Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 16 ga watan Yuni, 2026.

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • Sadis Buba

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Muslim Muhammad Yusuf da Usman Minjibir

  1. 'A yi taka-tsantsan kan hukuncin kotu game da asalin ɗanƙasa a Filato'

    Caleb Mutfwang

    Asalin hoton, Caleb Mutfwang/X

    Gwamnatin Filato ta yi kira ga al'ummar jihar da su yi taka-tsantsan da kauce wa kalamai ko ɗaukar matakan da za su iya tayar da hankali bayan hukuncin da kotu ta yanke kan batun bayar da takardun shaidar asalin ɗan ƙasa a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

    A cikin wata sanarwa da kwamishinar yaɗa labarai ta jihar, Joyce Lohya Ramnap, ta fitar, gwamnatin ta bayyana damuwarta kan yadda batun "ya haifar da muhawara mai zafi da ka iya haifar da rashin jituwa tsakanin al'ummomin da suka shafe shekaru suna zaman lafiya tare".

    Wata Bahaushiya mai suna Fatima Akawu da aka haifa kuma ta tashi a Jos ce ta shigar da ƙaramar hukumar Jos ta Arewa ƙara bayan da ta buƙaci shaidar zama ƴar Jos ta Arewa aka hana, inda aka aka ba ta takardar shaidar ɗan ƙasa ta wucin-gadi.

    Babbar kotun jihar ta umurci ƙaramar hukumar ta ba ta cikakkiyar takardar shaidar zama ɗan ƙasa (Indigene) cikin kwana 30, inda ta yanke hukuncin cewa "duk wanda aka haifa kuma ya tashi a ƙaramar hukumar yana da haƙƙin samun shaidar".

    Gwamnatin ta bayyana cewa ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, ba ta gamsu da hukuncin kotun ba, inda ta ce tana da haƙƙin ɗaukaka ƙara a kotu ta gaba, bisa tanadin doka.

    "Duk da cewa gwamnati tana girmama haƙƙin ƴan ƙasa na bayyana ra'ayoyinsu kan al'amuran da suka shafi jama'a, tana kira ga kowa da kowa da ya nuna dattaku, sanin ya kamata da taka-tsantsan wajen yin tsokaci kan wannan batu," in ji sanarwar.

    Haka kuma gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta goyi bayan duk wani yunƙuri na amfani da lamarin wajen haifar da ƙiyayya, rarrabuwar kai ko tayar da fitina tsakanin al'ummomi ba. Ta jaddada aniyarta na ci gaba da kare doka, mutunta 'yancin shari'a da samar da yanayin da kowa zai gudanar da harkokinsa cikin lumana.

    Sai dai gwamnatin ta ce, bai dace a taƙaita irin wannan hukunci ga ƙaramar hukumar Jos ta Arewa kaɗai ba.

  2. 'Harin Isra'ila a Lebanon ya kashe mutum huɗu'

    Israel

    Asalin hoton, Getty Images

    Akalla mutum huɗu sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon a ranar Talata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na gwamnati, NNA, da jaridar L'Orient-Le Jour suka ruwaito.

    Rahotannin sun ce an kai hare-haren ne kan motoci uku a wurare daban-daban tsakanin garuruwan Mayfadoun da Shoukin.

    Haka kuma, NNA ta ce wasu mutum huɗu sun jikkata bayan da aka jefa bam a garin Hadatha da ke kudancin Lebanon.

    Sai dai Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya sha bayyana a baya cewa dakarun ƙasarsa ba za su janye daga kudancin Lebanon ba duk da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da Iran.

    Trump dai ya ce bai ji daɗin yadda Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare kan Hezbollah a Lebanon ba.

  3. Sojojin Isra’ila sun tabbatar da kai sabbin hare-hare a Lebanon

    Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Isra’ila sun sanar da cewa sun kai hare-hare da dama a ƙasar Lebanon a yau Talata.

    Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi nasarar kakkaɓo wasu rokoki da aka harba daga kudancin Lebanon, waɗanda ta zargi ƙungiyar Hezbollah da harbawa.

    Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin Isra’ila sun kai hari kan wani wurin harba rokoki da ke kudancin Lebanon, wanda ta ce ana amfani da shi wajen kai hare-hare kan dakarunta.

    A ɗazu Shugaba Donald Trump ya ce bai ji daɗin yadda Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare kan Hezbollah a Lebanon ba, bayan an amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran.

  4. Gwamnan Sokoto ya ƙaddamar da gidajen ƴan gudun hijira

    Sokoto Govt

    Asalin hoton, Sokoto Govt

    Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ƙaddamar da gidaje 100 da aka gina wa ƴan gudun hijira a ƙaramar hukumar Illela.

    Baya ga gidajen, an kuma ƙaddamar da cibiyoyin samar da zaman lafiya da magance ibtila'i, tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin kilowatt 50, da kuma aza harsashin ginin wata babbar kasuwar ƙasa da ƙasa ta Illela.

    Gwamna Aliyu ya sanar da bayar da tallafin naira 500,000 ga kowane ɗaya daga cikin mazauna gidaje 100 da aka gina wa ƴan gudun hijirar domin su samu jari na fara sabuwar rayuwa.

    "Mun gina waɗannan gidaje ne domin samar wa waɗanda suka rasa matsugunansu muhalli mai aminci da dacewa domin su sake gina rayuwarsu. Haka kuma mun kammala shirye-shiryen gina irin waɗannan gidaje a wasu yankunan jihar da matsalar ƴan bindiga ta shafa," in ji shi.

    Sokoto

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, wanda ya ƙaddamar da gidajen ya bayyana cewa: "Gwamnan ya yi abin da ya zarce tsammaninmu. A gaskiya yana ɗaya daga cikin gwamnonin da suka fi nuna ƙwazo a Najeriya. Bayan zaɓensa, ba mu yi tunanin zai kai wannan matakin na aiki ba."

    Shiri da gwamnatin jihar ta aiwatar haɗin gwiwa ne da Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP).

  5. Ba na jin daɗin abin da Isra'ila ke aikatawa - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Donald Trump ya ce bai ji daɗin yadda Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare kan Hezbollah a Lebanon ba, bayan an amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran.

    Trump ya shaida wa manema labarai a wajen taron G7 cewa ya kamata Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya riƙa yin abu na masu hankali.

    Ya ce an kashe mutane da dama a Lebanon, kuma babu buƙatar Isra'ila ta riƙa kai hare-hare kan gidajen farar hula don kawai suna neman wani ɗan Hezbollah.

    "Ban ji daɗin abin da Isra'ila ta yi kan batun Lebanon da Hezbollah ba, ya kamata ace an yi an ƙare a ƙankanin lokaci, amma sai ga shi batun yana ɗaukar lokaci mai tsawo," in ji shi.

    Trump ya ce ya bayyana wa Isra'ila rashin jin daɗinsa a karon farko ne, bayan ta kai hari a Lebanon sa'a biyu gabanin Iran da Amurka su sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi.

  6. 'Yansanda uku sun mutu a wani harin nakiya a Zamfara

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    ‘Yan sanda uku daga sashen kwance bama-bamai (EOD) na rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara sun mutu bayan wani nakiya da aka dasa ya tashi a kan titin Anka zuwa Bagega a yammacin ranar Litinin.

    Rahotanni sun ce jami’an na kan aikin fatattakar ‘yanbindiga ne lokacin da motarsu mai sulke ta taka nakiyar da ake zargin an binne ta ne a hanya, wanda ya yi sanadin mutuwarsu nan take.

    Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa amfani da irin wannan salon wajen kai hari na nuna karin kwarewa da dabarun kungiyoyin ‘yanbindiga, wacce babbar matsala ce.

    Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da rasuwar jami’an, inda ta bayyana sunayensu tare da jinjinawa jarumtarsu, yayin da masana ke gargadin cewa yawaitar irin wadannan hare-hare na nuna sauyin salon dabarun ‘yanbindiga zuwa irin na ‘yan ta’adda.

  7. Yarjejeniyar Amurka da Iran ta jefa Netanyahu cikin mawuyacin halin siyasa

    ....

    Asalin hoton, getty images

    Yarjejeniyar da Amurka da Iran suka cimma domin kawo karshen yaki ta jefa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, cikin wani mawuyacin hali na siyasa, inda ta shafi muhimman ginshikan jagorancinsa.

    A baya, Netanyahu ya gina sunansa a matsayin jagora mai kusanci da Amurka, amma wannan yarjejeniya ta nuna kamar an kau da shi gefe daga manyan shawarwari, lamarin da ya janyo suka daga cikin gida da waje.

    Masu sharhi sun ce wannan na nuna raguwar tasirin Isra’ila a Washington.

    Haka kuma, Netanyahu ya dade yana mai da Iran babban abin da ya fi maida hankali a tsaron Isra’ila, amma yarjejeniyar ta kawo karshen yakin ba tare da cimma dukkan burin Isra’ila ba.

    Wasu na ganin hakan ya sa Iran ta fito da karfi fiye da yadda ake tsammani, yayin da Isra’ila ta kasa cimma burinta.

    A bangaren Lebanon kuwa, matsin lamba daga Amurka da Iran na bukatar a dakatar da hare-haren Hezbollah ya kara jefa Netanyahu cikin rudani, musamman gabanin zabe.

    Wannan ya sanya tambaya kan ko har yanzu zai iya ci gaba da daukar kansa a matsayin “jagoran tsaro” a idon jama’ar Isra’ila.

  8. Wane ne ya ƙirƙiro shekarar Musulunci?

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Talatar nan ɗaya ga watan Muharram a jerin watannin Musulunci 12 da ke amfani da yanayin tafiyar wata, inda watanninta da ke cikinta ke farawa suke kuma ƙarewa daidai da yanayin ɓullowa da kuma ɓacewar wata.

    A wasu jihohin Najeriya da wasu sassan Afirka, hukumomi kan ayyana ranar 1 ga watan Muharram a matsayin ranar hutu domin murna da kuma gudanar da bukukuwan shigar sabuwar shekara.

    To amma abin da jama'a da dama ke neman sani shi ne yasueh aka fara amfani da shekarar ta Musulunci sannan wane ne ya ƙirƙiro ta?

  9. ADC ta yi watsi da hukuncin kotu kan soke rajistar jam'iyyar

    ...

    Asalin hoton, ADC/X

    Jam’iyyar ADC ta yi watsi da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta soke rajistar ta da wasu jam’iyyu huɗu, inda ta bayyana hukuncin a matsayin wani yunkuri na amfani da kotu domin raunana tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.

    Hukuncin, wanda Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke a Abuja, ya bayar da umarnin soke rajistar jam’iyyun ADC, Accord, Action Peoples Party, Action Alliance da Zenith Labour Party, bisa zargin gazawarsu wajen cika wasu sharuɗɗa da dokoki suka tanada, ciki har da samun kaso na ƙuri’u ko nasarar kujera a zaɓe.

    Sai dai jam’iyyar ADC, a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na ƙasa Bolaji Abdullahi ya fitar, ta soki hukuncin, tana mai cewa ya sabawa kundin tsarin mulki da kuma ka’idojin doka.

    Jam’iyyar ta ce hukuncin ya kuma saba da irin matsayin da INEC kanta ta gabatar a baya kan batun soke rajistar jam’iyyun siyasa.

    ADC ta kara da cewa INEC ta bayyana a gaban kotu cewa jam’iyyar ba ta karya wata doka ba, kuma ta cika dukkan sharuddan da ake bukata.

    Haka kuma jam’iyyar ta zargi kotun da karya tsarin shari’a, tana mai cewa an ci gaba da sauraron karar duk da umarnin kotun daukaka kara na dakatar da shari’ar, lamarin da ta ce na iya haifar da rikicin siyasa a kasar.

  10. Gwamnati za ta samar da a babura masu ƙafa uku da ke amfani da lantarki 10,000

    ....

    Asalin hoton, Shettima/X

    Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin samar da a masu kafa uku da ke amfani da lantarki guda 10,000 a watan Agustan 2026 a wani yunkuri na saukaka harkokin sufuri a fadin Najeriya.

    Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa wannan shiri na daga cikin tsare-tsaren gwamnati na inganta harkokin sufuri da kuma tsarin jigilar kayayyaki a kasar.

    Shettima ya bayyana cewa hukumar bunkasa yankin Arewa maso Gabas (NEDC) ce za ta rarraba wadannan babura domin amfani a yankin da sauran sassan kasar.

    Ya kuma ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da fadada wannan shiri zuwa sauran yankunan kasar ta hanyar hukumomin raya yankuna daban-daban.

    Mataimakin shugaban ya kara da cewa tsarin gyaran harkokin sufuri na gwamnatin tarayya ya ta’allaka ne kan yada amfani da iskar gas (CNG) a fadin kasa da inganta tashoshin jiragen ruwa da kuma karfafa tsarin jigilar kayayyaki.

    Ya bayyana cewa wadannan sauye-sauye na da nufin rage kudin sufuri, kara inganta tattalin arziki da kuma kyautata rayuwar masu aikin sufuri a Najeriya.

  11. Injiniya Nuhu Aminu ya zama shugaban ƙungiyar ɗaliban Najeriya a ƙasashen waje

    ..

    Asalin hoton, Engineer Nuhu Aminu Nuhu

    Ɗan arewacin Najeriya, Injiniya Nuhu Aminu Nuhu ya zama sabon shugaban ƙungiyar ɗaliban Najeriya da ke jkaratu a ƙasashen waje bayan zaɓe da aka gudanar a ranakun Lahadi da Litinin ɗin nan.

    Ɗalibai ƴan Najeriya da ke ƙasashe daban-daban ne suka gudanar da zaɓen kai tsaye ta intane.

    Ƙasashe 23 ne aka tantance su kaɗa ƙuri'a daga ƙasashen 25 da ɗaliban ke karatu ciki, inda kuma Injinya Nuhu Aminu Nuhu ya lashe ƙuri'un 23 baki ɗaya.

    Wannan dai shi ne karon farko da wani ɗan arewacin Najeriya ya samu irin wannan dama.

    Injiniya Nuhu Aminu Nuhu yana karatun digiri na uku a fannin injiyan gine-gine a jami'ar Beijing Jationg University da ke ƙasar China.

    Injiniya Aminu ɗan asalin ƙaramar hukumar Bagwai ne a jihar Kano.

  12. Jihar Sokoto ta ayyana yau Talata ranar hutun sabuwar shekarar Musulunci

    ....

    Asalin hoton, Ahmed Aliyu/x

    Gwamnatin Jihar Sokoto ta ayyana ranar Talata, 16 ga watan Yuni 2026, a matsayin ranar hutu a hukumance domin bikin fara sabuwar shekarar Musulunci 1 ga watan Muharram ta 1448 bayan hijira.

    Hakan na cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar domin bai wa al’ummar Musulmi damar gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar cikin natsuwa.

    Gwamna Ahmed Aliyu ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya, musamman ganin yadda matsalolin tsaro ke addabar wasu sassan jihar da ma kasa baki daya.

    Ya bayyana rashin tsaro a matsayin babbar barazana ga ci gaban Najeriya, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan kowa wajen shawo kan matsalar.

    Gwamnan ya kuma ce gwamnatocin tarayya da jihohi na ci gaba da kokari wajen tallafa wa hukumomin tsaro don yakar ta’addanci da sauran miyagun laifuka.

    Gwamna ya kuma yi kira ga Musulmi da su yi nazari a kan rayuwarsu tare da gyara kura-kuran da suka gabata a sabuwar shekarar 1448 AH.

  13. Babu wanda zai iya samar da tsaro nan take a Zamfara - Gwamna Dauda

    Bayanan bidiyo, Gwamnan jihar Zamfara Dauda Dare
  14. Duk wani sabon harin Isra'ila a Lebanon, saɓa yarjejeniya ne - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya gargadi cewa duk wani sabon hari da Isra’ila za ta kai kan Lebanon ko kuma ci gaba da mamaye yankuna a kasar, zai zama saɓawa yarjejeniyar da aka cimma da Amurka ne.

    Ya bayyana cewa Iran na kallon wannan yarjejeniya a matsayin dangantaka tsakanin Iran da kungiyar Hezbollah a gefe guda, da kuma Amurka da Isra’ila a gefe guda.

    Araqchi ya ce duk wani mataki da Isra’ila ta dauka sabanin wannan fahimta zai iya kara dagula al’amura a yankin, yana mai jaddada cewa Iran da abokan kawancenta za su dauki al’amarin da muhimmanci.

    Wannan gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da tashin hankali ke kara kamari a yankin gabas ta tsakiya.

    Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila ta sake kai wasu hare-hare a kudancin Lebanon, yayin da kungiyar Hezbollah ta sanar da cewa ta kaddamar da martani kan sojojin Isra’ila.

    Hakan ya kara tayar da hankulan jama’a kan yiwuwar barkewar sabon rikici a yankin.

    A nasa bangaren, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jaddada cewa sojojin kasarsa za su ci gaba da kai hare-hare a kudancin Lebanon, yana mai nuni da cewa Isra’ila ba za ta janye daga wadannan wurare ba duk da matsin lamba daga kasashen duniya.

  15. Sarkin Musulmi ya ayyana Talata 16 ga Yuni a matsayin 1 ga watan Muharram

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ayyana ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2026, a matsayin 1 ga watan Muharram 1448, sabuwar shekarar Musulunci.

    Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Majalisar Masarautar Sokoto.

    Sanarwar, wadda Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin harkokin addini na majalisar masarautar ya fitar ta bayyana cewa wannan hukunci ya biyo bayan ganin jinjirin watan Muharram da kuma tabbatar da shi bisa ka’idojin addinin Musulunci.

    Watan Muharram shi ne farkon sabuwar kalandar Musulunci, wanda ke nuna fara sabuwar shekarar Musulunci.

    Haka kuma yana cikin watanni masu tsarki a Musulunci, kuma yana da muhimmanci wajen tunatar da al’ummar Musulmi game da hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina.

    Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmi a fadin Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, hadin kai da cigaban kasa, tare da karfafa imani da ayyukan alheri a sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH.

  16. An ji ƙarar fashewa a mashigar Hormuz da Qeshm

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    An ji ƙarar wasu fashe-fashe guda uku a kudancin tsibirin Qeshm da kuma mashigar Hormuz a daren jiya kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito.

    Jaridar ta ce fashe-fashen biyu na farko sun faru ne a daren Litinin, 15 ga watan Yuni, yayin da na uku ya faru da sanyin safiyar Talata, 16 ga Yuni.

    A cewar wakilin Mehr, fashe-fashen sun faru ne a cikin mashigar Hormuz, kuma rahotannin farko sun nuna hakan na iya faruwa ne domin sarrafa zirga‑zirgar jiragen ruwa a yankin.

    Sai dai har yanzu babu wata hukuma ta gwamnati a Iran da ta fitar da cikakken bayani kan lamarin, ciki har da rundunar juyin juya halin Iran IRGC ko hukumomin yankin.

    A wasu rahotanni makamantan haka, an taba alakanta karar fashewa a yankin da harbin gargadi ga jiragen ruwa da ke kokarin wucewa ba tare da izini ba, a lokacin da ake tsaurara matakan tsaro a mashigar Hormuz.

  17. Mutum takwas sun mutu a hatsarin jirgin yaƙin Amurka

    ....

    Asalin hoton, CBS

    Mutane takwas sun mutu bayan jirgin yaƙin Amurka kirar B‑52 ya yi hatsari jim kaɗan bayan tashinsa daga wani sansanin soji da ke arewacin Los Angeles a ranar Litinin.

    Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya tashi da misalin ƙarfe 11:20 na safe a lokacin da yake kan wani gwaji na yau da kullum, kafin ya faɗi ya kama da wuta.

    Hatsarin ya haddasa wata babbar guguwar hayaki wadda aka hango daga nesa yana tashi.

    Kanar James Hayes ya tabbatar da mutuwar duka mutanen da ke cikin jirgin, yana mai cewa:

    “Mun yi rashin ‘yan Amurka takwas masu muhimmanci,” inda ya ƙara da cewa hatsarin “ba zai yiwu a tsira ba.”

    Jami’an sansanin Edwards Air Force sun ce binciken farko ya nuna cewa ba za a iya kaucewa hatsarin ba ko ceto wasu ba, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano abin da ya haddasa shi.

    Jami’ai sun ƙara da cewa hatsarin ya faru ne a cikin yankin filin jirgin na sansanin, kuma an dakatar da zirga-zirgar jirage na ɗan lokaci domin gudanar da bincike da ayyukan ceto

  18. Trump ya musanta rahoton biyan Iran dala miliyan 300

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta rahotannin da ke cewa kasarsa za ta biya Iran dala miliyan 300, inda ya bayyana hakan a matsayin “labarin ƙarya” a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

    Trump ya jaddada cewa Iran ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, yana mai cewa yarjejeniyar da aka cimma tana da nufin hana hakan.

    Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana a wata hira da manema labarai cewa Iran na iya samun fa’idodin tattalin arziki da suka kai biliyoyin daloli idan ta cika sharuddan da ke cikin yarjejeniyar.

    Sai dai ya ƙara da cewa akwai wasu muhimman sharuɗɗa da har yanzu ake tattaunawa a kai, kuma za a fitar da cikakken rubutun yarjejeniyar nan gaba.

    A gefen Iran kuwa, kwamandan rundunar Quds juyin juya halin Iran IRGC, Esmail Qaani, ya bayyana cewa sakamakon yarjejeniyar ya samo asali ne daga “tsayin daka” da ƙasar ta yi a yayin rikicin.

  19. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa barkanmu da ganin safiyar yau Talata

    A wannan shafin namu na kai tsaye, za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.