Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 20/09/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. 'Ana samun ƙaruwar miyagun ƙwayoyi a Scotland'

    Hukumar kula da magunguna ta nahiyar Turai ta bayyana cewa, ana ci gaba da samun bullar sabbin miyagun kwayoyi masu matukar karfi a Scotland, lamarin da ke kawo cikas ga kokarin rage yawan mace-macen da ke da alaka da ta'ammali da miyagun kwayoyi.

    Hukumar ta ce an samu karuwar yaduwar wasu nau'ukan kwayoyi cikin a Scotland, wadanda karfinsu zai iya ninka na hodar iblis kusan sau dari.

    Wakilin BBC ya ce Scotland ce ƙasar da ta fi samun yawan mace-mace masu alaka da miyagun ƙwayoyi a Turai - kuma masana kimiyya da ma'aikatan agaji da 'yan sanda sun ce kwararar sabbin kwayoyi na ƙara ta'azzara lamarin.

  2. Dole Amurka ta kasance a gaban China a fasahar AI - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai kafa hukumar kula da fasahar AI, sannan ya naɗa sabon mai ba da shawara kan harkokin da suka shafi fasahar don daidaita ɓangaren.

    A saƙon da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya ce ba zai hana ci gaban fasahar AI ba, yana mai jaddada cewa dole ne Amurka ta ci gaba da shigewa gaban China a bunƙasa fasahar.

    Wannan matakin ya biyo bayan damuwar da shugabannin masana'antar da ma'aikata da dama ke nunawa cewa fasahar AI barazana ce ga bil'adama.

    Wannnan naɗi dai shi zai zama na biyu da Shugaba Trump zai yi - bayan ɗan kasuwa David Sacks ya sauka daga irin wannan muƙamin a watan Maris.

  3. Iran ta sake aika sharuɗɗan kawo ƙarshen yaƙi ga Amurka

    Mohammad Baqer Qalibaf ya soki masu ra'ayin da ke ƙoƙarin jefa ƙasar cikin “yaƙin da babu raar ƙarewa.” Sannan ya kuma tabbatar da cewa Iran ta aika da saƙonni da kuma sharuɗanta ga Amurka ta hannun masu shiga tsakani.

    A wani jawabi gabanin zaman majalisar dokokin Iran, shugaban majalisar ya ce wasu “suna magana ne kan yaƙi amma ba su da wani tsari ko hanyar da za a kawo ƙarshensa.”

    Ya ce irin wannan ra'ayi, ta hanyar ƙin amincewa da duk wata mu'amala ko diflomasiyya ba tare da yin la'akari da yiwuwar abubuwan da za su iya faruwa ba, “a zahiri yana jefa ƙasar cikin tsananin yaƙi da ba shi da iyaka.”

    “Dole ne mu yi yaƙi, amma a gefe kuma mu riƙa shiga tattaunawa,” in ji shi.

    Mista Qalibaf ya kuma jaddada cewa: “An isar da saƙonni tare da bayyana sharuɗɗanmu ga ɗaya ɓangaren ta hannun masu shiga tsakani.”

    Ya ce matuƙar ba a cika sharuɗɗan da Iran ta gindaya ba, “ba za a koma kan tsarin shawarwarin da aka yi a baya ba, kuma ba za a bude mashigar Hormuz ba.”

    A jiya, Mohsen Rezaei, sakataren Majalisar Tsaron Iran, ya sanar da cewa Tehran ta isar da sharuɗɗunta na tattaunawa ga Amurka ta hannun masu shiga tsakani daga Qatar da Pakistan.

    Ya ce yanzu Iran na “jiran martanin Shugaba Trump.”

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya.

    Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo da kuma yin muhawara.

    Ku kasance tare da mu.