Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 15/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Laraba 15 ga watan Oktoban 2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima
  • Dattijuwa
  • Pantami
  • Mai zane
  • Atiku
  • Sanata BARAU da Hon Abba
  • Hoton Jirgi
  • Sheikh Daurawa
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar da Nabeela Mukhtar Uba

  1. An bude sabuwar gada tsakanin China da Koriya ta Arewa

    .
    Bayanan hoto, Gadar New Yalu River Bridge tana da tsawon kilomita 3 (mil 1.9), tana haɗa birnin Dandong da ke kan iyakar China da birnin Sinuiju na Koriya ta Arewa.

    Kafafen yaɗa labaran gwamnatin China sun rawaito cewa, an buɗe wata gada da aka daɗe ana jira wadda ta haɗa ƙasar da Koriya ta Arewa, a daidai lokacin da hulɗar kasuwanci ke ƙara ingancin tsakaninsu.

    China ita ce babbar ƙasar da Koriya ta Arewa ke kasuwanci da ita, kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen taimaka mata ta fuskanci takunkuman da ƙasashen yamma suka ƙaƙaba mata kan shirin ta na inganta makaman nukiliya.

    Gadar New Yalu River Bridge tana da tsawon kilomita 3 (mil 1.9), tana haɗa birnin Dandong da ke kan iyakar China da birnin Sinuiju na Koriya ta Arewa. Ana sa ran za ta zama babbar hanyar ƙasa da ake amfani da ita wajen safarar kayayyaki da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

    An fara shirin ƙaddamar da gadar ne tun shekarar 2014, amma aka dakatar da shi na wani lokaci, bayan Koriya ta Arewa ta dakatar da aikin gina hanyoyi da cibiyoyin ƙwastam da za su haɗu da gadar. A lokacin kuma dangantakarta da Beijing ta yi tsami.

    A wani saƙon bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet a ranar Alhamis, Firaministan China Li Qiang ya bayyana cewa gadar ta zama “sabon abin tarihi da ke nuna tsohuwar abota tsakanin China da Koriya ta Arewa”, sannan ya ce ƙasashen biyu sun “buɗe sabon babi a dangantakarsu ta ƙawance da haɗin gwiwa.”

  2. 'ISWAP sun kashe sojoji 15 a harin kwanton ɓauna kan sansanin soji a Borno'

    .
    Bayanan hoto, Masu tada ƙayar baya da iƙirarin jihadi sun jima su na addabar al'ummomin yankin arewa maso gabashin Najeriya

    Ana fargabar an kashe sojojin Najeriya sama da 15 da wasu matasa biyar na rundunar sa-kai ta Civilian JTF, a wani harin kwanton ɓauna da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kai sansanin sojoji da ke ƙaramar hukumar Guzamala a jihar Borno da ke arewa yammacin Najeriya,

    Wata majiya ta shaidawa BBC cewa harin ya faru ne tsakanin daren Talata zuwa Laraba da ta gabata, inda aka shafe sama da sa'o'i biyu ana musayar wuta tsakanin mayaƙan da dakarun sojin Najeriya.

    Majiyar ta ce bayan musayar wutar, wasu daga cikin sojojin sun tsere daga sansaninsu zuwa garin Monguno, mai nisan kusan kilomita 18 daga ƙauyen Mairari.

    Kawo yanzu ba a san adadin sojojin da suka ɓace bayan harin ba, kuma ba a tabbatar da halin da suke ciki ba bayan sun tsere cikin daji domin tsira da rayukansu.

    Wani soja da ya nemi a sakaya sunan shi, saboda ba shi da izinin yin magana a hukumance kan lamarin, ya ce harin ya faru ne a lokacin da al'ummar yankin suka fara samun ƙwarin gwiwar zaman lafiya na dawowa.

    Ya ce yana cikin sojojin da suka tsira daga harin, amma bai bayyana takamaiman adadin sojojin da ake tunanin suna sansanin a lokacin harin ba, ko kuma yawan waɗanda har yanzu ba a san inda suke ba.

  3. Hukumar Kwastam ta kama kayan miliyoyin Nairori a Zamfara da Sokoto

    .
    Bayanan hoto, Hukumar ƙwastam ta kama kayan miliyoyin nairori a jihohin Sokoto da Zamfara

    Hukumar Ƙwastam ta Najeriya ta kama kayan da akai fasa ƙwaurinsu da darajarsu ta haraji ta kai Naira miliyan 721.9, ciki har da tufafin gwanjo, da taba sigari da magungunan da ba su da rajista.

    Mukaddashin Kwanturola na Kwastam mai kula da yankin Zamfara da Sokoto Haliru Isah Abdullahi, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Sakkwato.

    Abdullahi ya ce an samu nasarar kama kayayyakin ne sakamakon ƙarfafa ayyukan yaƙi da fasa ƙwauri da nufin kare tattalin arzikin ƙasa, tabbatar da tsaron iyakoki da kuma hana yaɗuwar haramtattun kayayyaki a cikin ƙasar.

    Kayayyakin da aka kama sun haɗa da: Motar dakon kaya kirar DAF da aka yi amfani da ita, da kunshi 599 na tufafin gwanjo, da manyan buhu 7 na jakunkunan mata, da manyan katan ɗin taba sigari 43, da sauransu.

    Ya jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da ɗaukar matakai masu tsauri domin daƙile fasa ƙwauri da kare lafiyar jama'a da tattalin arzikin Najeriya.

  4. Hari ta sama ya hallaka yara biyar a jihar Kordofan

    .
    Bayanan hoto, Ƴan gudun hijirar Sudan

    Rahotanni daga Sudan sun ce aƙalla yara biyar ne suka mutu sakamakon wani hari ta sama a jihar North Kordofan.

    Ƙungiyar lauyoyin gaggawa, wadda ke sa ido kan cin zarafi da tashin hankali da ake yi wa fararen hula, ta ce wani jirgin sama na rundunar sojin Sudan ƙirar Antonov ya kai hari kan wani gida da ke ƙauyen Abu Zaeima.

    Kawo yanzu rundunar sojin Sudan ba ta yi karin bayani ko martani kan wannan rahoton ba.

    A baya-bayan nan, faɗa tsakanin dakarun gwamnati da ƙungiyar ƴan tawayen RSF ya ƙara tsananta a yankin Kordofan mai matuƙar muhimmancin, da ke yammacin ƙasar Sudan.

  5. Saudiyya ta zargi Iran taimakon Houthi a yaƙin da suke yi da kasar

    .
    Bayanan hoto, A baya-bayan nan rikici tsakanin Saudiyya da Yemen ya ƙara munana

    Wani jami'i a Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ya zargi Iran da ƙarfafa mayakan Houthi na Yemen su ci gaba da kai sabbin hare-hare kan Saudiyya.

    Mataimakin ministan harkokin wajen Saudiyya mai kula da hulɗa da jama’a Raed Karimli ne bayyana hakan yayin taron manema labarai ta intanet a ranar Alhamis.

    Ya ƙara da cewa; “Iran na ci gaba da bai wa mayaƙan Houthi makamai, da horon soji da goyon baya, abin da ya saɓa wa kudurorin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya. Mun yi imanin cewa Iran ce ke karfafa ƙaruwar hare-haren da yan Houthi ke kai wa ƙasarmu.”

    Jami’in na Saudiyya ya ce har yanzu ƙasarsa tana da alaƙa da Iran, amma ya nuna cewa Tehran ba ta da aniyar sasantawa domin magance matsalolin da ke tsakaninsu.

    Mista Karimli ya kuma zargi mayaƙan Houthi da ƙin shiga tattaunawar sulhu da Saudiyya ta gabatar a ƙasar Oman a makonnin baya-bayan nan, yayin da faɗace-faɗacen ke ƙara tsananta.

    “A farkon wannan lokaci da tashin hankali ya fara ƙaruwa, mun nemi a gudanar da wani taro a Muscat, babban birnin Oman, amma sun ƙi amincewa,” in ji shi.

  6. Ƴan bindiga sun kashe jami'in hukumar shige da ficen Najeriya

    .
    Bayanan hoto, Ƴan bindiga na kai hari kan jami'an tsaron Najeriya

    Ana zargin wasu ƴan bindiga sun kashe wani jami'in Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya, yayin wani sintiri na yau da kullum a yankin Tunga Taya zuwa Woro da ke Jihar Neja, yayin da wani abokin aikinsa ya samu munanan raunuka.

    Jami'in Hulɗa da Jama'a na Hukumar NIS, kuma Mataimakin ƙwanturola hukumar, Akinsola Akinlabi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

    Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne yayin da jami'an ke gudanar da ayyukansu na sa ido da sintiri a yankin, inda maharan da ake zargin ƴan bindiga ne suka kai musu hari.

    Harin ya yi sanadin mutuwar jami'i ɗaya a wurin, yayin da ɗayan ya ke ƙwance asibiti ya na karɓar magani.

    Hukumar ta yi Allah-wadai da harin tare da jinjina wa jami'in da ya rasa ransa yayin gudanar da aikinsa na kare iyakoki da tabbatar da tsaron ƙasa.

  7. Birtaniya na barazanar hana ƴan Eritrea bizar shiga ƙasarta

    .
    Bayanan hoto, A duk shekara ɗaruruwan bakin hauren Eritrea ne ke shiga Birtaniya ta ɓarauniyar hanya

    Gwamnatin Birtaniya ta yi gargaɗi Eritrea kan ƴan ƙasarta ka iya fuskantar rashin biza idan gwamnatin ba ta amince da karɓar ƙarin baƙin haure da suka shiga Birtaniya ba bisa ƙa'ida ba ta ƙananan ƙwale-ƙwale.

    Ministar harkokin cikin gida, Shabana Mahmood, ta ce an bai wa Eritrea dama sau ba adadi, domin ta bi buƙatar Birtaniya, amma har yanzu ba ta yi abin da ake buƙata ba.

    A bara, wasu ƙasashen Afirka ma sun fuskanci irin wannan barazanar hana ba da biza kafin daga bisani su amince da haɗin gwiwa da gwamnatin Birtaniya.

    Dubban mutane daga Eritrea na tserewa ƙasarsu a kowace shekara domin neman mafaka a ƙasashen waje. Suna korafin cewa ana tilasta musu aikin soja na tsawon lokaci ba tare dazaɓi ba, da take haƙƙin farar hula da matsin tattalin arziki.

  8. Shugaba Tiani ya amince da kafa hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta Nijar

    Tiani Nijar

    Shugaban Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya saka hannu kan wata doka da za ta kafa hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa.

    Dokar wadde ke da alhakin sanya Ido kan dukkan batutuwan da suka shafi kare haƙƙin ɗan adam, da bai wa gwamnati shawarwari, da kula da yanayin rayuwar mutanen da ake tsare da su, da faɗakar da al'umma kan batutuwan da suka shafi kundin tsarin mulki a bisa manufofin sake gina kasa da kuma kula da ƴancin mata da yara da nakasassu.

    Dokar da Shugaban majalisar mulkin sojan ƙasar ya sanyawa hannu ta fayyace fannonin da cibiyar za ta gudanar da ayyukanta a ciki.

    Cibiyar za ta tabbatar da inganta haƙƙin ɗan adam a faɗin Nijar.

    Dokar ta kuma tanadi cewa, ya zama wajibi ga wannan cibiya ta samar da taimakon shari'a, ko kuma ta sauƙaƙe samun sa, ga waɗanda aka take wa haƙƙoƙin ɗan adam.

    Sai dai wasu masu sharhi a ƙasar kamar Mahamadou Aboubacar na ganin dokar ta zo a makare.

    Yayin da Dr Yahaya Badamasi wani dan rajin kare haƙƙin bil adama a ƙasar ya yi fatan ganin an sakarwa wannan hukuma mara tayi aiki kamar yadda aka bayyana a rubuce.

  9. Gwamnatin Zamfara za ta siya wa ƴan jihar hannayen jarin Dangote

    dauda lawal

    Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da wani shiri na siya wa ƴan jihar su 36,176 hannayen jari a Kamfanin Dangote domin tallafa musu shiga hadar hadar kuɗi na zamani da kuma bunƙasa tattalin arziki.

    A cewar Ma'aikatar bayar da Agaji ta jihar, an tsara shirin ne domin bai wa al'umma damar shiga harkokin zuba jari tare da amfana daga ɓangaren kasuwanci na ƙasar.

    A ƙarƙashin shirin, ana sa ran kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai samu kusan hannayen jari 20 na Kamfanin Dangote, kamar yadda jaridar Channels ta ruwaito.

    Ma'aikatar ta ce Kwamishinan Harkokin Agaji, Salisu Musa Tsafe Kainuwa, ne zai jagoranci aiwatar da shirin.

    Ta ƙara da cewa za a zaɓo waɗanda za su amfana daga dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar, inda kowace ƙaramar hukuma 13 za ta samu mutum 2,261, yayin da Gusau, babban birnin jihar, za ta samu mutum 4,522.

    Gwamnatin jihar ta kuma ce shirin zai haɗa da masu buƙata ta musamman domin tabbatar da tafiya da kowa.

  10. Me ya kai gwamnonin hamayya cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu?

    Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jawo hankalin 'yan siyasa da masu sharhi bayan da jam'iyyar APC ta fitar da sabon tsarin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na 2027, inda aka bai wa wasu manyan 'yan siyasar da ba mambobin APC ba muƙamai masu muhimmanci.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  11. Ƙasashen Gulf da Tarayyar Turai sun ɗage taron su a Saudiyya saboda hare hare

    tutar saudiyya

    An ɗage wani taro tsakanin ƙasashen yankin Gulf da Tarayyar Turai wanda aka shirya gudanarwa a Saudiyya mako mai zuwa, sakamakon ci gaba da hare-haren da mayaƙan Houthi na Yemen ke kai wa ƙasar.

    Rahotanni sun ce yanayin tsaro a Saudiyya ya kara tsananta bayan mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran sun kai hare-hare uku masu muni kan filin jirgin sama na Riyadh a makon da ya gabata.

    A ranar Laraba kuma, hukumomin Saudiyya sun sanar da ɗage wasu manyan wasannin, ciki har da gasar ƙwallon tennis da fitattun 'yan wasa Novak Djokovic da Carlos Alcaraz za su halarta, da kuma wasu wasannin ƙwallon ƙafa.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta suka ce sun kakkabo wani makami mai linzami da aka harba yankin Madina.

    Sai dai kungiyar Houthi ta musanta kai harin.

  12. Ba mu hana ɗalibai masu niƙabi shiga makaranta ba - Kwalejin shari'a ta Aminu Kano

    logo

    Mahukuntan Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da koyon Shari'a ta Aminu Kano (AKCILS) sun musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa makarantar na hana ɗalibai mata masu sanya niƙabi shiga harabarta.

    A cikin wata sanarwa da kwalejin ta fitar, ta ce zargin ba gaskiya ba ne, inda ta ce abin da ake yi shi ne binciken tsaro ga ɗalibai da ma'aikata gaba ɗaya, domin tabbatar da an hana shigar da abubuwan da za su iya zama barazana ga tsaro da tarbiyyar ɗalibai.

    Mahukuntan makarantar sun ce ɗalibai mata masu sanya niƙabi ana buƙatarsu ne kawai su bayyana fuskokinsu a wurin binciken tsaro domin tabbatar da ko su wane ne, sannan a binciki jakunkunansu kafin a ba su damar shiga harabar makarantar.

    Sanarwar ta jaddada cewa ba a tilasta musu cire niƙabinsu ko cin zarafinsu ba.

    Kwalejin ta kuma ce babu wata ɗaliba ko ma'aikaciya da aka taɓa hana shiga saboda sanya hijabi ko niƙabi, tana mai zargin masu yaɗa jita-jitar da yin hakan ne domin wasu muradunsu na kashin kai da kuma haddasa ruɗani a cikin al'ummar Kano.

    Makarantar ta kuma ce a shekarar 2014, an samu wata barazanar tsaro lokacin da jami'an tsaron kwalejin suka hana wata mata da suke da shakku a kanta makarantar, Inda daga baya ta isa ƙofar makwabciyar makarantar Kano State Polytechnic ta tayar da bam.

  13. Mayaƙan Houthi sun musanta kai hari Madina

    madina

    Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta musanta rahotannin da ke cewa ta kai hari kan yankin Madina da ke Saudiyya a ranar Alhamis.

    Wannan na zuwa ne bayan da Saudiyya ta sanar cewa jami'anta sun samu nasarar "kakkabo tare da lalata" wani makami mai linzami da aka harba zuwa birnin Madina, daya daga cikin wurare masu tsarki a addinin Musulunci.

    Kakakin rundunar sojin Houthi, Yahya Saree, ya wallafa a shafin sada zumunta na X cewa rundunar ba ta kai wani hari kan kasar Saudiyya a ranar ba.

    Ya kuma ce iƙirarin da Saudiyya ta yi cewa an kai hari kan Madina karya ce tsagwaronta."

  14. Firaministan Albaniya ya dage cewa ba zai ajiye aiki ba duk da zanga zangar neman ya sauka

    firaminstan Albania

    Firaministan Albaniya, Edi Rama, ya dage cewa ba zai yi murabus ba duk da ci gaba da zanga-zangar ɗalibai da ta rikiɗe zuwa tashin hankali a wasu sassan ƙasar.

    A ranar Laraba ne dubban ɗalibai suka fito zanga-zanga a babban birnin ƙasar, Tirana, inda suka banka wa wani ginin gwamnati da bankuna biyu wuta tare da neman Mista Rama ya sauka daga mulki.

    'Yan sanda sun yi amfani da motocin feshin ruwa da kuma hayaƙi mai sanya hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar bayan tarzomar ta ɓarke.

    Rahotanni sun ce an sake gudanar da wata zanga-zanga a ranar Alhamis, yayin da masu zanga-zangar ke ci gaba da matsa lamba kan gwamnati.

    Firaminista Rama ya zargi jam'iyyun adawa da shirya zanga-zangar, amma masu zanga-zangar sun ce fushinsu ya samo asali ne daga mummunan yanayin jami'o'i, ƙarancin damar samun aikin yi ga matasa da kuma abin da suka bayyana a matsayin cin hanci da rashawa da ya yi kamari a ƙasar.

  15. Ukraine ta kai harin ramuwa kan matatar man Rasha

    Ukraine ta kai hari kan ɗaya daga cikin manyan matatun mai na Rasha, sa'o'i kaɗan bayan da Shugaba Zelensky ya sanar da cewa ƙasarsa za ta ci gaba da kai hare-hare.

    Shugaba Zelensky ya zargi Moscow da ƙin mutunta yarjejeniyar dakatar da hare-hare kan cibiyoyin samar da makamashi.

    Gwamnan yankin Ryazan na Rasha ya ce wani gagarumin hari da jiragen marasa matuƙa na Ukraine suka kai ya haddasa gobara a matatar man da ke yankin.

    A ranar Lahadi ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta kan hare haren da ɓangarorin biyu ke kai wa cibiyoyin samar da makamshi.

    Sai dai Ukraine ta ce harin da ta kai martani ne ga abin da ta bayyana a matsayin keta yarjejeniyar da Rasha ke yi.

  16. Adadin yaran da suka mutu a Pakistan bayan ruftawar rufin makaranta ya kai 33

    makarantar da ta rushe

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon ruftawar rufin wata makaranta a birnin Peshawar na Pakistan ya kai 34, a cewar sabbin alkaluman da hukumomi suka fitar.

    Asibitin Lady Reading ya sanar da mutuwar mutane 33, ciki har da yara 32 da wani malami guda, yayin da Asibitin Naseerullah Khan Babar Memorial ya tabbatar da mutuwar wani yaro guda ɗaya.

    Wani babban jami'in 'yan sanda a Peshawar, Farhan Ahmed, ya shaida wa BBC cewa ginin makarantar da ke unguwar Dir Colony yana cikin wani mummunan yanayi na lalacewa tun kafin aukuwar hatsarin.

    Ƴan sandan sun kuma tabbatar da kama mai makarantar.

    makarantar da ta rushe
    makarantar da ta rushe
  17. Remi Tinubu ta buƙaci a ƙara zuba jari wajen tallafa wa matan karkara don bunƙasa noma

    Remi Tinubu

    Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira da a ƙara zuba jari wajen tallafa wa mata mazauna karkara domin bunƙasa noma, samar da abinci da bunƙasar tattalin arziki.

    A cikin saƙonta na ranar Matan Karkara Ta Duniya ta shekarar 2026, wadda ake bikin ta a ranar 15 ga watan Oktoba, ta yabawa jajircewa da gudunmawar da mata a karkara ke bayarwa wajen ci gaban al'ummomi da ƙasashe.

    Ta ce bikin bana na da muhimmanci sosai domin ya zo ne a cikin Shekarar Manoma Mata ta Duniya, lamarin da ke ƙara jawo hankali kan muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen ɗorewar tsarin samar da abinci da kuma tattalin arzikin karkara.

    Sanata Oluremi Tinubu ta buƙaci a ƙara samar wa mata a karkara damar mallakar ƙasa, samun rance, horaswa samun fasaha da kuma hanyoyin kasuwanci domin inganta rayuwarsu da ayyukansu.

    Ta ce idan aka bai wa mata a karkara dama, iyalai za su amfana, al'ummomi kuma za su bunƙasa, sannan ƙasashe za su ƙara samun ci gaba da ƙarfi.

  18. Najeriya ta zama mamba a majalisar kare haƙƙin ɗan adam ta MDD

    MDD

    An zaɓi Najeriya a matsayin mamba a Majalisar Kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHRC) na wa'adin 2027 zuwa 2029, bayan ta samu kuri'u 172 cikin kuri'u 181 da aka kaɗa a Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya.

    Sauran ƙasashen da aka zaɓa tare da Najeriya sun haɗa da Brazil, Burundi, Jamhuriyar Dominica, Jamus, Ghana, Ireland, Japan, Jordan, Kuwait, Nepal, Moldova, Ukraine, Uruguay da Zambia.

    Kasancewa mamba a majalisar zai bai wa Najeriya damar shiga tattaunawar ƙasa da ƙasa da ta shafi kare haƙƙin bil'adama, da bayar da gudunmawa wajen yanke shawara.

    Majalisar Kare Hakkin Ɗan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya na da alhakin ƙarfafawa da kare haƙƙin bil'adama a faɗin duniya.

    Haka kuma tana magance matsalolin take hakkin dan adam, da bayar da shawarwarin yadda za a magance cin zarafi da kuma bibiyar yadda ƙasashe mambobin MDD ke mutunta haƙƙin bil'adama.

    Najeriya ta ce zaɓenta da aka yi na nuna cewa duniya ta shaida irin sadaukarwar da ta ke yi wajen ƙarfafa kare haƙƙin biladama.

  19. Gwamnatin Trump ce ke kawo cikas ga yadda Ukraine ke amfani da makaman intanet - Elon Musk

    Elon Musk ya ce mai yiwuwa gwamnatin Donald Trump ce ta sanya takunkumin da ya kawo cikas ga yadda Ukraine ke amfani da makaman intanet na tauraron ɗan adam na Starlink, lamarin da ya shafi ƙarfin Kyiv na daƙile hare-haren Rasha.

    Mamallakin kamfanin SpaceX, ya ce duk wani mataki na taƙaita amfani da tsarin sadarwar tauraron ɗan adam na kamfaninsa da ake kira Starshield, wanda aka ƙera domin ayyukan soji, hukuncin sojin Amurka ne, kuma a ƙarshe na Shugaba Donald Trump.

    An ƙaƙaba takunkumin ba tare da wani gargaɗi ba a daren Talata, amma daga bisani an sassauta wani ɓangare na takunkumin.

  20. Aƙalla yara 27 sun mutu bayan rufin wata makaranta ya rufta a Pakistan

    mutane a makarantar da rufi ya rushe

    Aƙalla yara 27 da kuma wani malami guda ne suka mutu bayan rufin wata makaranta ya rufta a birnin Peshawar da ke Pakistan, a cewar ma'aikatan ceto.

    Rahotanni sun ce gomman mutane kuma sun samu raunuka.

    Masu aikin ceto na ci gaba da ƙoƙarin tono ƙarin mutanen da suka maƙale a ƙarkashin ɓaraguzan ginin makarantar Iqra mai zaman kanta, inda hatsarin ya auku.

    Har yanzu dai ba a gano musabbabin abin da ya faru.

    Rahotannin farko sun nuna cewa yaran na cikin azuzuwansu ne a lokacin da rufin ya rufta.