Hanyoyi 10 na nuna hamayya a tsarin dimokraɗiyya

- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Tsarin dimokraɗiyya ya bai wa jama'a damar bayyana ra'ayoyinsu da kuma sukar ayyukan gwamnati cikin lumana.
Hamayya na daga cikin muhimman ginshiƙan tsarin dimokraɗiyya, domin tana taimakawa wajen tabbatar da cewa masu mulki suna aiki cikin gaskiya da riƙon amana.
Sai dai masana harkokin siyasa na cewa bayyana hamayya na buƙatar bin doka da ƙa'idojin dimokraɗiyya, tare da kauce wa kalaman tunzura jama'a ko matakan da za su iya haddasa rikici.
A ƙasashe da dama, jam'iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula na taka muhimmiyar rawa wajen bayyana matsalolin gwamnati da gabatar da wasu hanyoyin magance su.
Hakan na taimakawa wajen ƙarfafa tattaunawa da kuma inganta tsarin shugabanci.
Ta yaya ya kamata a bayyana hamayya ta yadda za ta amfani al'umma da tsarin dimokraɗiyya ba tare da haifar da rashin zaman lafiya ba?
Masana na cewa amsar wannan tambaya na cikin bin dokokin ƙasa, mutunta ra'ayin juna, da kuma amfani da hujjoji maimakon kausasan kalamai wajen bayyana bambancin siyasa.
A wannan muƙala, za mu yi nazari kan hanyoyin da masana da masu ruwa da tsaki ke ganin ya kamata a bi wajen bayyana hamayya a tsarin dimokraɗiyya.
Kafa ko shiga jam'iyyun adawa
Jam'iyyun adawa na taka muhimmiyar rawa wajen sa ido kan ayyukan gwamnati da kuma gabatar da wasu sababbin manufofi.
Ta hanyar shiga jam'iyyar adawa, ƴan ƙasa na da damar yin tasiri a harkokin siyasa.
Haka kuma jam'iyyun adawa na taimakawa wajen tabbatar da cewa gwamnati ba ta yi mulkin kama-karya ba.
Wannan wata hanya ce ta halal da kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince da ita, kamar yadda Dr Ja'e ya bayyana wa BBC.
Faɗin albarkacin baki
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ƴan ƙasa damar bayyana ra'ayoyinsu a fili.
Barista Nuhu Hamza Dantani, lauya mai zaman kansa, kuma masanin dokokin Najeriya ya ce dokokin Najeriya sun bai wa ƴanƙasar damar faɗin albarkacin bakinsu, ''matuƙar bai saɓa wa doka ba''.
Dr Yakubu Haruna Ja'e shugaban sashen kimiyyar siyasa da alaƙar ƙaashe da diplomasiyya na Jami'ar jihar Kaduna ya ce ana iya yin hakan ta hanyar hira da kafafen yaɗa labarai da rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta ko jaridu da tarurruka ko jawabai.
''Wannan na bai wa jama'a damar sukar manufofin gwamnati ko na jam'iyyun hamayya tare da nuna rashin amincewa da wasu matakan da ɓangarorin ke ɗauka'', in ji shi.
Sai dai malamin jami'ar ya ce dole ne a guji kalaman da za su iya haddasa tashin hankali ko ƙeta haƙƙin wasu.
Zanga-zangar lumana
Zanga-zangar lumana wata hanya ce ta nuna rashin amincewa da wani mataki ko manufa.
Masu zanga-zanga kan fito fili su isar da saƙonsu ba tare da amfani da tashin hankali ba.
A dimokraɗiyya, zanga-zanga na taimakawa wajen jawo hankalin gwamnati ga wata matsala.
Amma wajibi ne a gudanar da ita cikin lumana tare da bin tanade-tanaden doka.
Dr Ja'e ya ce tsarin dimokraɗiyya ya hana mummunan zanga-zanga.
''Ba ana fitowa ba ne a yi faɗa ko yaƙi ko a dinga zamba da cin mutuncin juna'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa ko yaƙin neman zaɓe ake yi ba a so jam'iyyu biyu su yi yaƙin neman zaɓe a wuri ɗaya.
Shiga zaɓe da yaƙin neman zaɓe
Mafi girman hanyar bayyana hamayya ita ce shiga zaɓe domin neman canji ta akwatin jefa ƙuri'a.
Ƴan takara da jam'iyyu na gabatar da manufofinsu ga jama'a domin neman goyon baya.
Idan jama'a sun gamsu, suna iya zaɓar wata jam'iyya ko ɗan takara daban.
Wannan shi ne ginshiƙin dimokraɗiyya, kamar yadda masana suka yi ƙarin haske.
Fito da gazawar juna
Dr Yakubu Ja'e ya ce ɗaya daga cikin hanyoyin bayyana hamayya a tsarin dimokraɗiyya shi ne fito da gazawar juna tsakanin jam'iyyu da ƴantakara ba tare da cin zarafi ko muzantawa ba.
''Ita hamayya a siyasance ana so ne a yi a ilimance kuma a faɗi ra'ayi domin mutane su fahimci manufar kowane ɓangare ta hanyar fito da gazawar juna'', in ji shi.
Shi ma Barista Nuhu Dantani ya ce jam'iyyun adawa za su iya fito da gazawar gamnati ta ahnyar nuni da wasu manufofinta da ba su yi wa talakawa daɗi ba.
''Ha ita ma gwamnati za ta iya fito da gazawar ɗantakarar adawa ko jam'iyyar adawa ta hanyar wasu manufofinsu da take gani ba za su taimaki talaka ba'', in ji shi.
Tattaunawa da muhawara
Muhawara da tattaunawa suna ba mutane damar bayyana ra'ayoyi mabambanta cikin mutunci.
A cewar Dr Yakubu Ja'e ana yin irin waɗannan muhawarori a kafafen yaɗa labarai da makarantu da tarukan jama'a.
''Akan shirya su ne domin gabatar da manufofin kowace jam'iyya ko ɗantakara ga jama'a domin su fahimci manufar kowa don yanke shawara kan wanda za su zaɓa'', in ji shi.
Hakan na taimakawa wajen ilimantar da al'umma kan muhimman batutuwa.
Dr Ja'e ya ƙara da cewa akan tsayar da duka ƴantakara su yi wa jama'a bayanai, talakawa su yi musu tambayoyi.
Amfani da dokar 'ƴancin samun bayanai (FOI)
Dokar Freedom of Information ta bai wa jama'a damar neman bayanai daga hukumomin gwamnati.
Wannan na taimakawa ƴan jarida da masu fafutika da sauran jama'a su binciki yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati.
Idan an gano kura-kurai, za a iya bayyana su ga jama'a domin neman gyara.
A cewar masana wannan hanya na ƙarfafa gaskiya da riƙon amana a mulki.
Amfani da kafafen sada zumunta
Kafafen sada zumunta sun zama wata muhimmiyar hanya ta bayyana ra'ayi a wannan zamani.
Jama'a na iya amfani da su wajen sukar manufofin gwamnati ko jam'iyyun hamayya ta hanyar bayyana matsaloli da gazawar juna.
Hakan kan taimaka wajen yaɗa bayanai cikin sauri da kuma tattara ra'ayin jama'a.
''Amma yana da muhimmanci a guji yaɗa ƙarya, zagi ko kalaman ƙiyayya ko na cin zarafi'', a cewar Dr Yakubu Ja'e.
Amfani da majalisun dokoki
Ƴan majalisa na iya bayyana hamayya ta hanyar muhawara da gabatar da ƙuduri ko yin bincike kan ayyukan gwamnati.
Majalisun dokoki na da alhakin sanya ido kan ɓangaren zartarwa.
Ta wannan hanya, ana iya gano kura-kurai da neman gyara, kamar yadda masana harkokin siyasa ke cewa.
Hakan yana taimakawa wajen ƙarfafa gaskiya da riƙon amana a shugabanci.
Barista Nuhu Hamza Dantani ya ce adawa a siyasa ba laifi ba ne, hasalima yana daga cikin gishirin dimokraɗiyya.
Ayyukan ƙungiyoyin farar hula
Ƙungiyoyin farar hula kan yi nazari da sanya ido kan ayyukan gwamnati tare da kare muradun jama'a.
Sukan shirya gangamin wayar da kai da bincike da kuma kamfen domin neman sauyi.
Sai dai Barista Nuha Dantani ya ce shiga ƙungiyoyin farar hula bai ba wa mutum damar faɗar duk abin da ya ga damar faɗi ba.
''Dokar da ta bai wa ɗan Najeriya bayyana ra'ayinsa ba ta ba shi damar cin mutunci ko zagi ko aibata wani mutum da yake hamammay da shi ba'', in ji lauyan.
Sau da yawa suna zama muryar waɗanda ba su da damar isa ga masu mulki.
Gudummawarsu na taimakawa wajen ƙarfafa dimokraɗiyya da shugabanci nagari.











