Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Laraba 09/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji

Rahoto kai-tsaye

Daga Muslim Muhammad Yusuf da Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Wani fasinja ya mutu bayan jirgin ƙasa ya yi hatsari da babbar mota a wurin ketare layin dogo a Poland

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani fasinja ya mutu a ƙasar Poland bayan da wani jirgin ƙasa ya sauka daga kan layinsa sakamakon karo da babbar motar da ke haɗa siminti a wurin da layin jirgin ya haɗu da hanyar mota.

    Kimanin kimanin 120 ne ke cikin jirgin mai zirga-zirga tsakanin birane a lokacin da hatsarin ya auku a Sokolniki Suche, wani wuri mai nisan kilomita 100 (mil 60) kudu da babban birnin ƙasar, Warsaw, da misalin karfe 11:20 na safe.

    Kamfanin PKP Intercity, wanda ke kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa na dogon zango a ƙasar, ya bayyana cewa: "Mutane 20 ne suka samu raunuka, kuma huɗu daga cikinsu sun kasance munana ".

    Wannan shi ne karo na biyu da irin wannan lamari ya faru a ƙasar Poland cikin ƴan kwanakin nan.

    Firaminista Donald Tusk ya bayyana cewa hatsarin "mai tsanani ne matuƙa, kuma hakan na nufin dole ne mu fara ɗaukar matakan gaggawa na samar da dokoki masu tsauri".

  2. An tuhumi wani ɗan Birtaniya da laifin taimaka wa hukumar leƙen asirin Rasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An gurfanar da wani mutum ɗan ƙasar Birtaniya mai shekara 31 a ƙarƙashin dokar tsaron ƙasa (National Security Act) bisa zargin tuntuɓar hukumar leƙen asirin sojin Rasha.

    Hukumar kula da Shari'a ta Birtaniya (CPS) ta bayyana cewa, ana zargin Joshua Cammidge, mazaunin garin Swindon, da karɓar umarni daga wani mutum da ake kyautata zaton yana da alaƙa da ƙungiyar 'GRU Volunteer Corps'—wata ƙungiya da hukumar leƙen asirin sojin Rasha ke tafiyar da ita.

    Ana tuhumarsa da laifin taimaka wa hukumar leƙen asiri ta ƙasashen waje da kuma yin shirye-shiryen aikata laifi.

    Ana sa ran zai bayyana a gaban Kotun Majistare ta Westminster a ranar Alhamis.

    Jami'an ƴan sandan yaƙi da ta'addanci na Landan (CTP), tare da goyon bayan jami'an ƴan sandan Wiltshire, sun kama Cammidge a wani gida da ke Swindon a ranar Juma'a.

    Hukumar ƴan sandan Metropolitan ta bayyana cewa, an kai shi tashar ƴan sanda a Landan tare da gudanar da bincike a wani gida daban a Swindon.

    An sake kama shi tare da tsare shi a ƙarƙashin Dokar Tsaron Ƙasa a ranar Asabar.

  3. Masu sarauta a Turai sun yi bankwana da Sarki Harald V na Norway

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutane da dama daga cikin ƴaƴan gidajen sarautar Turai da shugabannin ƙasashe, ciki har da Yariman Wales da sarakuna uku daga ƙasashen yankin Nordic, sun halarci jana'izar Sarki Harald V a birnin Oslo.

    Dubban mutane ne suka jeru a kan hanyar da aka bi wajen gudanar da jerin gwano na jana'izar daga fadar sarauta zuwa babban cocin Oslo a ranar Laraba da yamma, kimanin makonni biyu bayan rasuwar sarkin yana da shekaru 89 a duniya.

    Bayan kammala jana'izar, iyalan gidan sarautar Norway—ciki har da sabon Sarki Haakon da matarsa ​​Sarauniya Mette-Marit, da mahaifiyarsa kuma matar marigayi Harald, Sarauniya Sonja—sun yi wa jama'a barka da zuwa yayin da suke tsaye a barandar fadar.

    An kuma yi shiru na tsawon minti ɗaya a fadin ƙasar baki ɗaya.

    Sarki Harald, wanda aka bayyana a matsayin shugaba mai farin jini da kuma kawo sauye-sauyen zamani, ya shafe shekaru 35 yana mulkin ƙasar Norway.

  4. Za a kawo ƙarshen yaƙin Iran bayan zaɓen watan Nuwamba -

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya shaida wa ƴan jarida a ranar Laraba cewa, yana ganin za a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran "kai tsaye bayan zaɓen da za a yi a Amurka."

    Mista Trump yana nufin zaɓen tsakiyar wa'adi da za a gudanar a Amurka a watan Nuwamba.

    An tsara gudanar da zaɓukan ne a ranar 3 ga watan Nuwamba. "Saboda ba za su iya ci gaba da jurewa ba. Sun shiga mawuyacin hali kuma suna ƙoƙarin yin tasiri kan zaɓen domin a samu gungun mutane masu rauni a majalisa, waɗanda za su ƙyale su su mallaki makamin nukiliya.

    Abin da kawai suke buƙata shi ne makamin nukiliya, kuma idan suka samu makamin nukiliya, duniya baki ɗaya za ta shiga cikin babban haɗari," in ji shi.

    Ya kuma ce "ana iya tattaunawa, amma ba ita ce abin da muke nema ba."

    A cikin jawabinsa, Mista Trump ya kuma yi ishara da batun nutsewar wasu jiragen ruwa tara na Iran masu ɗaukar man fetur, inda ya ce, "Mu ne muka kai waɗannan hare-haren."

  5. An ji ƙarar fashewar abubuwa a mashigar Hormuz

    A cewar rahotannin kafofin yaɗa labaran Iran, an ji ƙarar fashewa ƴan mintuna kaɗan da suka gabata daga yankin Mashigar Hormuz.

    Bisa waɗannan rahotanni, sa'a ɗaya kafin hakan, an ji ƙarar harbe-harbe da dama a yankin Mashiga, a birnin Jask.

    Har yanzu ba a bayar da ƙarin bayani kan wannan lamari ba.

  6. Mutum biyu sun mutu a kan iyakar Moldova bayan hare-haren Rasha da Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa mutum biyu sun mutu bayan da jiragen yaƙi marasa matuƙa na Rasha suka kai hari kan wata mashigar iyaka tsakanin Ukraine da Moldova.

    An rufe mashigar ta Starokozache bayan harin da aka kai da daddare.

    Hotunan wurin sun nuna motoci da dama da suka ƙone ƙurmus a tsakiyar ɓaraguzan gine-gine.

    A birnin Kyiv, babban birnin Ukraine, jami'ai sun ce an kashe wata mata tare da jikkata mutane 14, ciki har da yara biyu, bayan da wani jirgi mara matuƙi na Rasha ya bugi wani rukunin gidaje mai hawa tara.

    A Rasha kuma, jami'ai sun ce an kashe mutum huɗu, ciki har da ƙaramin yaro ɗaya, a tashar jiragen ruwa ta Novorossiysk dake bakin Tekun Black Sea sakamakon harin jirgin mara matuƙi na Ukraine; haka kuma wani jirgin ya bugi wata cibiyar masana'antu a birnin Novy Urengoy dake yankin Arctic, nesa da Ukraine da kimanin kilomita 3,000 (mil 1,864).

    A ƴan kwanakin nan, Rasha da Ukraine sun ƙara tsananta kai hare-hare masu nisan zango, duk da sabon ƙoƙarin diflomasiyya na kawo ƙarshen yaƙin.

  7. Muna daf da hamɓarar da gwamnati Iran - Natanyahu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa "Mun kusa hamɓarar da gwamnatin Iran" yayin da yake ziyartar yankin Jabal al-Sheikh na Siriya da Isra'ila ta mamaye,

    Bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad, Isra'ila ta ƙwace yankin tsaunukan Jabal al-Sheikh da ke Siriya.

    "Har yanzu akwai aikin da ya kamata a yi; babban manufar ita ce kawar da gwamnatin Iran mai ɗaukar nauyin ta'addanci. Mun kusa cimma wannan manufa. Mun san cewa daga karshe, dukkanin wannan ƙawance zai ruguje," in ji shi a cikin wani sakon bidiyo da ya fitar daga yankin.

    Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, shi ma ya raka Benjamin Netanyahu a yayin wannan ziyarar.

  8. Labarai da dumi-dumi, IAEA ta tura batun nukiliyar Iran gaban Kwamitin Tsaro na MDD

    Jakadan Iran a Kwamitin Tsaro na MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin gudanarwar Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya amince da wani ƙuduri da aka gabatar na miƙa batun Iran ga Kwamitin Sulhu domin duba zargin da ake yi wa ƙasar kan rashin cika wasu alƙawuran da suka shafi shirinta na nukiliya.

    A nata ɓangare Iran ta nuna rashin jin daɗinta game da matakin.

    A martanin farko da ya mayar kan wannan mataki, mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya wallafa a shafinsa na X cewa: "Sun kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran da ke ƙarƙashin kulawar IAEA, sun kawo cikas ga tsarin bincike da sa ido na yau da kullum, sannan suka yi amfani da wannan cikas a matsayin hujjar fitar da ƙuduri a Kwamitin Gudanarwar IAEA''.

    ''Da irin waɗannan hare-haren sama, ba za ku iya ɓoye gazawar manufofinku da ayyukanku ba, kuma ba za ku cimma wani abu a Kwamitin Sulhu ba," kamar yadda ya wallafa.

    Wannan ne karo na farko cikin shekaru 20 da aka miƙa batun Iran ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya bisa zargin karya alƙawuran da suka shafi hana yaɗuwar makaman nukiliya.

    Wasu jami'an diplomasiyya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, ƙudurin ya samu amincewa ne da ƙuri'u 23 masu goyon baya, yayin da ƙasashe uku suka ƙi amincewa, sannan takwas suka ƙaurace wa kaɗa ƙuri'a.

    Rahotanni sun ce Rasha da China da Nijar ne ƙasashen da suka ƙi amincewa da ƙudurin.

    Matakin na zuwa ne bayan wani ƙuduri da aka amince da shi a ranar 12 ga Yuni na bara, kwana guda bayan Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare kan wasu cibiyoyin nukiliyar Iran.

    A lokacin wannan rikici, Amurka ita ma ta kai hare-hare kan wasu wuraren nukiliyar Iran.

  9. Uganda za ta janye daga gasar Invictus ta Yarima Harry, in ji babban hafsan soji

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Uganda na janye daga gasar Invictus Games—gasar wasanni ta tsoffin sojoji da suka samu raunuka, wadda Duke na Sussex ke jagoranta—bayan watanni biyu kacal da kasar ta bayyana aniyarta ta shiga gasar.

    Janar Muhoozi Kainerugaba, babban hafsan tsaron ƙasar kuma ɗan shugaban ƙasa, ne ya sanar da hakan ta wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

    Ya bayyana cewa an ɗauki matakin janyewa daga gasar ne "domin gudun kada a fassara hakan a matsayin nuna adawa ga Mai Martaba Sarki Charles na Uku".

    Kakakin gwamnatin Uganda, Alan Kasujja, ya tabbatar wa BBC hakan inda ya ce: "Janar Kainerugaba ne ke yanke hukunci kan ko rundunar sojin ƙasar (UPDF) za ta shiga gasar Invictus Games ko akasin haka.

    Abin da kuka gani shi ne matsayinsa da ya bayyana. Idan kuma ya canza, zai sanar da duniya."

  10. Merz na Jamus ya caccaki jam'iyyar AfD bayan nasarar da jam'iyyar ta samu a zaɓe

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya yi karo da shugabar jam'iyyar AfD Alice Weidel a majalisar dokoki, inda ya kira jam'iyyarta "abin da ke lalata muradunm ci rani " wanda ya yi daidai da "shafe al'umma daga doron ƙasa" ga ma'aikata masu ƙwarewa.

    Merz yana jawabi ne ga majalisar Bundestag bayan nasarar da jam'iyyar adawa da shige da fice ta samu a jihar Saxony-Anhalt da ke gabashin ƙasar inda ta lashe kusan kashi 44% na ƙuri'un.

    Weidel ta shaida wa ƴan majalisar cewa masu zaɓe sun nuna cewa haɗin gwiwar Merz da masu matsakaicin ra'ayi ya gaza gaba ɗaya kuma lokacinsa ya ƙare.

    Merz ya mayar da martani yana mai cewa jam'iyyar AfD ta cutar da muradun Jamus ta hanyar goyon bayan Rasha, kuma manufarta kan batun ci rani za ta shafi miliyoyin mutane.

  11. Iran ta yi Alla-wadai da harin Amurka kan jiragen dakon man fetur ɗinta

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Alla-wadai da hare-haren da Amurka ta kai kan jiragen dakon man fetur na Iran, tare da gargaɗin illar da irin waɗannan hare-hare ka iya haifarwa.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, ma’aikatar ta ce dakarun Iran sun kai hari kan sansanonin sojin Amurka da cibiyoyinta da ke Jordan, wadda ta ce tana ci gaba da tallafa wa hare-haren sojin Amurka kan Iran, da kuma wasu jiragen ruwan Amurka.

    Ma’aikatar ta ce hare-haren Amurka na ƙara dagula lamura a yankin kuma suna zama barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya.

  12. Ƴan sandan Nijar sun kai samame maɓoyar ƴan fashi da masu safarar miyagun ƙwayoyi, Daga Tchima Illa Issoufou

    Ƴan sandan Nijar

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami’an ƴan sandan Nijar a jihar Agadez, sun kai samame a wata kasuwar Sarasuka da ke yankin Tabelot, ɗaya daga cikin wuraren da rundunar ƴan sandan ta ce ƴan fashi da masu safarar miyagun ƙwayoyi ke taruwa.

    Wannan samame na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ƴan fashi da sauran manyan laifuka a yankin Tchirozérine.

    A yayin samamen, ƴan sanda sun kama mutane 67 tare da ƙwace miyagun ƙwayoyi iri daban-daban.

    An kuma kama mutane uku ɗauke da wiwi da wasu magungunan da ke da illa ga kwakwalwa, musamman pregabalin, Exol da tramadol.

  13. Najeriya ta yi Alla-wadai da sabbin hare-haren Houthi a Saudiyya

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta yi Alla-wadai da sabbin hare-haren da mayaƙan Houthi a Yemen suka kai wa Saudiyya ranar Litinin 7 ga Satumba 2026, waɗanda suka jikkata fararen hula da dama tare da lalata wasu muhimman gine-ginen farar hula.

    A wata sanarwa da kakakin ma'aikatar Oluwafemi Adeniyi ya fita, Najeriya ta ce tana kallon sabbin hare-haren a matsayin babbar barazana ga tsaro da ikon Saudiyya, da kuma zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.

    Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa, kuma su yi taka-tsantsan tare da kauce wa duk wani mataki da ka iya ƙara ruruta rikicin.

    Ta ce ƙara dagulewar lamarin na iya jefa rayukan fararen hula cikin haɗari, barazana ga tsaron yankin da kuma ƙara kawo cikas ga samar da makamashin da ake buƙata a duniya.

    "Najeriya na goyon bayan gwamnati da al’ummar Saudiyya a wannan lokaci mai wahala, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa," in ji sanarwar.

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da goyon bayan matakan samar da zaman lafiya da sasanta rikice-rikice da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.

  14. Amurka ta ƙara faɗaɗa takunkuman kasuwanci kan kayayyakin Kanada

    Amurka da Kanada

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta faɗaɗa takunkuman kasuwanci kan kayayyakin Kanada, inda ta haramta shigar da wasu kayayyaki gaba ɗaya, yayin da saɓanin tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara kamari.

    Sabbin matakan sun haɗa da hana shigar da barasa, kayayyakin madara da babura daga Kanada zuwa Amurka.

    Shugaba Donald Trump ya zargi Kanada da nuna wariya ga Amurka, bayan da gwamnatin Kanada ta fara aiwatar da harajin ramuwar gayya na kashi 50 cikin 100, daidai da matakan da Washington ta ɗauka kan kayayyakin Kanada.

    Ana sa ran sabbin takunkuman na Amurka, waɗanda suka haɗa da ƙara yawan kayayyakin Kanada da za a ƙaƙaba wa haraji, za su fara aiki a ƙarshen wannan watan.

    Firaministan Kanada, Mark Carney, ya gargaɗi ƴan ƙasar cewa rage dogaro da makwabciyarsu Amurka ba zai rasa tasiri ga tattalin arzikin Kanada ba.

    Sai dai ya ce, hakan shi ne mafi alheri fiye da ci gaba da sayen kayayyakin Amurka.

  15. Ƴan jarida 5 sun yi ɓatan dabo a kan hanyarsu ta zuwa ɗauko rahoto

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ƴan jarida biyar na Indonesia sun ɓace bayan da suka yi tafiya da jirgin ruwa domin ɗauko rahoto kan fashewar wani dutse mai aman wuta na Mount Anak Krakatau.

    Jami’an agaji na ci gaba da neman ƴan jaridar tare da wasu mutum uku da ke cikin jirgin a lokacin da suka ɓace.

    Fashewar dutsen mai aman wutar, wadda ta fara a daren Juma’a, ta janyo dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tare da rufe sararin samaniya da toka mai kauri a birane da dama, ciki har da babban birnin ƙasar, Jakarta.

    Ana ci gaba da aikin bincike da ceto, sai dai igiyar ruwa mai ƙarfi da rashin kyakkyawar hango nesa na haifar da jinkiri wajen aikin ceton.

    Hatsarin teku ya kasance ruwan dare a wannan yanki, sakamakon rashin tsauraran matakan kiyaye lafiya a harkar sufuri ta ruwa da kuma matsanancin yanayi da ake fuskanta a lokuta daban-daban.

  16. Farashin ɗanyen man Brent ya kai dala 100

    Brent

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyen man Brent ya haura dala 100 kan kowace ganga a kasuwar duniya a yau.

    Wannan ne karon farko tun watan Yuli da farashin mai ya haura dala 100, yayin da ake ci ga gaba da zaman ɗar-ɗar a Gabas ta Tsakiya.

    Farashin man ya ci gaba da hauhawa a hankali a cikin ƴan makonnin nan, har ya haura wannan dala 100.

    Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa harin da ƴan Houthi na Yemen suka kai kan cibiyoyin mai na Saudiyya a wannan makon ya haddasa gobara a cibiyar.

    Rahoton ya ce lamarin na iya yin barazana ga jigilar ɗanyen mai ta Tekun Maliya, wadda ke zama wata hanya ta daban bayan mashigar Hormuz.

  17. Kotu ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM

    Robert Orya

    Asalin hoton, @officialEFCC/X

    Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 490 a gidan yari da aka yanke wa tsohon shugaban bankin shige da fitar da kayayyaki a Najeriya na NEXIM, Robert Orya.

    Kotun ta ce ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume 49, inda aka yanke masa hukuncin shekaru 10 a kan kowanne tuhuma, wanda ya kai jimillar shekaru 490, kuma hukuncin zai gudana ne a lokaci guda.

    Robert Orya ya rike muƙamin Manajan Daraktan bankin NEXIM tsakanin shekarar 2009 da 2016 a zamanin mulkin marigayi Shugaba Umaru Yar’Adua, sannan tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya sake naɗa shi a 2014.

    Bayan ya bar muƙaminsa, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2021 kan tuhume-tuhume 49 da suka haɗa da karɓar kuɗi ta hanyar yaudara da zamba da suka kai naira biliyan 2.4.

    A ranar 5 ga Fabrairu 2026, wata Babbar Kotun Babban Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 490 a gidan yari, wanda za a yi a lokaci guda.

    A hukuncin da kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara suka yanke, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Muhammed Danjuma, kotun ta ce alkalin kotun farko, Mai Shari’a Messiri, ya yi daidai wajen yanke hukuncin.

    Mai Shari’a Danjuma, tare da sauran alkalan biyu, Ntong Ntong da Ele Enenche, sun ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa Orya ba tare da wata tantama ba.

  18. Iran ta ce ta kai harin makamai masu linzami kan tankokin yaƙin Amurka

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar Kare Juyin Juya Halin Iran, IRGC, ta ce ta kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka guda biyu da makamai masu linzami.

    A cikin wata sabuwar sanarwa da rundunar ta fitar a safiyar Laraba, ta ce ta kai harin ne kan jiragen ruwan yaƙin Amurka DDG-119 da DDG-53, waɗanda ke ɗauke da makamai masu linzami na cruise da na Aegis.

    Rundunar ta yi iƙirarin cewa harin ya lalata jiragen.

    Hakan na zuwa ne sa'a guda bayan da Rundunar Tsakiyar Sojin Amurka, CENTCOM, ta ce ta kai hari tare da lalata tankokin ɗaukar ɗanyen man Iran guda biyar, a matsayin martani ga yunƙurin Iran na kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka.

  19. Batun addini ne ke taka rawa a shari'ar El-Rufai - NSCIA

    El-Rufai

    Asalin hoton, El-Rufai/X

    Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta nuna damuwa kan abin da ta kira alamun nuna wariyar addini a shari'ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

    A wata sanarwa da Sakataren Janar na majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya fitar, NSCIA ta ce ta daɗe tana ƙoƙarin ganin ta kaurace wa yin tsokaci kan shari'ar, saboda tun farko ta ɗauke ta a matsayin shari'a ta yau da kullum, tare da tunanin cewa kotuna za su iya tabbatar da adalci.

    Sai dai majalisar ta ce wasu abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, sun sa ta fara ganin akwai alamun wariyar addini ce ke taka rawa a shari'ar.

    Wannan ya biyo bayan kalaman Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, wanda ya zargi El-Rufai da shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamna.

    NSCIA ta ce waɗannan kalamai sun sa ta sauya matsayinta na ƙin tsoma baki a batun, tana mai cewa akwai abubuwan da ke nuna yiwuwar wani "son zuciya na wariyar addini" a kan tsohon gwamnan.

    Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma ɓangaren shari'a da su tabbatar da cewa ba a yi amfani da hukumomin gwamnati ko tsarin shari'a wajen aiwatar da wata manufa ta bangaranci a kan El-Rufai ba.

    Ta kuma yi kira ga jama'a da su guji kalaman tunzura jama'a da ka iya yin tasiri kan shari'ar El-Rufai ko kuma ƙara dagula yanayin tsaro a Najeriya.

  20. Amurka ta mayar da martani kan iƙirarin Iran na kama jirgin ruwanta

    Jirgin ruwan Amurka da Iran ta ƙwace

    Asalin hoton, Getty Images

    Hedikwatar Rundunar Sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta mayar wa BBC martani kan ikirarin da Iran ta yi na cewa ta kama wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku maras matuƙi na Amurka a mashigin Hormuz.

    A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun CENTCOM, Laftanar Kyaftin Tim Hawkins, ya ce jirgin ruwan ƙarƙashin tekun ya lalace ne fiye da kwana ɗaya da ya gabata.

    Ya ce jirgin yana sintiri ne a ruwan yankin domin tallafa wa ayyukan da sojojin Amurka ke ci gaba da gudanarwa.

    Hawkins ya ƙara da cewa, "jirgin tsohon samfuri wanda ba ya tattara muhimman bayanan sirri, kuma ba ya ɗauke da na'urorin radar ko na'urorin gano bayanai masu sirri."

    Ya kuma ce ayyukan sojojin Amurka a ruwan yankin na ci gaba kamar yadda aka saba.

    A sa'o'in da suka gabata ne kamfanin dillancin labarai na Fars, mai alaƙa da rundunar juyin juya halin Iran, ya ba da rahoton cewa Iran ta "kama" wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku mai fasahar zamani na Amurka.

    A cewar Fars, jirgin na daga cikin sababbin jiragen ruwa marasa matuƙi masu zamani da sojojin Amurka ke amfani da su.

    Kamfanin ya kuma ce an kama jirgin ne a bakin shiga mashigar Hormuz.