masu cin gajiyar asusu da kuma ma'amaloli domin tabbatar da sun dace da sabon takunkumin.

    Babban Bankin ya kuma ce kada a bai wa mutanen ko kamfanonin da aka sanya wa takunkumin kuɗi, ko ayyukan kuɗi ko wasu albarkatun tattalin arziki damar hada-hada kai tsaye ko ta bayan fage.

    Sannan ya umarci cibiyoyin kuɗi su kai rahoton duk wata ma'amala da ake zargi ga sashen dake tattara bayanan siriri na hukumar kula da shige a ficen kuɗaɗe ta Najeriya NFIU idan an tabbatar ko an yi yunƙurin yin ma'amala da waɗanda ke cikin jerin sunayen.

    Sanarwar ta kuma umarci Bankunan da su aika wa CBN rahoto cikin sa'o'i 48, inda za su bayyana asusun da abin ya shafa, adadin kuɗaɗen da aka rufe da kuma matakan da suka ɗauka.

  3. Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ne ke haddasa matsalolin tsaro a Sokoto - Aliyu

    Sokoto Govt

    Asalin hoton, Sokoto Govt

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ne ke haddasa kusan kashi 80 na matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

    Aliyu ya ce mafi yawan masu aikata laifuka a jihar da ƴanbindiga na amfani da miyagun ƙwayoyi kafin su aikata ta'addanci.

    Gwamnan wanda mataimakinsa, Idris Mohammed Gobir, ya wakilta ya bayyana hakan ne a yayin wani taron lacca da aka shirya domin tunawa da ranar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da safararsu.

    "Kashi 80 cikin 100 na matsalolin tsaron da ke addabar jiharmu suna da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi. Waɗannan mutane na amfani da ƙwayoyi masu haɗari. Mutumin da yake cikin hankalinsa ba zai dubi wani ɗan adam ya kashe shi ba," in ji shi.

    Aliyu ya kuma buƙaci matasa su guji shiga harkar shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi domin samun damar zama shugabanni da fitattun mutane a nan gaba.

    Ya ce gwamnatin jihar ta kafa ofishin babban mataimaki na musamman kan daƙile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi domin jagorantar shirye-shiryen wayar da kan jama'a.

  4. Ƴansanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Kenya

    Kenya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗaruruwan matasa sun yi tattaki a birnin Mombasa da ke gabar tekun Kenya domin girmama waɗanda aka kashe a lokacin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati ta Gen-Z shekaru biyu da suka gabata.

    Masu zanga-zangar sun saka baƙaken kaya tare da yin lulluɓi da tutocin Kenya, kuma suna ɗauke da allunan da ke kira da a yi adalci da kuma kawo ƙarshen kisan gillar da jami'an tsaro ke yi wa mutane ba tare da yin shari'a ba.

    Kenya

    Asalin hoton, Getty Images

    Kenya

    Asalin hoton, Getty Images

    A Nairobi, ƴan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan taron jama'a a wajen babban ofishin ƴan sanda na birnin bayan sun tsare wasu masu fafutuka kusa da majalisar dokoki.

    Ƴan sandan sun kuma hana motoci shiga tsakiyar garin, abin da ya sa tituna suka kasance fayau.

    Kenya

    Asalin hoton, Getty Images

    Kenya

    Asalin hoton, Getty Images

    Su ma ƴan kasuwa ba su sakakance ba, domin mafi yawancin shaguna sun kasance a rufe, yayin da ma'aikatu da yawa suka ce ma'aikatansu su yi aiki daga gida.

    An kuma tsaurara tsaro a faɗin babban birnin na Kenya, inda ƴan sanda suka sanya shingaye a manyan hanyoyi domin taƙaita shiga tsakiyar birnin.

    Kenya

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Iran ta musanta shirin sayen hatsi daga Amurka

    Qalibaf

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya yi fatali da kalaman hukumomin Amurka cewa za a yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen Iran da aka riƙe wajen sayen hatsi daga Amurka.

    Qalibaf, wanda shi ne kakakin tawagar masu tattaunawa ta Iran, ya wallafa a shafinsa na X cewa yana zargin Amurka da yaudara kan batun sakin kadarorin Iran.

    Ya rubuta cewa: "Abin da Amurka ta fi fitarwa shi ne waken soya da aka yi wa sauyin ƙwayoyin halitta, sai karya alƙawari da kuma maganganun da ba su da tushe."

    A baya bayan nan, Shugaban Amurka Donald Trump da Mataimakinsa JD Vance sun sha bayyana cewa za a yi amfani da kuɗaɗen wajen sayen masara da waken soya da kuma alkama daga Amurka.

    Tun da farko, Gwamnan Babban Bankin Iran, Abdolnaser Hemmati, ya ce yarjejeniyar da Iran da Amurka suka cimma a shekarar 1402 ta kalandar Iran, ta tanadi cewa za a yi amfani da dala biliyan shida na farko ne wajen sayen kayayyakin masarufi da magunguna.

    Sai dai ya ce idan kayayyakin Amurka sun fi na sauran ƙasashe arha da inganci, babu wani abin da zai hana Iran sayen su, yana mai cewa a shekarun baya ma an riƙa gudanar da irin waɗannan sayayya ta hannun manyan kamfanonin Amurka da na Turai.

  6. An ceto mutum 10 daga ginin da ya rufta a jihar Legas

    An ceto mutum 10 da ransu bayan wani ginin bene ya rufta da su jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya

    Lamarin ya faru ne a kan titin Old Ojo Road kusa da tashar motar Alakija da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Badagry, inda rahotanni suka ce har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano ko akwai wasu da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:37 na safe, inda ta tura jami'anta zuwa wurin da lamarin ya faru.

    Babbar daraktar hukumar a jihar Legas, Margaret Adeseye, ta tabbatar da cewa an ciro mutum 10 da rai daga cikin ɓaraguzan ginin.

    "Waɗanda aka ceto sun samu raunuka daban-daban, kuma an miƙa su ga likitoci domin duba lafiyarsu," in ji ta.

    Ta ƙara da cewa ana ci gaba da aikin ceto yayin da jami'ai ke binciken wurin domin gano ko akwai wasu da suka rage a ƙarƙashin ginin.

    Hukumomi sun ce har yanzu ba a gano musabbabin ruftawar ginin ba, amma za a fara bincike da zarar an kammala aikin ceto.

  7. Ƴanbindiga sun kashe ƴansanda biyu a jihar Kaduna

    Kwamishinan Yan sandan jihar Kaduna

    Asalin hoton, Mansir Hassan

    Rundunar ƴansandan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce jami'anta sun ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

    Sai dai rundunar ƴansandan ta ce a yayin da jami'anta ke kan hanyar dawowa daga ceto mutanen, wasu ƴanbindigar sun yi musu kwanton ɓauna inda suka harbi jami'ai biyu waɗanda daga baisani suka rasu.

    A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 24 ga Yunin 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri cewa kimanin ƴanbindiga kusan 15 ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Unguwan Sa'idu da ke kusa da Birnin Gwari, inda suka yi garkuwa da wasu mutane daga gonakinsu.

    Sanarwar ta ce jami'ansu tare da haɗin gwiwar ƴan banga sun yi artabu da maharan, lamarin da ya tilasta wa ƴanbindigan tserewa cikin daji a kan babura bayan sun bar mutane 9 da suka yi garkuwa da su.

  8. Gwamnan Kano ya kafa kwamitin yaƙi da miyagun ƙwayoyi

    Abba Kabir Yusuf

    Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/FB

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa wani kwamiti na musamman domin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safarar su a jihar.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne domin magance matsalar da ke addabar yawancin matasa a jihar.

    Daga cikin ayyukan da kwamitin zai fi maida hankali su ne gano manyan wuraren da ake hada-hadar miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar, domin kai samame da kama waɗanda ake zargi.

    Sanarwar ta ce an kuma ɗora wa kwamitin alhakin tattara bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro, gano hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi da kuma ƙarfafa wa al'umma yadda za su riƙa kai rahoton ayyukan da ake zargi na da alaƙa da miyagun ƙwayoyi ko ɓata gari.

    Bugu da ƙari, kwamitin zai yi aiki tare da ɓangaren shari'a domin gaggauta yin shari'o'in da suka shafi miyagun ƙwayoyi da yanke hukunci.

    Tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar, Muhuyi Magaji Rimingado ne zai shugabanci kwamitin.

    Akwai kuma wakilai daga hukumomin tsaro irinsu NDLEA, DSS, ƴan sanda, NSCDC, Kwastam da kuma wakilai daga ma'aikatun gwamnati da sarakuna da malamai da ƙungiyoyin farar hula.

  9. Najeriya na ci gaba da kwashe mutanenta daga Afirka ta Kudu

    ...

    Rukunin ƴan Najeriya na biyu sun dawo gida daga ƙasar Afirka ta Kudu bayan da aka samu jinkiri a shirin na kwashe mutane sakamakon tashe-tashen hankula masu nasaba da ƙin jinin ƴan ci-rani.

    Fiye da ƴan Najeriya 260 ne suka isa Legas a ranar 11 ga watan Yuni bayan da suka yi rajistar dawowa da radin kansu sakamakon ƙaruwar ƙyamar baƙi da kuma fargabar tashin hankali a sassan Afirka ta Kudu.

    A ranar 15 ga watan Yuni ne dai aka sa ran tashin jirgin na biyu, sai dai an samu jinkirin gudanar da aikin, lamarin da ya sa ƴan Najeriya da dama da shirin ya shafa shiga halin rashin tabbacin lokacin da za su iya tashi.

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Najeriya Kimiebi Ebienfa, ya shaida wa BBC a ranar Alhamis cewa "'wasu ƴan Najeriya " sun koma gida da sanyin safiyar yau.

    Ya ce an dawo da "kusan mutane 50" daga Afirka ta Kudu, ya kuma ƙara da cewa ƴan Najeriya 700 da suka yi rajistar shirin ƙwashe mutanen na nan suna jiran ranar dawowar su.

    Sama da ƴan Najeriya 1,000 ne suka fara nuna sha’awar komawa gida bayan zanga-zangar ƙin jinin baƙi da kuma hare-haren da ake kai wa ƴan ƙasashen ƙetare ya bazu zuwa wasu sassan ƙasar Afirka ta Kudu, a cewar jami’an Najeriya.

  10. Wanda ake tuhuma a badaƙalar cin hanci da rashawa a Afrika ta Kudu ya amsa laifinsa

    ...

    Asalin hoton, SABC

    Vusimusi "Cat" Matlala, babban wanda ake a wani bincike da ke ci gaba da gudanarwa a Afirka ta Kudu, ya amsa laifukan cin hanci da rashawa da zamba da kuma halasta kuɗin haram a wani bangare na yarjejeniya da masu shigar da ƙara na ƙasar.

    An zarge shi da bayar da cin hanci ga manyan jami'an ƴan sanda don cin hancin rand miliyan 360 ($22m) a shekarar 2024.

    Yarjejeniyar, wadda har yanzu alƙalin kotun bai amince da ita ba, zai sa Matlala ya ba da shaida a kan "manyan jami'ai", in ji lauyan gwamnati Santhos Manilall.

    Babban kwamishinan ƴan sanda, Janar Fannie Masemola, na ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma dangane da wannan shari'a.

    Ya musanta zargin da ake yi masa.

    Manilall ya shaida wa kotun da ke birnin Pretoria cewa, an shafe kusan watanni biyu ana tattaunawa kafin cimma wannan yarjejeniya.

    Idan aka amince da ita, yarjejeniyar za ta sa Matlala, mai shekaru 49, ya shafe shekaru takwas a gidan yari.

  11. Iran ta gargaɗi Isra'ila ta fice daga Lebanon

    Esmail Ghaani

    Asalin hoton, AFP

    Esmail Ghaani, kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci reshen ƙasashen ƙetare, ya gargadi Isra'ila cewa sojojinta su fice daga ƙasar Lebanon.

    A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa nma X Mista Qaani ya ce: "Idan ba ku janye a yau ba don ra'ayin kan ku, gobe za a tilasta muku ku gudu a wulaƙance cikin ƙasƙanci."

    Tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Labanon wani ɓangare ne na yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka, kuma a ko da yaushe gwamnatin Iran ta ɗauki tabbatar da shi a matsayin wani muhimmin sharaɗi na wannan yarjejeniyar.

    To sai dai kuma ana ci gaba da arangama tsakanin sojojin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah, kuma firaministan ƙasar Isra'ila Benyamin Netanyahu ya fitar da wata sanarwa a cikin ƴan kwanakin nan domin mayar da martani kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka inda ya ce: "Za mu ci gaba da zama a cikin yankin tsaro a kudancin Labanon matuƙar akwai buƙatar yin hakan, a matsayina na firaministan Isra'ila, ina mai jaddada hakan kuma babu abin da zai canza hakan.''

  12. An kashe wani sojan Isra'ila a kudancin Lebanon

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe wani sojanta a wani abin ta bayyana a matsayin "aiki mai muhimmanci" a kudancin Lebanon.

    Duk da tsagaita wuta da aka sanar, ana samun rahotannin arangama tsakanin Isra'ila da dakarun Hezbollah a yankin.

    Wani mai magana da yawun sojojin Isra'ila ya shaidawa kamfanin dilancin labarai na AFP cewa sojan ya mutu ne a lokacin da motar sa ta kife.

    Sojojin Isra'ila sun bayyana cewa an kashe sojoji 37 da kuma wani ma'aikaci farar hula a kudancin Lebanon tun bayan fara rikici da ƙungiyar Hezbollah ya ɓarke a farkon watan Maris.

  13. Tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran ta yi atisaye a Washington

    ...

    Asalin hoton, IRNA

    Tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran da ta isa Amurka da safiyar yau ta gudanar da atisaye domin shirin tunkarar wasan da za ta yi da Masar ranar Asabar a filin wasa na Jami'ar Washington da ke Seattle.

    Hukumar ƙwallon ƙafar Iran ba ta fitar da cikakkun bayanai kan wannan atisayen ba, amma ƴan wasa 29 ne suka halarta.

    Kamfanin yaɗa labarai na Iran ya ruwaito cewa, a gobe Juma'a ne tawagar ƙasar Iran za ta gudanar da atisaye a filin wasan da za ta fafata da tawagar ƙasar Masar ranar Asabar.

    Wasan da za ta yi da ta Masar a ranar Asabar, zai yanke hukunci kan makomar tawagar ƙwallon ƙafar Iran a gasar cin kofin duniya.

    Iran ta buga wasanninta biyu na farko ne a Los Angeles (Southern California), amma wasanta da Masar za a yi ne a Seattle (jihar Washington) da ke kusa da iyakar Amurka da Kanada.

  14. Masu aikin ceto na fautukar gano waɗanda suka tsira daga girgizar ƙasar Venezuela

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Akalla mutum 164 ne suka mutu yayin da wasu 700 suka jikkata bayan girgizar ƙasa guda biyu suka afku cikin ƙanƙanin lokaci tsakanin juna a babban birnin ƙasar Venezuela ranar Laraba, in ji shugaban rikon ƙwarya Delcy Rodríguez.

    Girgizar ƙasa ta biyu ta kasance ɗaya daga cikin girgizar ƙasa mafi ƙarfi da ta afku a ƙasar ta Kudancin Amurka cikin ƙarni guda, inda ta kai maki 7.5.

    Gine-gine sun ruguje, mazauna yankin kuma sun kwararo kan tituna domin tsira da rayukansu yayin da tagwayen girgizar ƙasar suka afku.

    Rodríguez ya ayyana dokar ta ɓaci sannan ta ce an dakatar da ayyuka a filin tashin jiragen sama da tashoshin jiragen ƙasa da sauran harkokin sufuri.

    Masu aikin ceto na fafutukar nemo waɗanda suka tsira da rayukansu da ka iya kasancewa a maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, ana kuma fargabar adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa.

  15. Ɗan takarar shugaban ƙasa a Colombia ya amince da shan kaye

    ...

    Asalin hoton, REUTERS/Sergio Acero

    Ɗan takarar jam'iyya mai sassaucin ra'ayi a zaɓen shugaban ƙasar Colombia, Iván Cepeda, ya amince da shan kaye kwanaki uku bayan da al'ummar Colombia ta kaɗa ƙuri'u.

    Sakamakon farko da aka fitar sa'o'i bayan rufe rumfunan zaɓe ya nuna cewa Cepeda ya sah kaye ne da ƙasa da kashi ɗaya a hannun abokin hamayyarsa, ɗan kasuwa mai ra'ayin mazan jiya Abelardo de la Espriella.

    Da farko Cepeda ya ce zai jira ƙidaya na ƙarshe bisa doka - wanda har yanzu ke ci gaba da gudana - amma a ranar Laraba ya sanar da cewa "ya yanke shawarar karɓar sakamakon".

    Ya soki shugaban Amurka Donald Trump saboda goyon bayan abokin hamayyarsa de la Espriella.

  16. Trump ya buƙaci Majalisa ta amince masa kashe dala biliyan 67 kan tsaro

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar White House ta buƙaci ƴan majalisar su amince ta kashe dala biliyan 87.6, akasari kan abin da ta kira "buƙatun gaggawa" da ke da alaka da yaƙin da Amurka ke yi da Iran, kwana guda bayan da majalisar dokokin ƙasar ta zartar da wani kuduri na tsawatarwa kan yaƙin.

    Galibin kuɗin - $67bn - na Ma'aikatar tsaro ta Amurka ne, in ji Fadar White House.

    Amma buƙatar na fuskantar ƙalubale a Majalisa.

    Rikicin na Iran dai na fuskantar suka daga masu kaɗa ƙuri'a gabanin zaɓen tsakiyar wa'adi na Amurka da za a yi a watan Nuwamba, ko da yake a halin yanzu tsagaita wuta na aiki.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma samu saɓani tsakaninsa da wasu ƴan jam’iyyarsa ta Republican kan batun Iran, kuma an ruwaito cewa ya yi sa-in-sa da wani sanata a ranar Laraba.

    Sanatan, Bill Cassidy na Louisiana, na ɗaya daga cikin tsirarun ƴan jam’iyyar Republican da suka bijire wa shugaban ƙasar a ranar Talata ta hanyar jefa ƙuri’a don zartar da wani mataki na neman ya dakatar da yaƙin ko kuma ya nemi amincewar majalisa kafin ya ci gaba da ɗaukar matakin soji.

  17. An jibge ƴansanda a Nairobi kan zanga-zangar matasa a Kenya

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Ƴansanda a Kenya sun rufe wasu muhimman titunan da ke shiga tsakiyar birnin Nairobi gabanin zagayowar cika shekara biyu da gudanar da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka yi a ƙasar ƙarkashin jagorancin ƙungiyar matasa ƴan bana-bakwai.

    Dubban ƴan ƙasar Kenya ne suka yi zanga-zangar nuna adawa da shirin ƙara harajin da aka yi a watan Yunin 2024, wanda ya kai ga yin kutse zuwa cikin harabar majalisar dokokin ƙasar, inda daga bisani aka janye ƙudirin dokar.

    Masu zanga-zangar sun ce suna neman a hukunta masu hannu a kisan fiye da mutane 80 tare da jikkata wasu da dama yayin zanga-zangar ta 2024 da kuma zanga-zangar tunawa da ranar da aka yi a bara.

    Mutane da dama sun maƙale a kan hanya da safiyar ranar Alhamis bayan da jami’an tsaro suka tare hanyar shiga tsakiyar birnin, yayin da aka rufe kasuwanni da makarantu da dama.

    Ana sa ran za a gudanar da zanga-zangar da aka tsara a kan shafukan sada zumunta na intanet a manyan garuruwan da suka haɗa da Nairobi da Mombasa da kuma wasu sassan tsakiyar ƙasar Kenya.

  18. Farashin man fetur ya faɗi zuwa matakin da yake kafin yaƙin Iran

    ...

    Asalin hoton, Dallas Morning News via Getty Images

    Farashin man fetur ya faɗi zuwa matakin da ba a taɓa ganin irin sa ba tun kafin yaƙin Iran, yayin da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz ke ci gaba da farfaɗowa sannu a hankali.

    Ɗanyen mai nau'in Brent ya faɗi zuwa ƙasa da dala 72.48, farashin da ya kasance a ranar da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran a ranar 28 ga watan Fabarairu.

    Farashin makamashi ya yi tashin gwauron zabi tun lokacin da Iran ta mayar da martani ga hare-haren ta hanyar rufe mashigar ruwan da ke da matuƙar muhimmanci ga jigilar mai da iskar gas a duniya.

    Farashin danyen man fetur ya ragu matuƙa tun bayan da Amurka da Iran suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a ranar 17 ga watan Yuni wadda ta tanadi wa'adin kwanaki 60 don tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran ɗin da sauran matakan kawo ƙarshen yaƙin.

    Wakilan ɓangarorin biyu sun gana a ƙasar Switzerland a ƙarshen makon da ya gabata domin tattaunawa da niyyar kawo ƙarshen yaƙin, wanda ya sa Amurka ta ɗage wani ɓangare na takunkumin da ta ƙaƙaba wa Iran ɗin.

  19. Girgizar ƙasa ta kashe aƙalla mutum 32 a Venezuela, tare da jikkata 700

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata girgizar ƙasa mai ƙarfi ta afku a ƙasar Venezuela, inda ta kashe aƙalla mutum 32, yayin da wasu 700 kuma suka jikkata ta kuma lalata gine-gine a Caracas babban birnin ƙasar.

    Shaidun gani da ido sun an ji ce girgizar kasar mai ƙarfin maki 7.1 har zuwa makwabciyarta Colombia, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Tun da farko dai Hukumar gargaɗi kan guguwarTsunami ta Amurka ta fitar da sanarwar yiwuwar afkuwar guguwar a Venezuela, da tsibirin Virgin Islands da kuma British Virgin Islands, amma yanzu ta janye gargaɗin.

    Hotunan da wakiliyar BBC Vanessa Silva ta ɗauka, sun nuna yadda masu aikin ceto ke neman waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan wani ginin bene da ya ruguje a yankin arewacin Caracas na San Bernardino.

    Rahotannin da ba a tabbatar ba sun nuna cewa aƙalla mutum ɗaya ya mutu a unguwar.

  20. Assalamu Alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiya

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kamar yadda aka sani za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.