Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 29 ga watan Yunin 2026.

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • Sadis Buba

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Muslim Muhammad Yusuf da Haruna Kakangi

  1. Venezuela za ta kafa sansanonin wucin-gadi ga waɗanda girgizar ƙasa ta shafa

    Venezuela

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabar riƙon ƙwarya ta Venezuela, Delcy Rodríguez, ta ce gwamnati za ta kafa sansanonin wucin-gadi domin ba da mafaka ga mutanen da gidajensu suka lalace sakamakon girgizar ƙasar da ta afku a makon da ya gabata.

    Ta ce kwamitin da aka kafa zai dinga tantance lafiyar gine-gine ta amfani da tsarin launukan ja, da kore da rawaya.

    Yawan waɗanda suka mutu ya haura 1,700, yayin da har yanzu ba a san inda dubban mutane suke ba.

    Har yanzu jami'an ceto na ci gaba da zaƙulo mutane da rai daga ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, duk da cewa kwanaki biyar sun shige tun bayan afkuwar tagwayen girgizar ƙasar.

    Sai dai wakilin BBC a birnin La Guaira, wanda shi ne yankin da lamarin ya fi muni, ya ce aikin ceton na fuskantar ƙalubale, har ta kai ga sojoji na neman shawara daga fararen hula kan hanyoyin da suka fi dacewa wajen taimakawa.

    Wakilin ya kuma ce ƴan Venezuela na ci gaba da tururuwar zuwa yankunan da girgizar kasar ta shafa domin bayar da gudummawarsu.

  2. Kotun Ƙolin Amurka ta dakatar da yunƙurin Trump na korar gwamnar Babban Banki

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun Kolin Amurka ta dakatar da yunƙurin Shugaba Donald Trump na korar ɗaya daga cikin gwamnonin Babban Bankin ƙasar, Lisa Cook, bayan ya zarge ta da damfara da ta shafi takardun rancen sayen gidaje.

    A hukuncin da alƙalai biyar suka goyi baya, huɗu kuma suka nuna adawa da shi, kotun ta ce ba a bai wa Cook damar kare kanta yadda ya kamata kan zargin da ake mata ba.

    Cook ta yi maraba da hukuncin, tana mai cewa batun ba shi da alaƙa da takardun rancen da aka sanya wa hannu shekaru da dama da suka gabata. Ta ce zargin wani yunkuri ne da aka ƙirƙira domin a cire ta saboda ta ƙi bin matsin lambar siyasa.

    Shi kuwa Shugaba Trump ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa, "wanda ya aikata laifi ba zai ci gaba da yanke muhimman hukunci da suka shafi walwalar Amurka ba."

    A wani hukunci na daban, Kotun Kolin Amurka ta ce ba za ta saurari ɗaukaka ƙarar da Shugaba Trump ya shigar ba kan hukuncin da ya same shi da laifin cin zarafi da kuma ɓata sunan marubuciya E. Jean Carroll.

    Hukuncin na nufin Trump zai ci gaba da biyan diyyar dala miliyan biyar da kotu ta umarce shi ya biya Carroll.

    Carroll ta zargi Trump da cin zarafinta a wani kantin sayar da kaya da ke New York a shekarun 1990, zargin da Trump ya sha musantawa.

    Sai dai a shekarar 2023, masu yanke hukunci sun same shi da laifin cin zarafin lalata da kuma ɓata sunan Carroll bayan ya bayyana zargin nata a matsayin ƙarya.

  3. Dubban ƴan cirani na ƙoƙarin ficewa daga Afirka ta Kudu gabanin wa'adin zanga-zangar kyamar baƙi

    Dubban baƙi mazauna Afirka ta Kudu na ƙoƙarin barin ƙasar kafin cikar wa'adin da wasu ƙungiyoyin masu adawa da baƙi suka gindaya musu su fice.

    Mutane da dama sun taru a sansanonin da aka tanada domin sauƙaƙa musu tafiya, inda suka ce suna fargabar ɓarkewar tashin hankali yayin zanga-zangar da aka shirya gudanarwa ranar Talata, 30 ga Yuni.

    Yanzu hankali ya koma kan yadda zanga-zangar za ta kasance, ko za ta gudana cikin lumana ko kuma za ta rikide zuwa rikicin kyamar baƙi irin wanda aka sha gani a baya a ƙasar.

    Wasu daga cikin masu shirin barin ƙasar sun ce sun bar iyalansu, abokan zamantakewa da kuma ƙananan yaransu saboda gaggawar ficewa.

    A halin da ake ciki, an girke jami'an tsaro da dama a sassan ƙasar kafin zanga-zangar, yayin da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu tare da kauce wa tashin hankali.

    Haka kuma, ofisoshin jakadancin ƙasashe daban-daban sun cika da jama'ar da ke neman taimakon komawa ƙasashensu.

  4. Kasashen Duniya za su tallafawa Venezuela bayan girgizar ƙasa

    Venezuela

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen duniya na ci gaba da alkawarin bayar da taimako ga Venezuela bayan tagwayen girgizar kasar da aka yi a makon da ya gabata.

    Ƙasar Netherlands ta sanar da aikawa da jirgin ruwa mai ɗauke da kayan agaji, yayin da China ta yi alƙawarin bayar da tallafi kusan dala miliyan 15.

    Wakilin BBC ya ce, halin da ake ciki a nan ya yi tsanani, kuma Venezuela na matukar bukatar taimako cikin gaggawa.

    An yi nasarar zakulo wani matashi mai shekara 21 daga cikin ɓaraguzai bayan ya shafe fiye da sa'a 100 a maƙale, yayin da fatan da ake da shi na samun masu sauran numfashi ke ƙara dusashewa, hankali ya ƙara tashi bayan ƙasa ta ƙara motsi, sai dai babu rahotannin wani lahani da ta yi.

    An tabbatar da mutuwar kusan mutaum 1,500, amma ana zaton dubban mutane har yanzu sun ɓace.

  5. Har yanzu ba a buɗe babbar kafar yaɗa labarai mai zaman kanta a Uganda ba

    Yoweri Museveni

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar kafar yaɗa labarai mai zaman kanta a Uganda ta ce har yanzu ba ta koma bakin aiki ba, kwana guda bayan da shugaban rundunar sojin ƙasar, Janar Muhoozi Kainerugaba, ya bayar da umarnin rufe jaridarta da tashoshin talabijin da rediyonta.

    Daraktar gudanarwar kafar, Susan Nsibirwa, ta shaida wa BBC cewa har yanzu ba a sake wallafa jaridar ba, yayin da tashoshin talabijin da rediyonta ke ci gaba da kasancewa a rufe bayan jami'an tsaro sun ƙulle ofisoshin kamfanin da ke Kampala, babban birnin ƙasar.

    Ta ce har yanzu tana buya saboda barazanar da aka yi mata, duk da cewa an saki wasu daga cikin ma'aikatan kafar da aka tsare a daren Lahadi.

    Kamfanin ya ce yana jiran ƙarin bayani daga hukumomi, bayan da hukumar da ke kula da kafafen yaɗa labarai ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan matakin rufe kafar.

  6. Har yanzu farashin man fetur bai koma daidai ba a Najeriya

    ....

    Hukumar kare haƙƙin masu saye ta Najeriya (FCCPC) ta ce har yanzu farashin man fetur bai koma daidai yadda ya kamata ba a ƙasar duk da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

    Hukumar ta bayyana cewa binciken farko da take gudanarwa ya nuna raguwar farashin fetur a matatar mai da gidajen mai bai yi daidai da yadda farashin danyen mai ya ragu ba, lamarin da ke janyo damuwa ga masu saye.

    Ta yi gargaɗin cewa duk wani kamfani da aka samu da laifin cin zarafin jama’a ta hanyar tsayar da farashi ba bisa ka’ida ba zai fuskanci hukunci.

    Babban jami’in hukumar, Tunji Bello, ya ce abin tashin hankali ne yadda masu sayar da mai ke gaggauta ɗaga farashi idan ɗanyen mai ya yi tsada, amma suke jinkirin rage shi idan ya sauka, yana mai jaddada cewa duk da cewa kasuwa na karkashin tsarin ’yanci, dole ne a samu adalci ga kowa.

    Hukumar ta ƙara da cewa duk da cewa wasu dalilai kamar canjin kuɗi, sufuri da tsadar tace mai na shafar farashin, ya kamata ragin farashin danyen mai da ya sauka daga kusan dala 120 zuwa kusan dala 73 ya haifar da sauƙi a farashin fetur, maimakon ci gaba da kasancewarsa kusa da naira 1,200 kan kowace lita.

  7. Sojojin Najeriya sun ceto ɗalibai da malamai 10 da aka sace a Borno

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun ce sun ceto ɗalibai da malamai 10 da ƴan ƙungiyar ISWAP suka sace a wani hari da suka kai yankin Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.

    A wata sanarwa da mukaddashin jami'in yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safiyar ranar Litinin, lokacin da mayaƙan suka kai hari makarantar sakandaren fasaha ta Lassa, inda ɗaliban ke rubuta jarabawar kammala sakandare NECO.

    Sanarwar ta ce nan take rundunar ta tura sojoji tare da jiragen yaƙi domin gudanar da aikin ceto kuma bayan fafatawa da mayaƙan a yankin Daggu, sojojin sun samu nasarar ceto mutum 10 ba tare da sun ji rauni ba.

    "Har yanzu ana ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutanen da suka rage, tare da kamo waɗanda suka aikata harin domin gurfanar da su a gaban shari'a," in ji sanarwar.

    Rundunar ta ce yayin artabun, sojojin sun kashe wasu daga cikin mayaƙan tare da ƙwace babura bakwai da suka yi amfani da su wajen kai harin, lamarin da ya hana su tserewa cikin sauƙi.

    Sai dai rundunar ta ce an kashe wani soja da kuma mutum ɗaya daga cikin jami'an sa kai na JTF, a yayin musayar wuta da mayaƙan.

    Duk da wannan nasara da rundunar sojin Najeriyar ta samu, har yanzu akwai ɗalibai sama da 50 da ke hannun ƴan bindigar da suka sace su a jihohin Borno da Oyo tun a watan Mayun 2026, inda gwamnatin ƙasar ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin ceto su.

  8. Babban jami'in ƴan sandan Afirka ta Kudu ya sha da ƙyar bayan yunƙurin kashe shi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗaya daga cikin manyan jami'an ƴan sanda a Afirka ta Kudu ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin da aka yi na kashe shi a birnin Johannesburg, a cewar ƴan sanda.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an harbi mataimakin sashen leƙen asiri da aka dakatar, Maj-Gen Feroz Khan da yammacin ranar Lahadi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida, kuma tuni aka garzaya da shi asibiti domin yi masa tiyatar gaggawa.

    Harbin na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin Khan ya ba da shaida a wani bincike da ake gudanarwa kan aikata laifuka a rundunar ƴan sandan Afirka ta Kudu.

    An kama Khan ne tare da wasu mutane biyu a watan Mayu bisa zargin cinikin zinari ba bisa ƙa'ida ba.

    A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar ƴan sandan Afrika ta Kudu Brig Athlenda Mathe ta fitar a ranar Litinin ta ce ƴan sanda na gudanar da bincike kan harbin Khan.

  9. An zaƙulo mutumin da ya yi kusan kwana biyar a ƙarƙashin ɓaraguzai a Venezuela

    ...

    Asalin hoton, X / @nayibbukele

    Tawagar ma'aikatan ceto daga Venezuela, Mexico, da El Salvador sun kuɓutar da wani matashi ɗan shekara 21 a jihar La Guaira, in ji shugaba Nayib Bukele daga El Salvador.

    An zaƙulo Aaron Levi Cantillo Vargas ne da ransa a ƙarƙashin ɓaraguzai a garin Caraballeda, amma kafin masu ceto su kai ga Aaron, sia da suka ci karo da gawar wani da ginin ya rufto masa.

    A halin yanzu matashin yana samun kulawa ta musamman a asibiti, in ji Bukele, ya kara da cewa masu ceto za su ci gaba da aiki tare da fatan samun damar ceton rayuka da dama.

    Shugabar riƙo ta Venezuela Delcy Rodríguez ta ce aikin ceton ya ɗauki sa'o'i 43, bayan da Aaron ya maƙale na tsawon sa'o'i 106.

  10. Kocin ƙwallon ƙafar Koriya ta Kudu ya yi murabus bayan rashin nasara a gasar cin kofin duniya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Hong Myung-bo ya yi murabus daga muƙaminsa na kocin tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar Koriya ta Kudu bayan da suka kasa tsallakewa zuwa zagayen gaba na gasar cin kofin duniya. \

    Ƙungiyar ta yi fatan za ta iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba a gasar a matsayin ɗaya daga ƙasashe takwas na alfarma, amma hakan ya ci tura ranar Asabar.

    Ficewar da wuri ya haifar da suka a gida, inda shugaban ƙasar Lee Jae Myung ya yi kira da a gudanar da bincike kan dalilan da suka sa tawagar ta kasa taka rawar gani.

    Hong ya nemi afuwar magoya bayansa ranar Lahadi kuma ya ce alhakin "ya rataya ne a wuya ta ni kaɗai a matsayina na kociyan ƙungiyar".

    Koriya ta Kudu wadda ke matsayi na 32 a jerin ƙasashen da suka fi hazaƙa a fagen ƙwallon ƙafa, ta ci wasa ɗaya da kuma sha kashi a wsanni biyu a gasar cin kofin duniya ta, inda ta ƙare a bayan Mexico da Afrika ta Kudu, wadanda ke matsayi na 15 da 60 a duniya.

  11. Iran ta buƙaci mu yi wata ganawar a Qatar - Trump

    ....

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Iran ta nemi a yi wata ganawa da Amurka a ranar Talata a birnin Doha na ƙasar Qatar, bayan da ƙasashen biyu suka sake kai wa junansu hare-hare a kwanakin baya, lamarin da ke barazana ga tsagaita wuta da ake ƙoƙarin tabbatarwa

    Fadar White House ta ce manyan masu tattaunawa na Amurka, Jared Kushner da Steve Witkoff, za su halarci taron, inda kuma Trump ke fatan ganin an ci gaba da tattaunawar sulhun ba tare da tangarɗa ba.

    Haka kuma ta bayyana cewa za a gudanar da wasu tattaunawa a gefe domin ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da ke tsakanin ɓangarorin.

    Sai dai mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya musanta cewa za a yi irin waɗannan tattaunawar a wannan makon, yana mai cewa har yanzu ba a kammala shiri kan ranar da wurin ganawar ba, kuma ana masu shiga tsakani na ci gaba da shawarwari kan yadda tattaunawar za ta kasance.

  12. Hotunan ɓarnar da girgizar ƙasar Venezuela ta haddasa

    Ga wasu hotuna da ke nuna ɓarnar da girgizar ƙasa ta haddasa a Venezuela, inda gine-gine suka rushe ƙurmus suka koma tarkace. Rahotanni sun nuna cewa girgizar ƙasar ta janyo asarar rayuka sama da 1,400 tare da lalata gidaje da kadarori.

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wannan ginin ya rushe ƙuruƙus sakamakon girgizar ƙasar, inda tarkace suka mamaye ko’ina, tare da wasu mutane suna tsaye a wajen ɓarnar.
    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Masu aikin ceto suna bincike a cikin tarkacen gine-gine domin gano waɗanda suka maƙale.
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wannan kuma na nuna ɓarnar da girgizar ƙasa ta haddasa inda ake iya ganin yadda gine-gine suka rushe suka zama tarkace a ko’ina, ana kuma ganin lalacewar yankin daga sama.
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Nan ma wasu masu aikin ceto ne ke aiki a kan tarkacen gine-ginen da girgizar ƙasar ta rusa a Venezuela
    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jami’an ceto na tsaye a gaban wani gini da ya rushe sakamakon girgizar ƙasar, yayin da tarkace suka bazu a ko’ina.
  13. 'Iran da Amurka za su ci gaba da tattaunawa a Doha nan da kwanaki'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar Iran da Amurka ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa tawagogin ƙasashen biyu na aiki kan yadda za a ci gaba da aiwatar da tattaunawar yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka kuma ana sa ran za su gana ne a birnin Doha cikin kwanaki masu zuwa.

    Majiyar ta kuma bayyana cewa masu shiga tsakani sun buƙaci kafa hanyoyin sadarwa tsakanin ɓangarorin domin rage tashin hankali da kuma kauce wa duk wasu rikice-rikice, tare da ci gaba da tattaunawar fasaha a lokaci guda.

    A halin yanzu, shugaban tawagar Iran, Kazem Gharibabadi, wanda ke ƙasar Oman, ya sanar da gudanar da taron farko na kwamitin hadin gwiwa kan mashigar Hormuz tsakanin ƙasashen biyu a birnin Muscat.

    Rahotanni sun nuna cewa wannan yunƙuri na daga cikin matakan diflomasiyya da ake ɗauka domin rage rikici tare da tabbatar da zaman lafiya, musamman kan batun tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmanci ga harkokin mai a duniya.

  14. Har yanzu gwamnati ba ta tuntuɓe mu ba - Iyalan Shugaban Miyetti-Allah

    ....

    Asalin hoton, Amnesty International

    Iyalan shugaban ƙungiyar Miyetti-Allah, Alhaji Ardo Risku da aka kashe a jihar Benue sun koka cewa har yanzu gwamnati ba ta tuntuɓe su ba tun bayan faruwar lamarin, duk da alƙawuran da ake yi na cewa za a ɗauki mataki kamar yadda babban ɗan marigayin, Muhammad Idris ya shaida wa BBC.

    Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ’yansandan jihar Benue ta tabbatar da kama mutum 10 da ake zargi da hannu a kisan shugaban da wasu mutum uku, waɗanda aka harbe su a ranar Juma’a yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga wani taro da ya shafi tsaron jihar.

    Gwamnatin jihar Benue ta bayyana cewa ta yi Allah wadai da kisan tare da ƙaddamar da bincike, amma iyalan marigayin sun ce ba su ji wani sakamako kai tsaye daga gwamnati ba.

    Sun bayyana cewa har yanzu suna jiran a tuntuɓe su domin ganin an yi musu bayani kan matakan da ake ɗauka.

    Babban ɗan ya ce a ranar da aka kashe shi, ya je ya gaishe shi da safe, inda ya shaida masa cewa DPO na karamar hukumar Ohimini ya kira shi domin wani taro. “Sai ya kira wasu mutum uku su tafi tare, suka hau babur suka nufi inda za a yi taron,” in ji shi.

    Ya ƙara da cewa sun samu labarin kisan ne bayan sallar Juma’a, lokacin da suka ga mutane sun taru ana cewa an ga wasu mutane a bakin hanya an harbe su.

    “Mun kira wayoyinsu ba su shiga ba, daga nan muka tafi wurin muka tarar ’yansanda sun riga mu, sun ɗauki gawarwakin,” in ji shi, yana mai korafin cewa, “tun daga lokacin DPO bai kira mu ba, gwamnatin ma ba ta tuntuɓe mu ba.”

    Benue na daga cikin jihohin arewa ta tsakiyar Najeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro, inda ake samun yawaitar fito na fito tsakanin manoma da makiyaya.

    Gwamnatin Najeriya da kuma na jihar sun sha iƙirarin cewa suna yin bakin ƙoƙarinsu wajen shawo kan lamarin, sai dai har yanzu abin ya ci tura.

    Wani rahoto na Majalisar dokokin Amurka ya zargi ƙungiyoyin makiyaya da kasancewa cikin masu hannu wajen 'gallaza wa Kiristoci' a Najeriya, lamarin da ƙungiyoyin suka musanta.

  15. Ko sakamakon zaɓen 2023 zai iya zama madubin na 2027?

    ...

    Tun bayan da jam'iyyun siyasa a Najeriya suka kammala zaɓukar fitar da gwanayen da za su tsaya musu takara a zaɓukan 2027, wasu ƴanƙasar suka soma hasashen sakamakon zaɓen da ke tafe ta hanyar kwatanta shi da na 2023 da ya gabata.

    Bisa ga bayanan zaɓukan fitar da gwanayen ƴantakarar da suka fatata a 2023 ne za su sake karawa a zaɓen na 2027.

    Hakan ne ma ya sa wasu ƴanƙasar ke amfani da lissafin sakamakon 2023 domin hasashen sakamakon 2027.

    To sai dai masana da masu sharhin siyasar ƙasar na cewa sakamakon 2023 ba zai zama madubin na 2027 ba.

    A watan Janairun 2027 ne dai za a yi zaɓen shugaban ƙasa a Najeriyar, ƙasar da ta fi kowa yawan al'umma a nahiyar Afirka.

  16. Mutum biyar sun mutu, takwas sun jikkata a hatsarin mota a Neja

    An tabbatar da mutuwar mutum biyar, yayin da wasu takwas suka jikkata sakamakon hatsarin mota da ya faru a ranar Lahadi a yankin Agaie da ke ƙaramar hukumar Agaie a jihar Neja.

    Jami’in hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) a yankin, Hussaini Guregi, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

    Ya ce hatsarin ya shafi wata babbar mota ɗauke da kimanin fasinjoji 40 da kuma wata tankar mai.

    Motar na kan hanyarta ne daga Gusau a jihar Zamfara zuwa Shagamu a jihar Ogun lokacin da hatsarin ya afku.

    Guregi ya bayyana cewa mutane biyar sun mutu nan take, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kwamishinan Agaie domin samun kulawa.

  17. Gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da aikin kwaso ’yan Najeriya daga Afirka ta Kudu

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kwaso ’yan ƙasar daga Afirka ta Kudu, inda ake samun fargabar hare-haren ƙyamar baƙi dab da zanga-zangar da ake shirin yi a ranar 30 ga Yuni.

    An ce wani jirgin Air Peace ya tashi daga Najeriya a ranar Litinin, tare da shirin kwaso wasu daga cikin ’yan ƙasar zuwa Legas a safiyar Talata.

    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya ce wannan mataki na daga cikin shirin gwamnati na ba da dama ga ’yan ƙasar da ke son dawowa gida cikin aminci.

    Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shirin kwashe ’yan Najeriya kafin fara zanga-zangar adawa da baƙi a Afirka ta Kudu.

    Rahotanni sun nuna cewa fiye da ’yan Najeriya 700 na maƙale har yanzu a Afirka ta Kudu, kwanaki kaɗan kafin wa’adin da wasu ƙungiyoyin masu ƙyamar baƙi suka bayar ya cika.

    An kuma ce jinkirin fitar da kuɗin aikin kwaso ƴan ƙasar ya janyo tsaiko, lamarin da ya bar mutane da dama cikin barazana yayin da damuwar kai musu hare-hare ke ƙaruwa.

    Duk da haka, gwamnatin ta shawarci ’yan Najeriya da za su ci gaba da zama a Afirka ta Kudu su kasance cikin taka-tsantsan, su guji wuraren da ake zanga-zanga, tare da riƙa sadarwa da ofishin jakadancin Najeriya domin samun bayanai.

  18. Iran ta ƙara ƙaimi wajen yin kutse ta intanet tun bayan fara yaƙi - Isra'ila

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban jami’in tsaron intanet na Isra’ila ya ce Iran ta ƙara ƙaimi wajen yin kutse ta intanet tun bayan fara yaƙi tsakanin ƙasashen biyu.

    Yossi Karadi ya bayyana cewa an samu ƙaruwa a kutsen intanet daga Iran a cikin watannin baya-bayan nan.

    A wata hira da ya yi da jaridar Die Welt ta Jamus, Karadi ya ce a watan Yunin 2025, lokacin da Isra’ila ke gudanar da hare-haren soji kan Iran, sun gano kusan kutse ta intanet daga Iran 1,600.

    Amma a cikin makonni huɗu na baya-bayan nan na Yunin 2026, adadin ya ƙaru zuwa kusan 4,800.

    Ya ƙara da cewa masu yin kusten daga Iran ƙwararru ne sosai inda ya kuma ce dole ne a ɗauki lamarin da muhimmanci.

    Karadi ya kuma ce kutsen da Iran take yi ta intanet ɗin na harin muhimman cibiyoyin ƙasa, da ƙananan da matsakaitan kamfanoni kamar na lauyoyi da masu binciken kuɗi, da kuma jama’a baki ɗaya.

  19. Hare-haren saman Pakistan a Afghanistan sun hallaka mutane da dama

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani kakakin gwamnatin Taliban ya ce hare-haren sama da Pakistan ta kai kan yankuna a Afghanistan sun yi sanadiyyar kashe da jikkata fararen hula da dama, ciki har da mata da yara, a lardunan Paktika, Paktia da Kunar.

    Zabihullah Mujahid ya bayyana matakin na Pakistan a matsayin hari na “ban tsoro da ta’addanci,” yana mai cewa abin da ya faru ya saɓawa dokokin kasa da kasa ne.

    A wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta, an ga yara da fararen hula da suka jikkata sakamakon hare-haren.

    Sai dai a nata ɓangaren, Pakistan ta ce ta kai harin ne kan wuraren da ke karkashin mayaƙan Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP) da Jamaat-ul-Ahrar, inda ta ce ta kashe aƙalla mayaƙa 25.

    Jami’an Taliban sun ce aƙalla mutane 38 ne suka rasa rayukansu a hare-haren na daren jiya, inda mataimakin kakakin gwamnatin ya ƙara da cewa mutum 30 daga cikinsu sun mutu ne a kauyen Mandokhel da ke gundumar Samkani a lardin Paktia kadai.

  20. 'Iran da Amurka sun amince su rage tashin hankali da ci gaba da tattaunawa'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jami’in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa Iran da Amurka sun amince su dakatar da kai wa juna hare-hare tare da ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya.

    A cewarsa, za a ci gaba da tattaunawa kan dukkan fannoni na yarjejeniyar, yayin da ɓangarorin biyu za su ƙaurace wa ƙara tsananta rikici a halin yanzu, tare da bai wa jiragen ruwa damar zirga-zirga cikin ‘yanci.

    Duk da wannan bayani, har yanzu Iran ba ta tabbatar da rahoton ba.

    A ‘yan kwanakin nan dai, rikici ya ƙara tsananta sakamakon taƙaddama kan tafiyar da mashigar Hormuz, tare da kai wa juna hare-hare tsakanin Iran da Amurka, lamarin da ya ƙara yawan fargabar rushewar tsagaita wutar da ake ƙoƙarin cimmawa.

    Jami’in na Amurka, wanda ya nemi a sakaya sunansa, bai bayyana lokacin da kuma wurin da za a ci gaba da tattaunawar ba, sai dai wasu majiyoyi sun ce ana sa ran ɓangarorin biyu za su sake haɗuwa a Doha, babban birnin Qatar, domin ci gaba da tattaunawa, yayin da kowanne ɓangare ke zargin ɗayan da karya yarjejeniyar da aka cimma a baya-bayan nan.