Ina Iran ta ɓoye sinadarin Uranium ɗinta na haɗa nukilya?

- Marubuci, Journalist
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, R eza Sabet
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Daga cikin muhimman abubuwan da suke jan hankali game da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran akwai batun Uranium din Tehran.
Sai dai har yanzu fahimtar asalin inda sinadarin wanda aka inganta domin samar da makamin nukiliya yake ya zama tamkar sirrin boye.
Ana kai-komo ne kan makomar daruruwan kilogram na sinadarin Uranium da Iran ta inganta zuwa kashi 60, wato matakin zama makami, wanda kuma saura kiris ya kai matakin kashi 90 da yake zama makamin kare dangi na nukiliya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dole a lalata sinadarin ko dai a cikin Iran ko a wani wajen daban, amma Iran na cigaba da nanata rashin anincewarta.
Kusan shekara daya ke nan bayan Amurka da Isra'ila sun kai hare-hare a cibiyoyin nukiliyar Iran na Fordow da Natanza da Isfahan a lokacin da aka yi yakin kwana 12.
Sai dai har yanzu babu wata hukuma da ta tabbatar da irin barnar da aka yi wa cibiyoyin.
Haka kuma ba a iya kayyade ragowar sinadarin na Uranium, sannan a ina Iran ta adana su.
Wasu masu bincike sun ce suna ganin an kwashe sinadarin da aka inganta kafin hare-haren, wasu kuma suna ganin har yanzu akwai saura a karkashin baragunan ginin da ya rushe.
Shin me ya sa Iran take adana sinadarin, kuma ina makomar sinadarin?
Me ya sa Iran ke da sinadarin Uranium da aka inganta zuwa kashi 60?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A yarjejeniyar nukiliya da aka shiga a shekarar 2025 da aka fi sani da JCPOA, Iran ta amince ta inganta sinadarin Uranium dinta ne zuwa kashi 3.67 kawai.
Za a iya amfani da shi a wannan matakin ne kawai domin samar da makamashi. Bayan Amurka ta fice daga yarjejeniyar a zamanin mulki Trump na farko a shekarar 2018, sai Iran ta kara sana'anta sinadarin zuwa kashi 4.5, sannan ta kara zuwa kashi 20 har ta nausa zuwa kashi 60 daga baya.
Daga bisani ne aka yi yunkurin sake shiga yarjejeniyar ta JCPOA, amma aka samu tsaiko.
Lamarin ne ya kara haifar da takun-saka tsakanin Iran da kasashen yamma.
Hukumar kula da nukiliya ta duniya ta ce bayan Iran ta kara inganta sinadarin, ta kuma rage yawan lokacin da ake bukata domin inganta sinadarin, inda take iya gyara sinadarin mai mai yawan gaske a cikin kankanin lokacin.
Kafin yakin kwana 12 na bara, matakin sinadarin Uranium na Iran ya riga ya kai kashi 60, sannan ta riga ta inganta kusan kilogram 440 na sinadarin kamar yadda hukumar kula da nukiliya ta bayyana.
Sai dai ita ma hukumar ta nanata cewa ba ta da cikakkiyar masaniya kan makomar sinadarin da inda yake a yanzu.
Ana adana sinadarin ne a yanayi na iskar gas ta uranium hexaflouride wato UF6 da ake ajiyewa a cikin tukunyar gas ta musamman.
Me ya sa aka mayar da hankali kan cibiyoyin karkashin kasa?
An fara ganin alama ne daga hukumar kula da makamashin nukiliya da kanta bayan ta ce ta dasa na'urorin adana nukiliya a cibiyar Isfahan bayan ta Fordow tun a shekarar 2024.
Don haka kun kafin hare-haren na Yunin 2025, duniya ta riga ta fara sa ido kan cibiyoyin na karkashin kasa.
An kara samun haske ne kimanin wata bakwai bayan yakin kwana 12, inda rahoton hukumar ya nuna cewa ta lura da karuwar zirga-zirgar motoci a kusa da cibiyoyin.
Hukumar ta kara da cewa a cibiyoyin ne aka adana uranium samfurin hexafluoride da aka inganta zuwa kashi 20 da wadanda aka inganta zuwa matakin kashi 60.
Sai dai kasancewar jami'an hukumar ba su samu damar zuwa ziyara cibiyoyin domin barnar da hare-haren suka yi ba, yanzu ba ta da tabbacin ko dai akwai sauran sinadarin a cibiyar Isfahan ko babu.
Zirga-zirgar motoci da tankokin ruwa kafin hare-hare
An samu haske kan yanayin cibiyar ne kwanaki kadan kafin harin na Yunin 2025. Jaridar Le Monde ta Faransa ta nuna wani hoto a ranar 28 ga watan Maris na 2026 da ke nuna alamun akwai wani abu a cibiyar.
Hoto ya nuna manyan motoci a kusa da kofar cibiyar Isfahan makare da manyan tukunyoyin gas.
Wasu na ganin an shigar da sinadarin uranium hexafluoride ne a cikin tukunyar.
Sai dai masana sun ce hotunan kadai ba za su tabbatar da asalin batun ba, sannan hukumar nukiliya ba ta tabbatar da abin da ke cikin motocin ba.
Wuraren sirri
Bayan kammala yakin kwana 12, jaridar New York Times ta ruwaito bayanan sirri daga hukumar leken asirin Amurka cewa an kwashe wani bangaren na sinadarin Uranium din Iran kafin a kaddamar da hare-hare a cibiyoyin.
Sannan rahoton ya nuna cewa akwai yiwuwar Iran ta boye sauran sinadarin ne a wasu wuraren sirri da ba a sani ba.
Jaridar ta kuma ruwaito wata majiya daga Isra'ila da ke nuna cewa Iran na da wata cibiyar a boye ''da ta tanada domin ta cigaba da aikin sana'anta sinadarin na Uranium a cikin sirri."
Wata alama da aka samu kuma, duk da ba a tabbatar ba ita ce sanarwar da hukumomin Iran suka fitar.
A wata wasika da kasar ta aika wa hukumar kula da nukiliya a watan Yunin 2025, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce kasarsa za ta dauki matakai da suka dace "wajen kare sinadaran hada nukiliya da kayan aiki."
Amma ya bayyana wa jaridar New York Times daga bisani cewa "ba shi da cikakkiyar masani kan" inda aka boye sinadaran na Uranium na kasar bayan hare-hare.
Daga baya kuma hukumomin kasar, musamman Mr Araghchi sun bayyana cewa sinadaran na karkashin baraguzan kasa.
Sannan a watan Maris na 2026 ya shaida wa CBS cewa Iran ba ta shirya hako su ba.
Sai dai Iran ba ta boye rashin amincewarta da yunkurin kwashe sinadaran a tafi da su wani waje na daban ba.
A Afrilun 2026, mai magana da yawun ma'aikatar wajen Iran Esmail Baghaei ya ce, "Iran ba za ta aminta a kwashe sinadaran Uranium da ta inganta ba a kai su wani wajen daban."
Sannan kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wasu mutum biyu daga cikin gwamnatin Iran na cewa jagoran addin kasar ya bayar da umarnin kada a bari a fitar da Uranium din da kasar ta gyara.
A bangaren Amurka kuwa, hukumomi a kasar sun bayar da jawabai mabambanta ne game da makomar sinadarin Uranium din.
Jin kadan bayan yakin kwana 12, Amurka ta ayyana "tarwatsa cibiyoyin nukiliyar Iran baki daya."
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce akwai yiwuwar an boye kayan makamin nukiliya ne a cikin duwatsu da kankare, sannan sakataren tsaron Amurka na wancan lokacin, Pete Hegsett ya ce babu alamar da ke nuna an kwashe sinadaran da kayan aikin kafin Amurka ta kaddamar da hare-hare.
Yanzu dai babu cikakken bayani kan inda aka boye ko aka adana sinadarin na Uranium.
"Tsaunuka"
Bayan jawaban ɓangarorin biyu, wani bayanin na uku da ya samu karbuwa sosai shi ne wai an mayar da kayan aiki da sinadaran zuwa wani sabon wajen a karkashin kasa, kamar yadda hukumomin Isra'ila suka bayyana wa New York Times.
Wajen da aka fi kira shi ne "Tsaunin Pickaxe" wanda wata cibiya ce da ke kusa da Natanz, kamar yadda jaridar Washington Post ta bayyana.
Kafar ta ruwaito cewa an fara aikin gina cibiyar ne a shekarar 2020, sannan an kara karfafa aikin wajen tun bayan yakin kwana 12.
Rahoton ya kara da cewa bisa la'akari da hotunan tauraron dan Adam da aka dauka, akwai hanyoyin karkashin kasa da aka gina a cibiyar da kuma samar da ababen tsaro.
PBS ta ruwaito a watan Disamban 2025 cewa cibiyar "Koh Kalang " da ke kusa da Natanz na cikin ayyukan karkashin kasa ba san su ba.
Rahoton ya kara da cewa jami'an hukumar kula da makashin nukiliya ba su taba zuwa duba wajen ba, sannan Iran ba ta bayar da damar zuwa wasu cibiyoyin a gani ba tun fara yaki.
PBS ta kara da cewa hukumomin Iran sun bayyana cewa makasudin gina wajen shi ne adana wasu na'urori ba adana sinadarin Uranium da aka sana'anta ba.
Cibiyar Center for Strategic and International Studies ita kuma ta ruwaito cewa za a iya amfani da cibiyar a nan gaba wajen adana sinadarai da kayan aiki saboda zurfin ramin da ingancin kofofin da sauran su.
Sai dai duk ana amfani ne da hotunan tauraron dan Adam wajen nazari da hasashen yanayin wurin, sai kuma bayanan sirri da sharhin masana da kuma bayanan hukumar kula da nukiliya.
Me Iran ta ce kan ma'adanar?
A ranar 13 ga Yunin 2025, Abbas Araghchi ya sanar da hukumar nukiliyar cewa Iran "za ta dauki duk matakan da suka dace wajen adana sinadarai da kayan aikin nukiliyarta."
Sai kuma darakta janar na hukumar ya yi martani cewa dole a sanar da hukumar a duk lokacin da za a sauya wa sinadarin waje.
A ranar 2 ga Agustan 2025, Abbas Araghchi ya bayar da amsa a tattaunawarsa da jaridar Financial Times cewa, "ban sani ba," a lokacin da aka tambaye shi ko aikin da suka yi na inganta Uranium ya kai kashi 60.
Sai dai ga kara da cewa, "maganar gaskiya ba ni da masaniya saboda suna wurare ne da aka jefa wa bama-bamai.
Ya nanata cewa a iya sanin shi, abin da ake tambaya a kai suna cibiyoyin da aka kai wa hari ne, kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ce za ta iya tantance komai.
A ranar 11 ga Satumban 2025, Abbas Araghchi ya bayyana a tashar talabijin cewa, "Uranium dinmu na karkashin baraguzan cibiyoyin nukiliya da aka ruguza da bama-bamai," in ji shi, sannan ya kara da cewa hukumomi ne za su tantance yadda wurin yake.










